Isra’ila Za Ta Sake Kai Hare-hare Idan Ta Karbi Dukkan Mutanenta Da Hamas Ta Kama.
Published: 15th, October 2025 GMT
Ministan kula da ayyukan soji na HKI Katz ya bayyana cewa dakarun sojin Isra’ila za su koma da kai hare-hare a yankin Gaza, bayan ta kammala karbar dukkan mutanen ta da kungiyar Hamas ta kama, don nuna rashin amincewa da sabuwar yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma tsakanin Hamas da kuma gwamnatin tel Aviv.
Isra’ila tana fuskantar babban kalubale wanda bayan dawo da dukkan mutanen ta da aka kama, shi ne batun lalata dukkan ramukan hamas dake yankin Gaza kai tsaye ta hanyar sojoji kuma ta hanyar tsarin kasa da kasa da za’a kafa karkashin umarnin da kulawar Amurka,
Wannan yana zuwa ne kwana daya kafin kulla yarjejeniyar dakatar da bude wuta tsakanin hamas da Isra’ila, da shiga tsakanin kasashen Qatar Masar da kuma kasar Amurka domin kawo karshen dogon yakin daka kwashen shekaru biyu ana yi a Gaza.
Ko a jiya ma sojojin isra’ila sun kashe falasdinawa guda 9 a daidai lokacin da sojojin ke gargadin falasdinawa da su guji zama a yan kunan da har yanzu suna cikin mamaya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Trump Ya Fadawa Hamas Su Mika Makamansu Ko Kuma A Kwace Su Da Karfi October 15, 2025 Iran Ta Samarda Sabbin Hanyoyi Na Fuskantar Barazanar Makiya October 15, 2025 Hamas Ta Ce HKI Tana Cikas Neman Gawawwakin Yahudawa A Gaza October 15, 2025 Yansandan Italiya Sun Kara Da Masu Goyon Bayan Falasdinawa A Garin Udine October 15, 2025 Iran Ta Yi Allah Wadai Da Kalaman Kin Jinin Iran Da Trump Ya Yi A Majalisar Dokokin Isra’ila October 15, 2025 A Lokacin Yaki, Iran Ta Tarwatsa Wata Cibiyar Leken Asirin Yahudawan Sahayoniyya Da Ke Yankin Farar Hula October 15, 2025 Shugaban Kasar Columbia Ya Yi Dirar Mikiya Kan Donald Trump Kan Bai Wa Isra’ila Makamai October 15, 2025 Kungiyar Jihadul-Islami Ta Falasdinu Ta Ce; ‘Yantar Da Fursunonin Falasdinawa Abu Ne Mai Muhaimmanci October 15, 2025 Majalisar Dinkin Duniya Ta Bayyana Cewa: Sake Gina Gaza Zai Ci Dala Biliyan 70 October 15, 2025 Araghchi : Trump bai cancanci mai samar da zaman lafiya ba October 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ma’aikatar Harkokin wajen Kasar Iran Ta Yi Tir Da Jawabin Trump A Knesset Ta HKI
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi tir da maganganun shugaban kasar Amurka Donal Trump a cikin majalisar dokokin HKI a jiya Litinin inda ya bayyana cewa HKI ta sami nasara a yakin da ta kaiwa JMI a cikin watan Yunin da ya gabata, sannan daga karshe ya ce akwai bukatar a cimma yarjeniya da JMI kan shirinta na makamashin Nukliya.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ma’aikatar na cewa jawabin Trump a majalisar Knesset jawabi ne wanda bai da wani kima. Musamman a lokacinda yake gabatar da ita a gababan yan ta’adda makasa.
Ma’aikatar ta tunatarwa Trump har yanzun tana jirin randa za’a gabatar da shi a gaban kuliya kan kissahn Janar shahida Qasim Sulaimani, wanda shi gwarzon yaki da kungiyoyin yan ta’adda a Iraqi da Siriya. Shi ya jagoranci kawo karshen mamayar da kungiyoyin Daesh suka yiwa kasashen biyu a shekara 2017.
Ma’aikatar da bayyana Amurka a matsayin kasa wacce ta fi ko wace kasa a duniya goyawa yan ta’adda a yankin Asiya da kudu da kuma wasu wurare, sannan tana amfani da kujerar Veto a kwamitin tsaro na MDD don kare yan ta’adda da kuma hanasu gurfana a gaban kuliya don fuskantar adalci.
Ma’aikatar ta yi watsi da maganar Trump kan cewa shirin Iran na makamashin Nukliya ba ta zaman lafiya bane, ta kuma kara da cewa Trunp bai da wata shaida da take tabbatar da hakan, sannan ta kara da cewa, wannan zargin bai yadda zata halatta kaiwa JMI yaki ba.
Daga karshen ma’aikatar ta tabbatar da cewa kwarar makaman Amurka da na kasashen yamma zuwa HKI shi ne yake jawo rashin zaman lafiya a yankin. Kuma matukar HKI tana nan babu kuma zaman lafiya a yankin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka An Gudanar Gagarumar Zanga Zangar Goyon Bayan Falasdinawa A Australia Da Indonasia October 14, 2025 Syria: Busaina Sha’aban Ta Karyata Labaran Da Aka Danganta Ma Ta Na Ganawa Da Jami’an Iraniyawa October 14, 2025 Mahalarta Taron ‘Sherm-Sheikh” Sun Rattaba Hannu Akan Yarjejeniyar Zaman Lafiya October 14, 2025 MDD: Mutane 300,000 Su Ka Gudu Daga Sudan Ta Kudu A 2025 October 14, 2025 Iran Ta Gabatar Da Shawarar Kulla Yarjejeniyar Tausayawa A Tsakanin Matan Duniya October 14, 2025 Larijani: Gagarumar Tarbar Da Aka Yi Wa Fursunonin Falasdinawa Ta Nuna Hakikanin Wanda Ya Sami Nasara October 14, 2025 Hamas Ta Mika Yahudawa 7 Daga Cikin 20 Da ke Hannunta Ga Kungiyar Red Cross October 13, 2025 Iran: Kakabawa Kasa Mai Makwabta 16 Takunkumi Ba Abu Ne Mai Sauki Ba. October 13, 2025 An Gano Gawarwaki 323 Karkashin Burabutsai Bayan Dakatar Da Bude Wuta A Gaza October 13, 2025 Tehran Ta yi Gargadi Game Da Barazanar Yaduwar Fadan Iyakar Afghanisatan Da Pakistan. October 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci