Gwamnatin Jihar Jigawa za ta kafa ƙananan masana’antu a karamar hukumar Gagarawa.

Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan yayin kaddamar da rabon kayayyakin bunkasa tattalin arziki ga wasu daga cikin al’ummar Gagarawa.

Malam Umar Namadi ya yi bayanin cewar, masana’antun za su hada da na sarrafa shinkafa da sauransu.

Yana mai cewar hakan zai taimaka wajen samar da ayyukan yi ga matasa marasa aikin yi a yankin.

Kazalika, Gwamnan yace gwamnatin jihar za ta ware kudi a kasafin kudin shekarar badi don gina hanyar mota daga Medu zuwa Dandidi zuwa Madaka, domin saukaka sufuri ga al’ummar yankin.

Baya ga kaddamar da tallafin, Malam Umar Namadi, ya bude wasu ayyukan ci gaba ciki har da makarantar Tahfizul Qur’ani ta Hajiya Maryam Namadi da babban dakin taro da kuma gyaran babban masallacin Gagarawa.

A halin yanzu, mutane sama da 2,000 ne aka zakulo domin cin gajiyar kayayyakin tallafin.

Kayayyakin sun hada da tallafin naira miliyan 70 da babura da injinan dinki da na niƙa.

Sai kuma kekuna ga ɗalibai da injinan yin taliya da kuma shigar da makiyaya sama da 1,000 cikin makarantun ‘yayan fulani makiyaya.

Taron ya samu halartar shugaban majalisar dokokin jihar da wasu daga cikin ‘yan majalisar zartarwar jihar, da dai sauransu.

Usman Mohammed Zaria

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Gagarawa Jigawa

এছাড়াও পড়ুন:

CAF ta ƙara yawan ’yan wasan ƙasashe zuwa 28 a gasar nahiyar Afrika

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Afrika (CAF), ta sanar da cewa daga yanzu kowace ƙasa da za ta taka leda a Gasar Cin Kofin Afrika za ta je da ’yan wasa 28, maimakon 23 da ake amfani da su a baya.

CAF, ta ce ta ɗauki wannan matakin ne domin rage matsalar samun raunin da ’yan wasa ke samu a lokacin gasar, tare da bai wa masu horaswa damar samun zaɓin ’yan wasa.

Gwamnatin Kano ta nemi a binciki Ganduje kan zargin kalaman ta da hankali Yadda mutane suka yi cikar ƙwari don halartar jana’izar Sheikh Dahiru Bauchi

Haka kuma, an amincewa kowace ƙasa za ta je gasar da mutum 17 daga cikin masu horaswa da likitoci.

Hukumar ta bayyana cewa zuwa ranar 11 ga watan Disamba, dole a turo mata da cikakken jerin sunayen ’yan wasa, wato kwana 10 kafin a fara gasar.

Gasar za ta gudana daga 21 ga Disamba zuwa 18 ga watan Janairu, wanda ƙasar Maroko za ta kasance mai masaukin baƙi, inda ƙasashe 24 za su fafata a gasar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 165
  • Gwamnatin Kano Ta Kara Jaddada Dokar Haramcin Yin Haya da Babur a Jihar
  • ’Yan bindiga sun sace fasto da matarsa  masu ibada a Kogi 
  • Jihar Jigawa Ta Mayar da Rarar Kudi Sama da Naira Miliyan 50 Ga Maniyyatan Aikin Hajjin 2026
  • Mutum 6 sun jikkata a rikici manoma da makiyaya a Jigawa
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 163
  • Yadda aka horar da mata 100 sana’o’in dogaro da kai a Gombe
  • Barau ya musanta zargin gwamnatin Kano, ya soki gwamna Abba
  • Sarakuna sun goyi bayan Gwamnatin Gombe kan yaƙi da cin zarafin mata
  • CAF ta ƙara yawan ’yan wasan ƙasashe zuwa 28 a gasar nahiyar Afrika