Baki Kusan 50 Daga Kasashe 30 Na Turai Za Su Halarci Bikin Tunawa Da Nasarar Yakin Turjiyar Sinawa Kan Zaluncin Japanawa
Published: 29th, August 2025 GMT
A yau Alhamis, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya sanar da cewa, ya zuwa yanzu akwai shugabanni da tsoffin ‘yan siyasa da manyan jami’ai, da jakadun dake kasar Sin da sauransu kusan 50 daga kasashe 30 na Turai da suka tabbatar da za su halarci bikin da za a yi albarkacin cika shekaru 80 da samun nasara a yaki da kutsen Japan da yaki da mulkin danniya a duniya.
Guo ya jaddada cewa, kasar Sin ta shirya bikin ne da nufin tunawa da tarihi da magabata, da kiyaye zaman lafiya da ma tabbatar da makoma mai kyau ga bil Adama a nan gaba. (Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp ShareTweetSendShare Previous Post Shugaban NPA, Dantsoho Ya Zama Mataimakin Shugaban Kungiyar Tashoshin Ruwa Ta Duniya Relatedএছাড়াও পড়ুন:
Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya
Ya ce Sin tana maraba da kamfanonin dake fuskantar kalubale su tuntubi ma’aikatar ko hukumomi masu ruwa da tsaki, yana cewa, ma’aikatar za ta nazarci ainihin abubuwan dake faruwa da kuma bayar da damar fitar da kayayyaki ga wadanda suka cancanta. (Mai fassara: FMM)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA