Gaza : Adadin Wadanda sukayi shahada a hare-haren Isra’ila cikin sa’o’I 24 ya karu
Published: 6th, September 2025 GMT
A cikin sa’o’i 24 da suka gabata, akalla Falasdinawa 68 ne suka yi shahada a Zirin Gaza, wanda ya kawo adadin wadanda suka rasu a yakin kisan kare dangi na Isra’ila tun watan Oktoban 2023 zuwa sama da 64,368.
Akalla Falasdinawa tara ne sukayi shahada a wani kazamin harin da aka kai ta sama a birnin Gaza da Khan Yunus, ciki har da takwas lokacin da aka kai hari kan wani gini a unguwar Sheikh Radwan.
Kamfanin dillancin labaran iqna, ya nakalto cewa, a ranar Asabar, wani yaro ya yi shahada a wani harin da Isra’ila ta kai kan wata mota a sansanin al-Mawassi da ke Khan Yunis.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, bayan harin bam da Isra’ila ta kai kan cibiyar rarraba kayan agaji a kudancin Wadi Gaza da ke tsakiyar yankin zirin Gaza, an kashe wasu Falasdinawa biyu tare da jikkata wasu akalla 17.
Dama kafin hakan, an kashe wasu Falasdinawa shida da ke jiran agajin jin kai sakamakon harbin da Isra’ila ta yi musu a kusa da wata cibiyar rarraba kayayyaki a kudu maso yammacin birnin Khan Younis, kamar yadda majiyar ta ruwaito.
A wani labarin kuma, Majiyoyin Falasdinawa sun rawaito cewa, da gangan sojojin Isra’ila suka kai hari kan Hasumiyar Al-Soussi, wani gini da ke dauke da dimbin al’ummar Gaza da suka rasa matsugunansu a ranar Asabar. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da majalisar zartaswar firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ta amince da “Operation Gideon’s Chariots II”, wanda ke da nufin kwace iko da birnin Gaza.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kungiyoyin gwagwarmaya sun fusata da barazanar Isra’ila na bude “kofofin jahannama” a Gaza September 6, 2025 Iran ta aike da kayayyakin jin kai tan 100 zuwa Afghanistan September 6, 2025 Ammar Hakeem ya gana da larijani a nan birnin Tehran . September 6, 2025 HKI Ta Kashe Falasdinawa 50 A Harin Da Takai A Yankin Gaza September 6, 2025 An yi Kira Ga El-rufai Da Ya yi Hattara Da Kalamansa September 6, 2025 An Gudanar Da Zanga-zangar Adawa Da Shirin Amurka Na Kwace makaman Hizbullah. September 6, 2025 Manyan Jami’an Kungiyar Hamas sun Gana Da Minister Harkokin Wajen Iran September 6, 2025 Afirka za ta iya samun tagomashi wajen habaka tattalin arzikin dijital – IFC September 6, 2025 Araqchi: Kasashen Turai Suna Nuna Son Kai A Kan Batun Hana Kera Makamin Nukiliya September 6, 2025 Kasar Iran Ta Bayyana Lokacin Sabon Zagaye Na Tattaunawa Tsakaninta Da Hukumar IAEA September 6, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Bukaci IAEA Tayi Tir Da Harin Da Isra’ila Ta Kai A Tashoshin Nukiyarta.
Mohammad Islami shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya na Iran ta fadi a bayan taron da hukumar ta IAEA dake gudanarwa a Vienna yanzu haka cewa yana neman hukumar ta IAEA ta goyi bayan kudurin da ta fitar kuma ta yi Tir da harin wuce gona iri da hki ta kai kan tashoshin nukiliyarta.
Wakilai guda 180 a hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ne suka hallara abirnin viyana daga ranar 15-19 domin gudanar da taron kasa da kasa karo na 69 da hukumar ta duniya ke shiriya a hedkwatarta dake Vienna na kasar Austeria
Yace mun bayyana cewa alummar Iran basu da rauni wajen fuskantar duk wata barazana, kuma basu da niyyar mika wuya, ,ya kara da cewa ilimin nukiliyar Iran na asalai ne kuma ba zaa iya share shi ta hanyar tayar da bama bamai ba.
.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Jonathan Zai Jagoranci Taron Tattaunawa Kan Dimokuraɗiyya A Ghana September 16, 2025 Pezeshkian: Saudiyya Na Iya Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Samar Da Hadin Kan Kasashen Musulmi September 16, 2025 Pezeshkian: Ta’addancin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Kan Kasar Qatar Zalunci Ne Ga Diflomasiyya September 16, 2025 Baqa’i: Kowace Kasa A Duniya Tana Da Hakkin Mallakar Makamashin Nukiliya Na Zaman Lafiya September 16, 2025 Kungiyar Human Rights Watch; Isra’ila Ta Kashe ‘Yan Jarida Fiye Da 30 A Kasar Yemen Ne Da Gangan September 16, 2025 Kungiyar Kare Hakkokin Bil’Adama Ta Siriya Ta Bankado Karin Fararen Hula Da Aka Kashe A Rikicin Suweida September 16, 2025 Tawagar Yan Wasan Damben Gargajiya Ta Iran Ta Zama Zakara A Damben Ta Duniya September 16, 2025 An Fara Taron Hukumar Makamashin Nukliya Ta Duniya IAEA Karo Na 69 A Birnin Vienna September 16, 2025 Espania Ta Soke Cinikin Makamai Na EUR Miliyon 700 Da HKI Saboda Kissan Kiyashi A Gaza September 16, 2025 Makaman ‘Drons’ Na Yemen Sun Fada Kan Wurare Masu Muhimmanci A HKI September 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci