2025-11-18@12:43:47 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3235

«Kwamitin Shura»:

    Masu gabatar da kara a kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) a ranar Litinin din nan sun bukaci kotun da ta zartar da hukuncin daurin rai da rai kan Ali Muhammad Ali Abd-Al-Rahman, wanda aka fi sani da Ali Kushayb, kwamandan rundunar Rapid Support Forces (RSF), saboda rawar da ya taka a...
    Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da daftarin kudurin Amurka, don ba da izinin kafa Rundunar Tsaro ta Kasa da Kasa (ISF) a Zirin Gaza. Mambobi 13 daga cikin 15 na Majalisar sun amince da kudurin, inda Rasha da China suka kaurace wa kada kuri’ar. Kudurin yana da nufin tura sojojin kasashen waje...
    Hukumar ƙwallon ƙafar Afirka CAF, ta bayyana cewa bayan tankade da rairaya da ta yi, a yanzu ’yan wasa uku kacal ne suka rage a takarar gwarzon nahiyyar na bana. A wata sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana Achraf Hakimi da Mohamed Salah da Victor Osimhen, a matsayin sauran ukun da...
    Mataimakin shugaban kasar Iran na farko ya bayyana cewa: Iran tana da kyakkyawar alaƙa ta musamman da kuma al’adu da membobin ƙungiyar haɗin gwiwa ta Shanghai Mataimakin Shugaban Kasa na Farko na Iran ya ce, “Iran tana da alaƙar haɗin gwiwa na musamman da al’adu da dukkan ƙasashe membobin Ƙungiyar Haɗin Kan Shanghai (SCO), kuma...
    Jagoram juyin juya halin Musulunci da kan sa ya jagoranci yaki da harkokin al’umma a lokacin yakin wuce gona da iri na karshe kan Iran Kakakin Rundunar Tsaron kare Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC), Brigadier Janar Ali Mohammad Na’ini, ya tabbatar da cewa: Maƙiya ‘yan sahayoniyya ba su da yanayin sabon yaƙi, kuma abin da...
    Hukumar ƙididdiga ta Najeriya (NBS) ta ce hauhawar farashin kayyayaki a ƙasar ya ragu zuwa kashi 16.05 cikin 100 a watan Oktoban 2025. Cikin rahoton wata wata da hukumar ke fitarwa, ta ce hauhawar farashin ya ragu ne da kashi 1.97 idan aka kwatanta da kashi 18.02 da aka samu a watan Satumba. ’Yan Majalisar...
    An ɗaura auren Sanatan Kano ta Kudu, Abdulrahman Kawu Sumaila, da Aisha Isah, wata jami’ar soji a Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, a wani ɗan ƙwarya-ƙwaryan biki da aka gudanar sali-alin a Rano. Ɗaurin auren wanda jama’a kaɗan ne suka halarta ya gudana ne da safiyar Litinin ɗin nan a fadar Sarkin Rano da ke...
    Ma’aikatar raya al’adu da yawon bude ido ta kasar Sin ta fitar da sanarwa a jiya Lahadi, wadda ke kira ga al’ummunta da su yi taka-tsantsan a kwanakin nan wajen zuwa yawon bude ido kasar Japan. Game da hakan, masani a kwalejin bincike ta Nomura Takahide Kiuchi, ya bayyana a jiyan cewa, raguwar yawan Sinawa...
    Rahotanni sun bayyana cewa bangarorin falasdinawa sun yi watsi da kudurin da aka kaddamar ga kwamitin sulhu na majalsar dinkin duniya na shirin aikewa da sojojin ketare zuwa yankin Gaza sun yi kira ga kasar Aljeriya da sauran mambobin da ba na dindin ba a kwamitin sulhu da su kalubalance shi. Daftarin kudurin an tsara...
    Asusun Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND) ya bayyana cewa ya raba jimillar kuɗi Naira biliyan 116 domin tallafa wa dalibai a faɗin ƙasar nan wajen biyan kuɗin makaranta da kuma kula da rayuwarsu ta yau da kullum. Shugaban NELFUND, Akintunde Sawyerr ya bayyana a Abuja cewa, daga cikin kuɗin, an tura Naira biliyan 65 aka...
    Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa za ta dauki mataki idan idan Kwamitin Gwamnonin Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) ya amince da wani sabon kuduri da bai dace da Iran ba. Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran Kazem Gharibabadi, ne ya bayyana hakan, a gefen taron kasa da kasa mai taken ‘’yancin kasa da...
    Babban jirgin ruwan yaki mai dakon sojojin kasa da sauran kayan yaki da ake amfani da su a kan-tudu samfurin 076 irinsa na farko a kasar Sin mai suna Sichuan, ya koma tashar jiragen ruwa da ke birnin Shanghai da misalin karfe 5 na yamma a yau Lahadi, bayan kammala gwajinsa na farko a teku....
    Gwamntin daliban ta kasar Afghnistan ta sanar da sauya akalar harkokin kasuwancinta ta hanyar iran da tsakiyar asiya, domin rage dogaro da kasar Pakistan a lokacin da zaman tankiya ya kara Kamari tsakanin makwabtan guda biyu da ya kai ga rufe iyakokinsu. A wani yunkuri na kewaye kasar Pakistan  da kuma kaucewa matsalolin da ake...
    Dakarun kare  juyin juya halin Musulinci na Iran, sun sanar da kwace wani jirgin ruwan dakon mai a gabar tekun kudancin Makran. A cikin wata sanarwa da ta fitar IRGC ta ce rundunarta ta gaggawa ta fara bin diddigin jirgin ruwan dake dauke da tutar Tsibirin Marshall a ranar Juma’a da safe, bayan umarnin kotu...
    Kalaman tayar da husuma na firaministar Japan Sanae Takaichi, dangane da batun yankin Taiwan na kasar Sin, na ci gaba da shan suka da Allah wadai daga sassan kasa da kasa. Wani sakamakon kuri’un jin ra’ayin al’umma da kafar CGTN ta gabatar ya nuna yadda akasarin masu bayyana mahanga suka amince da cewa, matakin na...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Jakadan Sin A Japan Ya Bayyana Matukar Adawa Da Kalaman Firaminista Takaichi Dangane Da Kasar Sin November 15, 2025 Daga Birnin Sin Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya November 14, 2025 Daga Birnin Sin Sin Za Ta Mayar Da Martani Idan Har Japan...
    ’Yan banga 16 sun kwanta dama a yayin da ’yan bindiga suka yi garkuwa da mutane 42 a wani hari na daban a Ƙaramar Hukumar Mashegu da ke Jihar Neja. Aminiya ta samu rahoton cewa ’yan bindiga sun kai hare-haren ne daga ranar Alhamis zuwa Asabar, lamarin da ya sa mutane da dama yin ƙaura...
    ’Yan banga 16 sun kwanta dama a yayin da ’yan bindiga suka yi garkuwa da mutane 42 a wani hari na daban a Ƙaramar Hukumar Mashegu da ke Jihar Neja. Aminiya ta samu rahoton cewa ’yan bindiga sun kai hare-haren ne daga ranar Alhamis zuwa Asabar, lamarin da ya sa mutane da dama yin ƙaura...
    Kyaftin ɗin tawagar ƴan wasa matan Nijeriya ƴan ƙasa da shekara 17 (Flamingos), Shakirat Moshood, na cikin jerin ƴan wasa uku da suka kai matakin ƙarshe domin lashe ƙyautar Matashiyar Ƴar Wasan CAF ta 2025. Sauran ƴan wasan da ke fafatawa da ita su ne Moha El Madani daga Morocco da Adji Ndiye ta Senegal....
    Da yake ƙarin haske kan muhimman sassan da aka fi bai wa fifiko, Gwamnan ya bayyana cewa, ɓangaren tattalin arziƙi da ci gaban al’umma ne suka samu kaso mafi tsoka na kasafin kuɗin, inda aka ware sama da Naira biliyan 269 don sanya hannun jari a muhimman fannoni. Fannin ayyuka, gidaje da sufuri ne ke...
    Da misalin karfe 9:00 na safiyar yau Juma’a ne farkon matsakaicin jirgin ruwan yaki dankon jirage masu saukar ungulu na yaki samfurin 076 na kasar Sin, wato jirgin ruwa na Sichuan, ya tashi daga tashar jirgin ruwa ta kamfanin kera jiragen ruwa na Hudong-Zhonghua a Shanghai, zuwa wani yankin teku don gudanar da gwajin sufuri...
    An kashe wani da ake zargin ɗan bindiga ne, yayin wani artabu da ’yan sanda da ’yan sa-kai suka yi da wasu mahara a Jihar Kwara. Lamarin ya faru ne a ƙauyen Adekanbi, kusa da garin Bode Saadu. Kotu ta sake hana PDP gudanar da babban taronta na ƙasa Mutfwang ya musanta raɗe-raɗin sauya sheƙa...
    Kasar Cote De Voire ta sanar da tsaurara harkokin tsaro akan iyakokinta na Arewa domin fuskantar ‘yan hijira da suke kwararowa daga kasar Mali da take fama da rikicin masu dauke da makamai. Majalisar tsaron kasar “Cote De Voire” ce ta bai wa sojojin kasar umarni da su tabbatar da tsaro a kan iyakoki, kamar...
    Mataimakin ministan harkokin waje na kasar Sin Sun Weidong ya gana da jakadan Japan a Sin Kishi Nobuo bisa umurnin gwamnatin kasar a jiya Alhamis, inda ya yi tsokaci a hukumance kan kalaman da firaministar Japan Takaichi Sanae ta yi game da kasar Sin. Sun ya ce, batun Taiwan na da matukar muhimmanci cikin muradun...
    An sanya ranar 25 ga watan Nuwamba a matsayin ranar da za a fara shari’arsa kan zargin karkatar da biliyoyin kuɗi da EFCC ta gabatar. Obiano ya yi gwamna a Jihar Anambra daga 2014 zuwa 2022. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Musulmin da Aka Kashe  A Zamfara, Katsina Da Sokoto Sun Ninka Na Kiristoci...
    El-Rufa’i ya kara da cewa mutane amintattu za a ba su mukamai idan ADC ta samu nasarar kwace mulki a hannun APC a 2027, yana mai cewa cewa kashi 40 cikin dari na mukamai za su je ga matasa. Ya yi kira ga magoya bayansa da su kiyaye masu yaudara da ke kokarin raba kan...
    Annabi (SAW), shi ne farkon wanda kasa za ta tsage wa ya tashi a ranar Alkiyama, shi ne farkon wanda zai shiga Aljannah, shi ne wanda Allah ya kebanta da tsani da wasilah, shi kuma ya kebanci muminai masoyansa da ita. Allah ya girmama Manzon Allah (SAW) da abin da bai girmama wani dan Adam...
    Cibiyar dake kula da noman dabino ta kasa a Iran, ta ce kasar ta zamo ta farko wajen fitar da dabino a duniya, inda take samar da tan miliyan 1.5 a kowace shekara. Bayannin ya zayyana Kasashe goma mafiya samar da dabino a duniya wadanda su ne Masar, Saudiyya, Iran, Aljeriya, Pakistan, Iraki, Sudan, Hadaddiyar...
    Kasashen Iran da Turkiyye sun jaddada mahimmancin karfafa zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. Wannan bayyanin ya fito ne bayan tattaunawar wayar tarho data wakana tsakanin ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi, da takwaransu na Turkiyye Hakan Fidan, game da dangantakar dake a tsakanin kasashen biyu da kuma halin da ake ciki a yankin...
    Haka zalika, ya buga misali da Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, da aka yi garkuwa da shi, kuma aka biya wadanda suka sace shi miliyoyin kudade kafin a sako shi, wanda ya bayyana hakan a matsayin babban abin takaici. Dangane da batun Shugaban Amurka Donald Trump, Sultan Sa’ad ya bukaci Nijeriya da kada ta...
    Iran da China sun bayyana shirinsu na haɓaka alaƙar da ke tsakaninsu da kuma haɓaka haɗin gwiwa bisa ga yarjejeniyoyin da aka cimma tsakanin ƙasashen biyu. Jakadan Iran a China Abdolreza Rahmani Fazli ya ce a ranar Alhamis cewa Tehran a shirye take ta ƙarfafa cikakken haɗin gwiwa da Beijing a sassa daban-daban a matsayin...
    Shugaban Afirka Ta Kudu Cyril Ramaphosa ya soki Shugaban Amurka Donald Trump saboda kin halartar taron shugabannin G20 da ke tafe, yana mai gargadin cewa yunkurin ware kasar da ke karbar bakuncin taron ba zai yi wani tasiri ba ga taron ko sakamakonsa. Trump ya sanar da cewa shi ko wani jami’in Amurka ba za...
    Sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya bayyana “damuwarsa mai zurfi” game da rahotannin “mummunan kisan gillar da kuma take hakkin bil’adama masu tsanani a El Fasher,” Sudan, yana mai cewa “tashin hankali ma yana karuwa a Kordofan.” A cikin wani rubutu da ya yi a dandalin X a ranar Alhamis, Guterres ya jaddada bukatar...
    Wasu Yahudawa ’yan kama-wuri-zauna sun lalata tare da kona wani masallaci da ke gabar yammacin kogin Jodan da Isra’ila ta mamaye, kamar yadda kamfanin dillancin Labarai na Falasɗinu (WAFA) ya ruwaito a ranar Alhamis. WAFA ya ce Yahudawan sun kuma yi rubuce-rubucen batanci a bangon masallacin da ke cikin wani ƙauye a arewa maso yammacin...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya yi kira ga kasar Japan da ta janye kalaman baya-bayan nan da firaministar kasar ta furta, dangane da yankin Taiwan na kasar Sin, in ba haka ba, ta shirya girbar sakamakon danyen aikinta. Lin Jian, ya yi kiran ne yayin taron ganawa da manema labarai na...
    A yammacin wannan Alhamis ce tawagar ƙwallon ƙafar Nijeriya Super Eagles za ta fafata da ƙasar Gabon a wasan neman tikitin shiga Gasar Kofin Duniya ta 2026. Wasan da za a buga da karfe 5 na yamma a filin wasa na Prince Moulay Hassan da ke Rabat, Morocco, zai zama wasa na farko tsakanin ƙasashen...
    Cibiyar Masu Binciken Adadi ta Nijeriya (NIQS) ta yi kira ga gwamnatin tarayya da Majalisar Dokoki ta Kasa da su samar da mafita wajen kayyade kudin hayar gidaje, musamman a manyan birane, kamar Abuja. Shugaban Cibiyar, QS Kene Nzekwe ne ya yi kiran a ranar Laraba a Abuja a wani taron manema labarai don tunawa...
    Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta fitar da wani rahoto da shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi ya fitar da a ciki yake tabbatar da cewa, Iran tana aiki da dukkanin nauyin da ya rataya a wuyanta. Rahoton dai ya kunshi cewa, tun bayan yarjejeniyar birnin Alkahira na kasar Masar da aka...
    Gwamnatin Jihar Kwara ta jaddada kudirinta na ba da ingantaccen kulawa da kuma ƙarfafa matakan rigakafi ga waɗanda suka tsira daga cin zarafin jima’i da na jinsi (SGBV) a fadin jihar. Kwamishiniyar Harkokin Mata, Hajiya Opeyemi Afolashade, ce ta bayyana haka yayin ziyarar sa ido da tantance ayyuka a Cibiyoyin Tallafawa Wadanda Aka Yi wa...
    Ya yi nuni da rahoton 2021 da Cibiyar Binciken kasa ta Nijeriya ta fitar, wanda ya gano kimanin filaye da gine-ginen gwamnatin tarayya 11,866 da aka yi watsi da su a duk faɗin ƙasar.   Daga cikin manyan kadarorin da ɗan majalisar ya lissafa akwai Cibiyar Sakatariyar Tarayya da ke Ikoyi, Legas; Ginin Otal na...
