Tsohon Ɗan Majalisar Bayelsa Ya Shawarci Jonathan Ya Guji Neman Takara A 2027
Published: 17th, October 2025 GMT
Tsohon ɗan majalisar wakilai daga jihar Bayelsa, Israel Sunny-Goli, ya shawarci tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan da ya guji duk wata matsin lambar da wasu ƴan siyasa ke yi masa na ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Sunny-Goli ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin halartar shirin Politics Today na tashar Channels, inda yake mayar da martani kan ficewar gwamnan Bayelsa, Douye Diri, daga jam’iyyar PDP.
Ya ce, tun bayan barin ofis a 2015, tasirin siyasar Jonathan ya ragu, kuma babu wani alamar da ke nuna yana son komawa cikin harkar siyasa kai tsaye. “Bai nuna wata alama ta shiga siyasa ba, tun bayan barin mulki,” in ji shi.
Sunny-Goli ya ƙara da cewa tsohon shugaban ya fi dacewa ya ci gaba da mayar da hankali kan ayyukan zaman lafiya da hulɗa da ƙasashen duniya maimakon komawa cikin rigimar siyasa a gida, musamman a yayin da ake ganin yanayin siyasa a Bayelsa na ya sauya.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Sabon shugaban INEC ya halarci Majalisar Dattawa don tantancewa
Sabon shugaban Hukumar zaɓen Najeriya mai zaman kanta INEC, Joash Ojo Amupitan ya halarci zauren Majalisar Dattawan Najeriya domin zaman tantance shi.
Amupitan ya halarci zauren Majalisar tare da rakiyar Gwamnan Jihar Kogi, Ahmed Ododo da wasu jami’an gwamnati.
Za a kafa kamfanin ƙera kayan sola a Kano Kashi 16 na ’yan Najeriya ne kawai ke da wajen wanke hannu — UNICEFDa misalin ƙarfe 12:50 na rana ne, mai baiwa shugaban Ƙasa shawara kan Harkokin Majalisar Dattawa (Majalisar Dattawa), Sanata Abubakar Lado ne ya shigar da sabon shugaban INEC zuwa zauren majalisar dattijai, kuma tuni ya zauna gabanin fara aikin tantance shi.
An bar Amupitan ya shiga zauren majalisar ne bayan shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele ya bayar da umarnin a samar da doka ta 12 domin ba wa baƙi damar shiga zauren majalisar, kuma shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Abba Moro ya mara masa baya.
Matakin na zuwa ne bayan Shugaba Tinubu ya aike wa majalisar wasiƙar buƙatar tantance shi.
A makon da ya gabata ne dai majalisar magabatan ƙasar ta amince da naɗin Farfesa Amupitan a matsayin wanda zai jagoranci hukumar zaɓen INEC.
Bayan tantancewa da amincewar majalisar dattawan, Shugaba Tinubu zai rantsar da shi a matsayin shugaban hukumar ta INEC.