Larijani: Iran Tana Adawa Da Juya Akalar Siyasar Yankin Daga Wasu Masu Son Baba-Kere
Published: 30th, August 2025 GMT
Babban sakataren Majalisar kolin tsaron kasar Iran ya jaddada cewa: Iran na adawa da duk wani sauyi na siyasa a yankin
Babban Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya bayyana cewa: Iran na adawa da duk wani sauyi na siyasa a yankin da kuma cutar da alaka tsakanin Iran da Armeniya.
Ali Larijani, babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran, ya gana tare da tattaunawa da Armen Grigoryan, sakataren kwamitin koli na tsaron kasar Armeniya a safiyar yau.
A cikin wannan taro, babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya bayyana gamsuwar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take da shi kan matakin tattalin arziki, siyasa, tsaro da kasar Armeniya, tare da jaddada hadin gwiwa da makwabciyarta ta arewa wajen kammala aikin layin dogo na arewa da kudu da kuma alakanta tekun Farisa da tekun Black Sea.
Ali Larijani ya bayyana goyon bayan Iran ga shawarwarin zaman lafiya tsakanin Armeniya da Azabaijan, inda ya tattauna kan manufar Iran na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, yana mai cewa: Iran a ko da yaushe tana goyon bayan ‘yancin kai da karfin kasashen yankin don kiyaye tsaronsu.
Mr. Grigoryan, sakataren kwamitin koli na tsaron kasar Armeniya, ya bayyana dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu a matsayin wacce ba a taba irinta ba a yayin wannan ganawar, ya kuma bayyana cewa, burinsa na wannan ziyara shi ne fadada huldar dake tsakanin kasashen biyu a dukkan fannoni, ya kara da cewa, “Armeniya a shirye take ta rattaba hannu kan wani cikakken daftari kan huldar abokantaka da Iran nan gaba kadan.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kungiyar Hamas Ta Yi Maraba Da Matakin Wasu Kasashen Turai Na Nuna Kyamarta Zaluncin Isra’ila August 30, 2025 Kasar Denmark Tana Goyon Bayan Dakatar Da Yarjejeniyar Kasuwacin Da Isra’ila August 30, 2025 Moroko: Zanga-Zangar Rashin Amincewa Da Kisan Kiyashi Da Kakaba Yunwa A Gaza August 30, 2025 Guinea: An Fara Tattaunawa Kan Zaben Raba Gardama Na Sabon Kundin Tsarin Mulki August 30, 2025 Turkiyya Ta Bukaci A Dakatar Da Isra’ila (HKI) Daga Majalisar dinklin duniya August 30, 2025 Iran: IRGC Sun Kama Ma’aikatan Mosad A Arewa Maso Gabacin Kasar August 30, 2025 Iran Ta Yi Watsi Da Shirin ‘SnapBack’ Na Kasashen Turai August 30, 2025 E3 sun gindaya sharudda 3 kan dakatar da dawo da takunkuman MDD a kan Iran August 30, 2025 Amurka ta hana izinin shiga kasarta ga shugaban Falastinawa don halartar taron MDD August 30, 2025 Rwanda ta dauki bakin haure kashi na farko da aka kora daga Amurka August 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: tsaron kasar Iran
এছাড়াও পড়ুন:
Kwamitin Kolin Tsron Kasar Iran Ya Amince Da Yarjejeniyar Da Aka Cimma Da Hukumar IAEA
Kwamitin koli na tsaron kasa ya amince da yarjejeniyar da hukumar makamashin nukiliya ta duniya IAEA
Kwamitin koli na tsaron kasar Iran ya yi gargadin cewa, idan aka dauki wani mataki na nuna adawa ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran da cibiyoyinta na makamashin nukiliya, ciki har da sake farfado da kudurorin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da suka kare, za a dakatar da aiwatar da tsare-tsare da yarjejeniyoyin da aka kulla da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA.
Sakatariyar kwamitin tsaron kasar Iran ta fitar da wata sanarwa a jiya Lahadi, bayan yarjejeniyar da aka rattabawa hannu tsakanin Seyyed Abbas Araqchi da Rafael Grossi. An yi wannan bayani ne dangane da tsare-tsare da ministan harkokin wajen kasar da babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA suka rattabawa hannu dangane da tsarin mu’amala tsakanin Iran da IAEA bisa la’akari da sabbin yanayi da ake ciki bayan hare-haren soji da gwamnatin yahudawan sahayoniyya da Amurka suka kaddamar kan cibiyoyin makamashin nukiliya na kasar Iran bisa tsarin kariya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Jami’in Kasar Yemen Ya Aike Da Sako Ga Mahalarta Taron Birnin Doha Na Kasar Qatar September 15, 2025 Yawan Mutanen Da Suka Yi Shahada Sakamakon Kisan Kiyashin ‘Yan Sahayoniyya A Gaza Ya Kusaci 65,000 September 15, 2025 Gwamnatin Sudan Ta Ce: Babu Sulhu Da ‘Yan Tawayen Kasar Na Kungiyar Rapid Support Forces September 15, 2025 Kasashen Larabawa da na Musulmi na taron gaggawa kan harin Isra’ila a Qatar September 15, 2025 Hamas ta bukaci kasashen musulmi da na Larabawa su dauki mataki mai tsari kan Isra’ila September 15, 2025 Rabin Sojojin Isra’ila da suka ji rauni a yakin Gaza na fama da ciwon damuwa September 15, 2025 Sudan ta soki takunkuman da Amurka ta kakaba mata September 15, 2025 Dakarun Sojin Yamen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Saman Ramon Na Isra’ila. September 14, 2025 Isra’ila Za ta Gamu Da Mummunar Martani Idan Tayi Gigin Afkawa Iran September 14, 2025 Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Larabawa Da Na Musulmi Sun Fara Taro A Qatar. September 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci