Wane Ci Gaba Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza Ta Haifar?
Published: 17th, October 2025 GMT
Kafin cimma nasarar hakan, an kwashe sama da shekaru biyu ana gwabza fada da mamaya a Gaza, lamarin da ya haddasa asarar rayuka sama da 67,000, da barnata dukiyoyin da aka kiyasta darajarsu kan kusan dalar Amurka biliyan 70, kana an lalata kusan kaso 90 bisa dari na daukacin gine-ginen dake Gaza, baya ga al’ummun zirin sama da miliyan guda da suka rasa matsugunansu.
Ko shakka babu wannan yanayi ya haifar da wani rauni da zai jima ba a manta da radadinsa a tarihin bil’adama ba. Falasdinawa da bangaren al’ummun Israila sun tafka asarar rayuka, da dukiyoyi, da kudaden kashewa a ayyukan soji, da tabarbarewar alakar sassan kasa da kasa, da ganin baiken yaki daga sassa daban daban.
Sai dai duk da haka, sassan biyu ba su da wata mafita da ta wuce neman wanzar da zaman lafiya. Don haka sassan masu ruwa da tsaki dake da hangen nesa, ke ta maimaita batun kafa kasashe biyu masu cin gashin kai, a matsayin hanya mafi dacewa ta samar da zaman lafiya mai dorewa tsakanin Falasdinu da Isra’ila.
Yanzu dai abun zuba ido a gani shi ne ko yarjejeniyar da aka cimma za ta haifar da cikakkiyar nasarar da ake fata ko a’a. Musamman batun kafuwar kasashe biyu, da baiwa Falasdinawa cikakkiyar damar jagorancin yankinsu, da sake gina Gaza, da bude kafar biyan bukatun jin kai na al’ummar zirin da suka haura miliyan 2.1.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Gabatar Da Kasafin Kudin 2026 Na Kimanin Triliyan Daya
Daga Shamsuddeen Mannir Atiku
Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta karɓi daftarin kasafin kuɗin shekarar 2026 da ya zarce naira miliyan dubu dari tara da tamanin da biyar daga bangaren zartarwa jihar.
Da yake gabatar da kasafin kudin a zauren majalisar, Gwamna Malam Uba Sani ya bayyana kasafin a matsayin na sauye-sauye da ci-gaba wanda aka tsara domin bunkasa al’umma cikin tsarin da ya haɗa kowa da kowa.
Ya ce gabatar da kasafin kuɗi muhimmin al’amari ne na dimokradiyya da ke bai wa gwamnati damar yin waiwaye, da tantance nasarorin da aka samu, da kuma fayyace hanyoyin ci gaba na shekara mai zuwa.
Gwamnan ya bayyana cewa an ware sama da naira biliyan dari shida da casa’in da tara daidai da kashi kashi 71 ga manyan ayyukan ci gaba, yayin da sama da naira biliyan dubu dari biyu da tamanin da shida daidai da kashi 29 za su tafi ga al’amuran yau da kullum.
Ya ce kaso mafi tsoka na ayyukan ci gaba ya mayar da hankali ne kan gina manyan muhimman ababen more rayuwa masu dorewa.
Rabe-raben kason sune: Ilimi ya samu kashi 25 bisa dari, sai Ayyukan Gine-gine da Cigaban KarKarkashi ma kashi 25 bisa 100, Lafiya kashi 15 bisa 100; Noma da Samar da Abinci kashi 11 bisa 100; Tsaro kashi 6 bisa 100; Ci gaban Zamantakewa kashi 5 bisa 100; Muhalli da Matakan Sauyin Yanayi kashi 4 bisa 100; sai Mulki da Gudanarwa kashi 5 bisa 100.
A nashi jawabin, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Rt. Hon. Yusuf Dahiru Liman, ya ce kasafin kuɗin 2026 ya nuna sahihiyar manufa wadda ta ƙunshi faɗaɗa ababen more rayuwa a yankunan karkara, da habbaka kwazon ma’aikata da tabbatar da ganin dukkan al’ummomi suna cin gajiyar ci gaba mai ɗorewa da ya haɗa kowa.
Rt. Hon. Liman ya jinjina ga Gwamna Uba Sani da tawagarsa a bisa gabatar da kasafin da ya dace da hangen nesan gwamnatin da ke ƙoƙarin gina Jihar Kaduna mai yalwar arziki.
Ya kuma gode wa gwamnan bisa samar da zaman lafiya, haɗin kai da sabunta kudurori a fadin jihar, tare da yabawa gwamnan bisa rashin yin katsalandan cikin harkokin majalisar wanda hakan alama ce dake nuna cikakken tsarin rabon iko da ke taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da ingantaccen sa ido da daidaito tsakanin bangarorin gwamnati.