Tallafin Walwalar Jama’a: Yadda Gwamnatocin Biranen Kasar Sin Ke Jifan Tsuntsu Biyu Da Dutse Daya
Published: 28th, August 2025 GMT
Lardin Hubei shi ma ya bi sawu, inda ya bullo da nasa shirye-shiryen na raba takardun tallafin tare da mai da hankali musamman a kan bangaren da ya shafi cin abinci. Babban makasudin hakan shi ne a karfafa mutane su rika fita zuwa gidajen cin abinci. Wannan ya kara farfado da salon cin abinci tare a tsakanin Sinawa da kuma kwarya-kwaryan harkokin da ake yi a gefen wasu tituna bisa tsari.
Shi ma birnin Shanghai ba a bar shi a baya ba a kan wannan sabga, inda shi kuma ya mayar da hankali a kan nishadantarwa ta fuskar al’adu. Birnin ya ware makudan kudi yuan miliyan 500 domin karfafa zuwan jama’a wurare da dandaloli na wasannin kwaiwakyo, da wasannin ban dariya, da harkokin wasanni na zamani da sauransu, inda a zagayen farko aka fara kashe yuan miliyan 30. A karkashin wannan tsarin na tallafi, mutane sun kashe fiye da yuan miliyan 91 a bangaren wasanni a birnin na Shanghai.
Shi kuwa lardin Zhejiang ya zo da wani salo ne na musamman mai hangen nesa, inda ya hade wasanni da yawon bude ido a bangaren karfafa walwalar jama’a da kashe kudi. Masu sha’awar kwallon kwando suna amfani da tikitin wasanni mai rangwame da lardin yake bayarwa don garzayawa wuraren wasanni masu jan hankali, da gidajen abinci da sauransu. Yin hakan wata fasaha ce ta karfafa hanyoyin taimakawa ci gaban tattalin arzikin cikin gida ta fuskar tsarin gudanar da rayuwar jama’a.
A can birnin Guangzhou ma, sama da mazauna birnin miliyan 6 ne suka yi amfani da takardun tallafin cin abinci, inda aka kashe yuan miliyan 409. Hakika wannan yana nuna cewa, duk lokacin da aka buda wa mutane sararin shiga a dama da su, to za su yi hakan da zuciya daya kuma cikin jin dadi.
A kwanan nan, wasu mahukunta a kasar Sin sun jaddada bukatar kara fadada hanyoyin cin gajiyar harkokin rayuwa na yau da kullum da ake kashe kudi wajen gudanar da su, don haka wadannan dabaru da gwamnatocin biranen suka bullo da su, suna ba su damar jifan tsuntsu biyu da dutse daya, ga amfanin da za a samu ta fuskar karuwar tattalin arziki musamman ga kananan masu sana’o’i, ga kuma inganta jin dadi da walwalar jama’a. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya
A daidaikun kasuwannin Abuja da wasu manyan birane na ƙasar nan, an bayyana yadda farashin doya ke ƙara hawa fiye da yadda ake tsammani.
Wannan na faruwa ne duk da cewa yanzu sabuwar doya ta fara shigowa kasuwa, bisa al’ada, a duk shekara fitowar sabuwar doya kan karya farashin wanda yake kasuwa. Sai dai a bana, wasu daililai na sa farashin doya kara hawa.
NAJERIYA A YAU: Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau Ukuwannan shine batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba akai.
Domin sauke shirin, latsa nan