    Ministocin harkokin wajen Iran da na Rasha sun tattauna ta  wayar tarho gabanin taron kwamitin gwamnonin IAEA A yayin tattaunawar Araghchi da Lavrov, sun yi musayar ra’ayi kan batutuwa daban-daban, ciki har da rikicin kan iyaka tsakanin Pakistan da Afghanistan, tare da jaddada muhimmancin yin shawarwari don warware batutuwan da ba su dace ba. Babban...
    A yammacin jiya  ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Iraki ta sanar da sakamakon farko na zaben ‘yan majalisar dokokin kasar na shekarar 2025, tare da tabbatar da cewa an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da inganci ta hanyar amfani da na’urorin lantarki. A taronta na manema labarai, Hukumar ta bayyana cewa...
    A kwanakin nan ana samun raguwar kujerun maniyyata aikin Hajji daga Najeriya, abin da ya jawo fargaba ga masu shirin zuwa kasa mai tsarki da kuma masu hidimar su. A da, Najeriya na samun kujeru sama da dubu casa’in daga gwamnatin Saudiyya, amma cikin shekaru kadan da suka gabata adadin ya ragu zuwa kusan dubu...
    Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar Shugaba Bola Tinubu na karɓo rancen Naira tiriliyan 1.15 domin cike giɓin kasafin kuɗin 2025. Amincewar ta biyo bayan rahoton da Kwamitin Majalisar Dattawa kan Lamunin Cikin Gida da na Ƙasashen Waje, ƙarƙashin jagorancin Sanata Manu Haruna, ya gabatar. Matasa 12 sun mutu a turmutsutsun neman aikin soja a...
    Rahotanni sun bayyana cewa kasar Amurka tana shirin kafa sanssanin soji  don aikewa da dubban dakaru zuwa iyakar Isra’ila da yankin Gaza, adaidai lokacin da ake fargabar wata sabuwar kasada da kuma sha’awar taimakawa gwamnatin mamaya wajen karbe ikon kula da yankin a nan gaba. Masharhanta na ganin wannan shirin yana zuwa ne saboda irin...
    Hukumar kula da aikin hajji ta kasar Iran ta bayyana cewa shugaban ga yarima mai jiran gado na kasar Saudiya  Mohammad Bin Salman a wata ziyara da suka kai birnin Riyadh a baya bayan nan. Wannan sakon yana nuna irin kokarin da ake yi ne na ganin an daidaita da kuma  kara yin aiki tare...
    Mataimakin wakilin dindindin na Sin a MDD Sun Lei, ya gabatar da jawabi yayin taron kwamitin sulhu game da batun Sudan ta Kudu da aka gudanar jiya Talata, inda ya yi kira da a inganta mika mulki cikin kwanciyar hankali a Sudan ta Kudu. Sun Lei ya ce, Sin ta bukaci dukkan bangarorin kasa da kasa da...
    Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin jihar Jigawa ta jaddada kudurin ta na ci gaba da samar da ingantaccen kiwon lafiya ga al`ummar jihar. Babban sakataren ma’aikatar lafiya na jihar, Dr. Kabiru Ibrahim ya bada wannan tabbacin a dakin taro na ma’aikatar lafiya ta jihar a Dutse. Yace ayyukan da za’a gudanar a asibitocin sun hada...
    Daga Usman Muhammad Zaria Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da Naira Biliyan daya da miliyan dari uku domin gyara da inganta tsofaffin ayyukan wutar lantarki a fadin jihar. Kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse....
    Hukumar tsaro ta DSS ta gurfanar wani matashi mai suna Innocent Chukwuemeka Onukwume, mai shekaru 27, bisa zargin kiran sojoji da su yi juyin mulki a Najeriya. Hukumar dai ta shigar da ƙarar matashin ne cikin tuhuma shida a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja. Ɗan Majalisar Wakilai daga Kano Sagir Ƙoƙi ya fice daga...