Majalisar Dattawa za ta tantance Amupitan a ranar Alhamis
Published: 15th, October 2025 GMT
Majalisar Dattawa za ta tantance Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN) a ranar Alhamis, a matsayin sabon shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).
Daraktan Yaɗa Labarai na Majalisar Tarayya, Bullah Audu Bi-Allah ne, ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.
Ba za mu yi sulhu da ’yan bindiga ba sai sun yi tuba na gaskiya — Radda Gwamna Buni ya ware N5.8bn don biyan haƙƙin tsoffin ma’aikata a Yobe
A makon da ya gabata ne, Shugaba Tinubu, ya aike wa Majalisar Dattawa sunan Amupitam, domin ta tabbatar da naɗinsa.
An karanta wasiƙar Tinubu yayin zaman majalisar, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio.
A cikin wasiƙar da ya aike, Tinubu, ya ce: “Dangane da sashe na 154 (1) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 (da aka yi wa kwaskwarima), ina farin cikin gabatar da Farfesa Joash Amupitan (SAN), domin a tabbatar da shi a matsayin shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).
“Na haɗa da taƙaitaccen tarihin aikinsa, kuma ina fatan Majalisar Dattawa za ta duba kuma ta tabbatar da naɗinsa cikin gaggawa.”
Sanarwar da Ofishin Yaɗa Labarai na Majalisar, ya fitar ta kuma bayyana cewa za a tantance shi a a ranar Alhamis, 16 ga watan Oktoba, 2025.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Majalisar Dattawa Naɗi Tantancewa Majalisar Dattawa a tabbatar da
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan Majalisar Tarayyar Kaduna 3 sun sauya sheka zuwa APC
’Yan Majalisar Tarayya uku daga Jihar Kaduna sun sauya sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APC.
Shugaban Majalisar Wakilai Abbas Tajuddeen ya sanar a ranar Talata cewa masu sauya shekar sun hada da Honorabul Abdulkarim Hussain Mohammed, Aliyu Mustapha Abdullahi da kuma Sadiq Ango Abdullahi.
Tajuddeen, wanda shi ma dan asalin Jihar Kaduna ne, ya sanar da cewa, Gwamnan jihar, Uba Sani ya halarci zaman majalisar domin shaida dawowar ’yan majalisar zuwa APC daga PDP.
Masu sauya shekar sun bayyana cewa rikin cikin gida da rabuwar kai da suka dabaibaye tsohuwar jam’iyyarsu ta PDP ce ta sa suka yanke shawarar sauya sheka.
Shugaban Hukumar Zaɓen Yobe Jihar Yobe ya rasu Faɗa ya ɓarke tsakanin Palasɗinawa da Hamas bayan sulhu da Isra’ilaJim kadan bayan sanar da sauya shekar tasu ce Gwamna Uba Sani ya jagorance su zuwa ga shugaban majalisar inda suka dauki hoto kafin shi da tawagarsa su wuce.
Tuni dai Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Wakilai, Kingsley Chinda, ya kalubalanci sauya shekar, yana mai kira ga shugaban majalisar da ya kwace kujerunsu, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.