HausaTv:
2025-09-17@20:32:15 GMT

Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Bayyana Cewa; Babu Dalilin Jin Tsoron Tattaunawa

Published: 12th, September 2025 GMT

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa; Bai kamata a ji tsoron tattaunawa ba saboda hanya ce ta jaddada zaman lafiya

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Ana gudanar da dukkan ayyukan diflomasiyya cikin cikakken hadin kai tare da hukumomin da abin ya shafa, kuma bisa takamaiman umarni da ayyuka.

Ya ce: “Ba za su taba yin kasa a gwiwa ba wajen kare hakki da tsaron al’umma, kuma ba za su taba tasirantuwa da kage-kagen yanayi ba, kuma za su yi aiki da karfi da azama wajen tabbatar da muradun al’ummar Iran.”

Wannan dai ya zo ne a wata hira da gidan talabijin na kasar Iran a yammacin jiya Alhamis, inda ministan harkokin wajen kasar Abbas Araqchi ya amsa tambayoyi kan yarjejeniyar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA suka cimma a birnin Alkahira, da kuma ci gaban da aka samu a shawarwari da kungiyar Tarayyar Turai Troika dangane da dage takunkumin kan Iran.

Da yake amsa tambaya kan ko yarjejeniyar da kuma bayanan hukumar ta IAEA game da halin da ake ciki da kuma wadatattun kayayyaki a Iran sun ba da damar sake kai hare-hare kan cibiyoyin, ya ce, “A nan, dole ne a bambanta tsakanin batutuwa biyu. Na farko, tattaunawar Iran da kasashen Turai uku, wadanda suka dade suna ci gaba da gudana tsawon lokaci. Wadannan kasashe uku har yanzu suna da’awar amincewa da yarjejeniyar makamashin nukiliyar, amma Iran ta ci gaba da gudanar da tarurrukan da suka gabata tare da su.” Ko a lokacin Yaƙin kwanaki goma sha biyu, kamar yadda za a iya tunawa, Araqchi ya yi balaguro zuwa ƙasashen waje don halartar taro da yawa na duniya. A birnin Geneva ya kuma gana tare da tattaunawa da ministocin harkokin wajen kasashen da kuma Madam Kalas, babbar wakiliyar Tarayyar Turai. An ci gaba da wannan tattaunawa bayan an gama yakin.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Wulayati: Dole Ne Duniya Ta Daina Yin Shiru Kan Ta’addancin Yahudawan Sahayoniyya September 12, 2025 Ayatullahi Khatami Ya Gargadi Kasashen Larabawa Kan Hare-Haren Gwamnatin Mamayar Isra’ila September 12, 2025 Kisan Kiyashin Kan Falasdinawa Da Sojojin Mamayar Isra’ila Ke Yi A  Yau Ya Lashe Rayukan Mutane 48 September 12, 2025 Tafiya Sallah Ta Kubutar Da Shugabannin Kungiyar Hamas Daga Kisan Gillar Gwamnatin Mamayar Isra’ila September 12, 2025 Qatar : shugabannin Isra’ila na kishirwar jefa duniya cikin rikici September 12, 2025 Guteress ya tattauna da Araghchi kan shirin shurin nukiliyar Iran  September 12, 2025 Netanyahu, ya sha alwashin dakile kafa kasar falasdinawa September 12, 2025 Araghchi ya caccaki kasashen Turai kan yin biris da cin zarafin Amurka da Isra’ila kan Iran September 12, 2025 Venezuela ta yi gargadi game da karuwar sojojin Amurka a cikin tekun Caribbean September 12, 2025 Kwamitin Sulhu ya yi Allah-wadai da harin da aka kai kan Qatar September 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: harkokin wajen

এছাড়াও পড়ুন:

Larijani: Iran Da Saudiyya Za Su Bunkasa Aiki Tare A Fagagen Kasuwanci Da Tsaro

 Babban sakataren majalisar koli ta tsaron jamhuriyar musulunci ta Iran Dr. Ali Larijani ya bayyana cewa; Za a bunkasa aiki tare a tsakanin Iran da Saudiyya a fagagen tattalin arziki da kuma tsaro.

