Leadership News Hausa:
2025-12-01@05:07:56 GMT

Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

Published: 16th, October 2025 GMT

Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

 

“Muna roƙon Allah (T) Ya kawo mana ƙarshen wannan matsala ta tsaro a duk faɗin Jihar Zamfara, Arewa da ma Nijeriya baki ɗaya.”

 

Lamarin ya jawo damuwa daga al’umma da shugabannin siyasa, yayin da hukumomin tsaro ke ƙara ƙoƙari wajen gano waɗanda suka aikata wannan mummunan laifi da tabbatar da zaman lafiya a yankin.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Amince Da Amupitan A Matsayin Shugaban INEC October 16, 2025 Labarai Gwamnatin Tarayya Za Ta Tallafa Wa Fursunoni Bayan Kammala Zaman Kurkuku October 16, 2025 Manyan Labarai Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC October 16, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Ƙasar Japan ta fara sayar da injin da ke yi wa mutane wanka

An fara sayar da wani inji da ke yi wa mutum wanka bayan ya burge baƙi a lokacin bajekolin duniya a Japan, in ji wata mai magana da yawun kamfanin da ya ƙera injin, a ranar Juma’a.

Masu amfani za su kwanta su rufe kansu a cikin injin da wani murfi, sannan ya wanke su kamar yadda ake wanke kaya a injin wanki, amma ba tare da ya jujjuya su ba, yayin da kiɗa ke tashi a ciki.

An gabatar da samfurin na’urar, mai suna “injin wankin ɗan adam”, kuma an sami dogayen layuka a baje kolin watanni shida da aka kammala a Osaka a watan Oktoba bayan ya sami halartar fiye da mutum miliyan 27.

Kamfanin Japan mai suna Science ne ya ƙera shi, kuma wannan na’urar sabuwa ce a kan irin ta da aka nuna a Osaka, a shekarar 1970.

“Injiniyanmu shugaban kamfani ya samu wahayi daga wannan tun yana ƙaramin yaro mai shekaru 10 a lokacin,” in ji mai magana da yawun Science, Sachiko Maekura, ga AFP.

Na’urar “ba wai tana wanke jiki kaɗai ba, har ma da ruhinka,” in ji ta, tare da lura da bugun zuciya da sauran muhimman alamomin lafiyar masu anfani da shi.

Bayan wani kamfanin shakatawa daga Amurka ya tuntubi Science don ganin ko za a shigar da samfurin fasahar kasuwa, sai kamfanin ya yanke shawarar samar da shi a zahiri.

Wani otal a Osaka ya sayi na’urar ta farko kuma yana shirin fara amfani da ita ga baƙin otal ɗin, in ji mai magana da yawun kamfanin.

Sauran abokan cinikin na’urar sun haɗa da Yamada Denki, babban kamfanin dillancin kayan lantarki a Japan, wanda ke fatan na’urar za ta jawo mutane zuwa shagunan su, in ji ta.

“Saboda wani bangare na jan hankalin wannan na’ura shi ne ƙarancinta, muna shirin samar da kusan guda 50 ne kawai,” in ji Maekura.

Jaridun ƙasar ta Japan sun rawaito cewa farashin siyarwa zai kasance yen miliyan 60, kwatankwacin sama da Naira miliyan 500.

AFP

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sojoji sun ceto mutum 7 da ’yan bindiga suka sace a Kano
  • Dalilin da na koma jam’iyyar ADC — Atiku
  • Iran A Shirye Take Ta Maida Martani Mai Kan Kan Duk Wata Barazanar Tsaro  
  • Muna buƙatar taimakon ƙasashen waje kan tsaro a Najeriya — Obasanjo
  • Barau ya musanta zargin gwamnatin Kano, ya soki gwamna Abba
  • DSS ta gayyaci Datti Baba-Ahmed kan zargin kalaman tayar da hankali
  • Gwamnatin Kano ta nemi a binciki Ganduje kan zargin kalaman ta da hankali
  • Ƙasar Japan ta fara sayar da injin da ke yi wa mutane wanka
  • Ya kamata ’yan majalisar Najeriya su koma zaman wucin gadi – Ndume
  • An janye ’yan sanda 11,566 daga yi wa manyan mutane rakiya – Egbetokun