Ƴan Wasan Nijeriya Da Suka Sauya Sheka A Kasuwar Musayar Ƴan Ƙwallo Ta Bana
Published: 7th, September 2025 GMT
Bictor Boniface
Wani dan wasan da ya tafi zaman aro shi ne Bictor Boniface wanda ya bar Bayer Leberkusen ya koma Werder Bremen a matsayin aro na tsawon kaka guda a ranar da za a rufe cinikin yan wasa, dan wasan na Nijeriya ya saka hannu akan kwantiragin da zai sa ya zauna a Werder har zuwa watan Yuni na shekarar 2026, kungiyoyin biyu ne za su biya albashin Boniface.
Tolu Arokodare
Wolbes ta sanar da daukar Arokodare daga kungiyar KRC Genk ta kasar Belgium dake buga gasar Belgian Pro League a ranar karshe ta musayar yan wasa, dan wasan mai shekaru 24 ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru hudu da kungiyar ta Firimiya tare da zabin karin shekara, Arokodare ya koma Wolbes ne bayan ya buga wasa mai ban shaawa a kungiyar Genk a kakar wasan da ta wuce, inda ya kare a matsayin dan wasan da ya fi zura kwallaye a gasar ta Belgium da kwallaye 21.
Wilfred Ndidi
Ndidi ya koma kungiyar Besiktas dake buga gasar Super Lig ta kasar Turkiyya daga Leicester City a farkon kasuwar musayar yan wasa, dan wasan na Nijeriya ya koma kungiyar ta Turkiyya ne kan kwantiragin shekaru uku a watan Agusta, an danganta dan wasan mai shekaru 28 da kungiyoyi da dama a Turai amma ya zabi komawa Besiktas.
Bictor Osimhen
Osimhen ya koma Galatasaray ne kan kwantiragin shekaru hudu daga Napoli a farkon wannan bazarar bayan da zakarun Super Lig na Turkiyya suka yanke shawarar biyan Yuro miliyan 75 domin daukarshi, Osimhen, wanda zai samu albashin Yuro miliyan 15 a duk shekara, tuni ya ci wa Galatasaray kwallaye biyu a kakar wasa ta bana, dan wasan na Nijeriya ya ci wa Galatasaray kwallaye 37 a dukkan wasannin da ya buga a bara.
Chidozie Awaziem
Mai tsaron bayan ya dawo Faransa daga MLS, inda ya bar Colorado Rapids ya koma Nantes kan kwantiragin shekaru uku.
Moses Simon
Simon ya kammala komawa kulob din Faransa dake buga gasar Ligue 1, Paris FC a farkon wannan bazara, dan wasan mai shekaru 29, ya koma Paris FC ne daga Nantes kan kwantiragin shekaru uku, kan kudi Yuro miliyan 7, dan wasan ya ci kwallaye takwas sannan ya taimaka wajen cin 10 a wasanni 32 da ya buga wa Nantes a bara.
Gift Orban
Dan wasan mai shekaru 22 ya bar Lyon zuwa Hoffenheim a kan Yuro miliyan 9 tare da karin kudi na Yuro miliyan 3, tuni dai ya bude asusunsa a kasar Jamus inda ya zura kwallo a raga a wasansa na farko da kungiyar inda aka tashi 2-2.
Dukkan wadannan yan wasa dake buga kwallo a kasashen Turai na daga cikin wadanda kocin tawagar Super Eagles ta Nijeriya Eric Chelle zai iya gayyata domin wakiltar Nijeriya a wasannin neman tikitin buga gasar Kofin Duniya da za a cigaba da bugawa a wannan watan na Satumba da ya kama, Osimhen, Moses Simon da Samuel Chukwuze na daga cikin yan wasan gaba da Nijeriya ke ji dasu a cikin tawagarta, hakazalika a lokuta da dama yan wasan sun sha fitar wa kasar kitse a wuta a wasanni masu muhimmanci.
Yayin da wasannin neman tikitin shiga gasar cin kofin Duniya na FIFA ke gabatowa mako mai zuwa, yana da muhimmanci wadannan yan wasan su kasance cikin natsuwa domin wakiltar Nijeriya a wadannan wasannin, tawagar Super Eagles ta Nijeriya za ta kara da takwarorinta na kasar Rwanda da Afirka ta Kudu a wannan watan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Nijeriya Wasanni kan kwantiragin shekaru dan wasan mai shekaru Yuro miliyan
এছাড়াও পড়ুন:
Trump Ya Umarci Ma’aikatar Yakin Amurka Ta koma gwajin makaman nukiliya
Shugaban Amurka Donald Trump ya umarci Ma’aikatar Yakin da ta ci gaba da gwajin makaman nukiliya nan take, shawara da tauni ta tsorata masu fafutukar yaki da irin wannan manufa.
A cikin wani sako da ya wallafa a dandalinsa na Truth Social yau Alhamis, Trump ya bayyana cewa ya bayar da umarnin “saboda shirye-shiryen tantancewa da wasu kasashe suke yi.” Kuma a cewarsa wannan tsari zai fara nan take,”
Shugaban Amurka ya bayyana Rasha da China a matsayin kasashe na biyu da na uku na duniya masu karfin makamman nukiliya, bi da bi, yana mai tabbatar da cewa idan Washington ba ta ci gaba da gwajin makaman nukiliya ba, wadannan kasashe za su cimma ta nan da ” shekaru biyar.”
Ana sa ran tsarin gwajin zai samar da bayanai kan ayyukan sabbin makaman yaki da kuma amincin tarin makaman da suka tsufa.
Matakin na Trump shi ne wani kira na kai tsaye da Amurka ta yi na ci gaba da gwajin nukiliya tun bayan gwajin da Washington ta yi na karshe a shekarar 1992.
Masu suka sun yi gargadin cewa sake fara gwajin nukiliya na kai tsaye zai iya kawo karshen shekaru da dama na kokarin hana yaduwa da kuma haifar da tarin gwaje-gwajen ramuwar gayya a duk faɗin duniya, wanda hakan zai wargaza Yarjejeniyar Hana Gwajin Makaman nukiliya (CTBT).
A bara, wani rahoto ya nuna cewa Amurka na shirin kashe ɗaruruwan biliyoyin daloli don sabunta makaman nukiliyarta.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Isra’ila ta amince da fadada matsugunai a Yammacin Kogin Jordan October 30, 2025 Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu October 30, 2025 Sudan : Kasashen duniya na tir da cin zarafi a El-Fasher October 30, 2025 Iran Ta Jaddada Bin Hanyar Diflomasiya Ko Da A Lokacin Yaki Ne Amma Ba Zata Amince Da Bin Umarni Ba October 30, 2025 Qalibaf: Amurka Tana Yaudarar Duniya Da Zaman Lafiya, Alhalin Tana Ci Gaba Da Kai Harin Wuce Gona Da Iri October 30, 2025 Ci Gaba Da Killace Gaza Bayan Tsagaita Bude Wuta Ya Janyo Mutuwar Mutane 1000 A Yankin October 30, 2025 Kungiyar Rapid Support Forces Ta Sanar Da Kafa Kwamitin Bincike Kan Cin Zarafin Al’umma A El Fasher October 30, 2025 An Kafa Dokar Ta Baci A Darul-Salam Saboda Tarzoman Zaben Shugaban Kasa A Tanzania October 30, 2025 Rasha Da Amurka Sun Sake Dawo Da Gwaje-gwajen Makaman Nukiliya October 30, 2025 Kasar Czech Ta Hana Wa Wani Sojan HKI Shiga Kasar Bisa Gargadin Faransa October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci