Ministan harkokin wajen kasar Iran da takwaransa na Tunisiya sun jaddada cewa: Warware matsalar Falasdinu na bukatar kawo karshen mamayar da ake yi

Ministocin harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Tunisiya sun jaddada cewa: Warware matsalar Falastinu na bukatar kawo karshen mamaya da kuma tabbatar da hakkin al’ummar Falastinu na cin gashin kansu.

Wannan dai na zuwa ne a yayin ganawar da ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Araqchi da ministan harkokin wajen kasar Tunisiya Mohamed Ali Nafti suka yi a ranar Laraba a gefen taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar ‘yan ba ruwan mu ta NAM karo na 19 a birnin Kampala na kasar Uganda.

A yayin wannan ganawar, bangarorin biyu sun yi nazari kan ci gaban da aka samu a dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da suka hada da shirye-shiryen taron hukumar tattalin arziki ta hadin gwiwa, tare da tabbatar da aniyar kasashen biyu na karfafa alaka da hadin gwiwa a dukkan fannoni.

Har ila yau, sun yi musayar ra’ayi kan abubuwan da ke faruwa a yankin yammacin Asiya da kuma mamaye Falastinu bisa fahimtar da aka cimma a Masar na dakatar da kisan kare dangi. Sun jaddada nauyin da ke wuyan kasashen da ke ba da tabbacin hana yahudawan sahayoniyya karya yarjejeniyar da aka cimma.

An jaddada cewa warware matsalar Falastinu na bukatar kawo karshen mamayar da ake yi da kuma tabbatar da hakkin al’ummar Falastinu na cin gashin kansu, sannan kuma wajibi ne a bin doka da oda da kuma wajibi kasashe su goyi bayan al’ummar Falastinu wajen aiwatar da wannan muhimmin hakki da ‘yantar da kansu daga mamaya da kuma kangin fuskantar nuna wariyar al’umma da kuma mulkin mallaka.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kasar Afirka Ta Kudu Ta Jaddada Aniyarta Ta Ci Gaba Da Shari’ar Neman Hukunta Isra’ila Kan Batun Gaza October 16, 2025 Gwamnatin Kamaru Ta Gargadi Dan Takarar Da Ya Shelanta Kansa A Matsayin Wanda Ya Lashe Zabe October 16, 2025 Ministocin Harkokin Wajen Kungiyar NAM Sun Nuna Goyon Bayansu Ga Venezuela October 16, 2025 Sojojin Pakistan Sun Tarwatsa Tankokin Yaki 6 Na Afghanistan A Rikicin kan Iyaka October 15, 2025 Tawagar Super Eagles Ta Nijeriya Ta Lallasa Benin Da ci 4-0 A Uyo October 15, 2025 Matakin Kasashen Yamma Na Maidowa Da Iran Takunkumi Ya Sabawa Doka. October 15, 2025 Kasar Indunusiya Ta Sanar Da Goyon Bayanta Ga Alummar Falasdinu October 15, 2025 Isra’ila  Za Ta Sake Kai Hare-hare Idan Ta Karbi Dukkan Mutanenta Da Hamas Ta Kama. October 15, 2025 Trump Ya Fadawa Hamas Su Mika Makamansu Ko Kuma A Kwace Su Da Karfi October 15, 2025 Iran Ta Samarda Sabbin Hanyoyi Na Fuskantar  Barazanar Makiya October 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Araghchi : Trump bai cancanci mai samar da zaman lafiya ba yayin da yake haifar da yake-yake

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya caccaki Donald Trump kan manufofinsa a yammacin Asiya, yana mai cewa shugaban Amurka ba zai iya da’awar samar da zaman lafiya a yankin ba yayin da yake aiwatar da manufofin wuce gona da iri da kuma hada kai da “masu aikata laifukan yaki.”

A cikin wani sako a shafinsa na X, Abbas Araghchi ya ce ikirarin da Trump ya yi a baya-bayan nan na cewa “ya rage makwanni” Iran ta kera makamin nukiliya kafin harin da Amurka da Isra’ila suka kai kan cibiyoyin nukiliyarta ” karya ce.”

“Wannan kawai KARYA ce tsungurungum dinta, kuma ya kamata a sanar da shi cewa babu tabbacin hakan, kamar yadda jami’an leken asirinsa suka tabbatar masa.”

Jami’in diflomasiyyar na Iran ya yi Allah-wadai da matakin da Amurka kan hare-haren da aka kai wa Iran a watannin baya, wanda ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula sama da 1,000 da suka hada da mata da kananan yara.

Araghchi ya ce Trump “na iya zama shugaban zaman lafiya ko kuma shugaban yaki, amma ba zai iya zama duka a lokaci guda ba.”

Ministan na Iran na maida martini ne kan yadda Trump ya bayyana kansa a matsayin mai samar da zaman lafiya da kuma kalamansa na cewa zai samar da zaman lafiya mai dorewa a fadin yankin, tare da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu.

Araghchi ya ce Iran tana shirye ga “mutunta duk wani yunkurin na diflomasiyya domin cin moriyar juna,” amma kasar ba za ta amince da barazana ko tilastawa ba.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka UNDP : An ruguza fiye da kashi 80 cikin 100 na gine-ginen Gaza October 14, 2025 Sojojin Madagaska sun karbe mulkin kasar October 14, 2025 Trump ya ce zai yi shawara game da batun kafa kasar Falasdinu October 14, 2025 Islamic Jihad : jarumtakar ‘yan gwagwarmaya ce ta haifar da sako fursunonin falasdinawa October 14, 2025 Aragchi Yana Uganda Don Halattan Taron Ministocin Kungiyar NAM October 14, 2025 Iran Ta Jadda Cewa A Shirye Take Ta Kare Kanta A Duk Wani Yaki Wanda Makiya Zasu Dora Mata October 14, 2025 Ma’aikatar Harkokin wajen Kasar Iran Ta Yi Tir Da Jawabin Trump A Knesset Ta HKI October 14, 2025 An Gudanar Gagarumar Zanga Zangar Goyon Bayan Falasdinawa A Australia Da Indonasia October 14, 2025 Syria: Busaina Sha’aban Ta Karyata Labaran Da Aka Danganta Ma Ta Na Ganawa Da Jami’an Iraniyawa October 14, 2025 Mahalarta Taron ‘Sherm-Sheikh” Sun Rattaba Hannu Akan Yarjejeniyar Zaman Lafiya October 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran Ta Jaddada Cewa: A Shirye Take Ta Tattauna Amma Ba Zata Amince Da Juya Akalarta Ba
  • Matakin Da Kasashen Yamma Su Ka yi Na Maidowa Da Iran Takunkumi Ya Sabawa Doka.
  • Trump Ya Fadawa Hamas Su Mika Makamansu Ko Kuma A Kwace Su Da Karfi
  • Iran Ta Yi Allah Wadai Da Kalaman Kin Jinin Iran Da Trump Ya Yi A Majalisar Dokokin Isra’ila                             
  • Araghchi : Trump bai cancanci mai samar da zaman lafiya ba yayin da yake haifar da yake-yake
  • Aragchi Yana Uganda Don Halattan Taron Ministocin Kungiyar NAN
  • Ma’aikatar Harkokin wajen Kasar Iran Ta Yi Tir Da Jawabin Trump A Knesset Ta HKI
  • Iran: Kakabawa Kasa Mai Makwabta 16 Takunkumi Ba Abu Ne Mai Sauki Ba.
  • Iran Ta Ki Zuwa Masar Saboda Bata Son Haduwa Da Azzaluman Da Suka Kashe Falasdinwa A Gaza