A yayin shari’ar, wanda ake tuhumar ya musanta zargin, sai dai kotun ta ce masu gabatar da kara sun gabatar da shaida wadda ta gamsar da ita ba tare da wata shakka ba. Mai shari’a Dahiru ya ce laifin ya ci karo da sashe na 284 na kundin laifuffuka, wanda ya haramta yin jima’i ba bisa ka’ida ba, don haka ya yanke wa Hayatu Muhammad hukuncin daurin shekaru hudu a kan kowanne daga cikin tuhumomin biyu, wanda zai fara ne tun ranar da aka kama shi.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Sojoji Sun Yi Juyin Mulki A Ƙasar Madagascar October 15, 2025 Labarai Gwamnan Kaduna Ya Taya Al’Amin Murnar Nasarar Lashe Gasar Ƙirƙirar Fasaha Ta Duniya A Ƙasar Birtaniya  October 15, 2025 Manyan Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Hauhawar Farashin Kayayyaki A Nijeriya Ya Ƙara Raguwa Zuwa Kashi 18.02% October 15, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Hukumar Hisbah Ta Kama Wasu Matasa Da Suka Yi Aure Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Kano

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wasu ma’aurata da wasu mutane biyar bisa zarginsu da gudanar da ɗaurin aure ba tare da izinin iyayensu ba ko kuma bin tsarin addinin Musulunci a unguwar Nasarawa da ke cikin birnin Kano. Wadanda ake zargin sun hada da ango mai suna Aminu mai shekaru 23 da amaryarsa Sadiya mai shekaru 22. Sauran wadanda aka kama su ne Umar mai shekaru 24 wanda ya kasance wakilin ango; Abubakar, mai shekaru 23, wanda ya kasance waliyyin amarya; Usaina, mai shekaru 21; da kuma wasu ‘yan mata guda biyu wadanda suka kasance shaidu a yayin ɗaurin auren. Ahmed Musa Ya Nemi Afuwar Ƙungiyar 3SC Akan Abinda Ya Faru Da ‘Yan Wasansu A Kano Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 236 A Jihohi 27 Da Birnin Tarayya Rahotanni sun bayyana cewa, an ɗaura auren ne akan sadaki Naira 10,000, ba tare da amincewar iyayen ma’auratan ba. Da yake tabbatar da faruwar lamarin, mataimakin babban kwamandan hukumar ta Hisbah, Dr. Mujaheeddeen Aminuddeen, ya ce an kama wadanda ake zargin ne biyo bayan korafe-korafen da ‘yan unguwar suka kai wa hukumar. Ya bayyana cewa, matakin da wadanda ake zargin suka ɗauka ya saɓawa koyarwar addinin Musulunci da kuma dokokin aure na jihar, yana mai jaddada cewa, hukumar ta Hisbah ba za ta amince da duk wani abu da ya saɓawa tsarin addini da na shari’a a jihar Kano ba. Dr. Aminudeen ya kara da cewa, a halin yanzu wadanda aka kama suna hannun Hisbah domin ci gaba da bincike. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Ra'ayi Riga Labarin Xinjiang A Zane: Aikin Yawon Shakatawa Na Kara Samar Da Arziki Ga Al’ummar Xinjiang October 13, 2025 Labarai Ba Gudu Ba Ja-da-baya Kan Ci Gaba Da Kwaskwarima Ga Tsarin Haƙar Ma’adanai – Minista October 13, 2025 Manyan Labarai Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 236 A Jihohi 27 Da Birnin Tarayya October 13, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kotu ta aike da mutumin da ake zargi da satar yaran Kano yana kaiwa Delta zuwa gidan gyaran hali
  • Gidauniyar Sheikh Dahiru Bauchi Ta Tura Ɗalibai 117 Karatu Ƙasar Algeria 
  • Kotu A Kano Ta Tsare Wani Mai Gidan Marayu Bisa Zargin Satar Yara Da Safararsu Zuwa Delta
  • Kamaru: Jam’iyyun adawa sun ayyana Bakary a matsayin wanda ya lashe zaɓe
  • NPFL Ta Ci Tarar Kano Pillars ₦9.5m, Ta Rage Mata Maki 3 Da Ƙwallaye 3
  • Zargin Batanci: An Sasanta Da Malam Lawal Triumph Da Majalisar Shura Ta Kano
  • Majalisar Shura ta fara ganawar sirri da Malam Triumph
  • Hukumar Hisbah Ta Kama Wasu Matasa Da Suka Yi Aure Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Kano
  • Zaɓen Kamaru: Tchiroma Bakary na da kwarin gwiwa a yayin da ake jiran sakamako