Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC
Published: 16th, October 2025 GMT
Cikakkun bayanai za su biyo baya.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Likitoci sun gindaya sabon sharaɗi bayan janye yajin aiki
Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Najeriya (NARD) ta dakatar da yajin aikin da ta shafe kwanaki 29 tana yi, bayan wani taron gaggawa da Majalisar Koli ta ƙungiyar ta gudanar a ranar Asabar.
Shugaban NARD, Muhammad Suleiman, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya wallafa, inda ya bayyana cewa an dakatar da yajin aikin ne na tsawon makonni huɗu, domin bai wa gwamnatin Tarayya damar aiwatar da muhimman buƙatun da suka gabatar.
Dalilin da na koma jam’iyyar ADC — Atiku Kuɗin Cizo ya tilasta rufe fitacciyar sinima a FaransaYa ce an cimma matsayar ne bayan saka hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da ta ƙunshi ci gaban da aka samu kan manyan buƙatu 19 na ƙungiyar, ciki har da biyan bashin albashi da alawus-alawus da sauran haƙƙoƙinsu.
Suleiman ya ce Majalisar Koli ta dakatar da yajin aikin ne a matsayin wata alama ta kyakkyawan fata, domin a ci gaba da sa ido kan yadda gwamnati za ta aiwatar da alƙawuran.
Ya ƙara da cewa ƙungiyar za ta yi amfani da wannan wa’adi na makonni huɗu domin ƙara faɗakar da ’yan Najeriya da kuma ci gaba da tattaunawa da gwamnati.
Yajin aikin ƙungiyar ya bar asibitoci 91 cikin mawuyacin hali, kasancewar likitoci 11,500 — waɗanda su ne manyan ginshiƙai da ke kula da marasa lafiya a ƙasar.