Dr. Larijani ya bayyana hakan ne jim kadan bayan fitowar daga ganawar da ya yi da Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mu8hammad Bin Salman.

Bugu da kari Dr. Ali Larijani ya ce a yayin ganawarwa da Yarima mai jiran gado na Saudiyya Muhammad Bin Salman, sun tattauna hanyoyin bunkasa alakar kasashensu ta fuskoki mabanbanta, da kara girman wannan alakar ta fuskar tattalin arzki da tsaro fiye da yadda take a yanzu.”

Haka nan kuma ya ce, za a yi aiki domin kawar da dukkanin abubuwan da suke kawo cikas a kan hanyar bunkasa wannan alakokin.

Dr. Ali Larijani ya kuma ce,an yi shawara akan yadda kasashen yankin za su bunkasa alakarsu ta tsaro domin ganin an tabbatar da zaman lafiya.

Da aka tambaye shi akan ko an sami sauyi akan mahangar kasashen Larabawa bayan harin da HKI ta kai wa Qatar, Dr.Ali Larijani ya ce; Tabbas da akwai sauyi a cikin yadda kasashen larabawa suke Kallon abubuwan da suke faruwa, domin suna ganin cewa kasantuwar HKI a cikin wannan yankin yana hana zaman  lafiya.

Babban sakataren Majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya ziyarci Saudiyya inda ya gana da ministan tsaronta da kuma Yarima mai jiran gado Muhammad Bin Salman.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hukumar Tarayyar Turai Ta Gabatar Da Shawarar Jingine Aiki Da Yarjejeniyar Kasuwanci Da HKI September 17, 2025  Gaza: HKI Tana Ci Gaba Da Yi Wa Falasdinawa  Kisan Kiyashi A Gaza September 17, 2025 Ma’aikatar Shari’ar Iran Ta Sanar Da Rataye Dan Leken Asirin Hukumar Mossad Ta Isra’ila September 17, 2025 Hamas Ta Karyata Gwamnatin Mamayar Isra’ila Kan Shirga Karya Don Kare Muggan Manufofinta September 17, 2025 Iran Ta Bayyana Abubuwan Da Bata Amince Da Su Ba A Jawabin Bayan Taro Na Kungiyar OIC A Birnin Doha September 17, 2025 Chadi:  Majalisa ta amince a baiwa shugaban kasa  damar ci gaba da Mulki har karshen rayuwa September 17, 2025 Iran Ta Bukaci Musulmi Su Goyi Bayan Yunkurin Kasa da Ka Na Kauracewa Isra’ila September 17, 2025 Kwamitin bincike na MDD ya zargi Isra’ila da aikata “kisan kare dangi” a Gaza September 17, 2025 Iran da Saudiyya sun bukaci hadin kan Musulmi game da halin da ake a yankin September 17, 2025 Duniya na tir da sabon farmakin Isra’ila kan Gaza September 17, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Larijani: Iran Da Saudiyya Za Su Bunkasa Aiki Tare A Fagagen Kasuwanci Da Tsaro
  • Iran Ta Bayyana Abubuwan Da Bata Amince Da Su Ba A Jawabin Bayan Taro Na Kungiyar OIC A Birnin Doha
  • Iran Ta Gabatar Da Sabbin Kayayyaki Guda 5 A Wajen Taron Kolin kere-kere .
  • Pezeshkian: Saudiyya Na Iya Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Samar Da Hadin Kan Kasashen Musulmi
  • Kungiyar Human Rights Watch; Isra’ila Ta Kashe ‘Yan Jarida Fiye Da 30 A Kasar Yemen Ne Da Gangan  
  • Ministan Tsaron Kasar venezuela Ya Gargadi Amurka Dangane Da Kokarin Juyin Mulki A Kasar
  • Fira Ministan Spain: Bai Kamata A Rika Barin “Isr’ila” Tana Shiga Gasar
  •  Dan Kasar Iran Mai Kirkira Ya Sami Kyautar Yabo A Kasar China
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Qatar, Turkiyya, Pakistan Da Labanon A Doha
  • Gwamnatin Sudan Ta Ce: Babu Sulhu Da ‘Yan Tawayen Kasar Na Kungiyar Rapid Support Forces