Gidauniyar Dangote Ta Kai Tallafin Abinci Ga Wadanda Iftila’in Gobara Ya Ritsa Da Su A Jigawa
Published: 26th, April 2025 GMT
Mazauna Ƙauyen Batakashi da ke ƙaramar hukumar Garki a Jihar Jigawa sun yaba wa Gidauniyar Aliko Dangote bisa tallafin abinci da ta kai musu.
Wasu daga cikin mazaunan da suka tattauna da wakilinmu sun bayyana farin cikinsu kan wannan karamci, tare da fatan alheri ga gidauniyar.
Daya daga cikin waɗanda suka amfana da tallafin, Malam Umar Abdullahi, ya ce gidauniyar ta kawo sassauci ga al’umma bayan iftila’in gobara da ya cinye gidaje kusan 45 a kwanan nan.
Haka shi ma Malam Usman Auwal, ya nuna farin cikinsa, inda ya yaba da gwamnatin jihar Jigawa da kuma Gidauniyar Dangote, bisa tallafinsu ga al’umma.
A jawabinsa yayin kaddamar da rabon tallafin na buhunan shinkafa guda 500 masu nauyin kilogiram10, Shugaban ƙaramar hukumar Garki, Alhaji Adamu Kore, ya gode wa Gidauniyar Aliko Dangote bisa ƙoƙarinta wajen taimakawa al’umma masu rauni a wannan lokaci da suke cikin bukatar.
Ya bayyana cewa wannan tallafi zai rage wa jama’ar ƙauyen Batakashi raɗaɗin halin da suka shiga sakamakon gobarar.
“Muna matuƙar farin ciki da tallafin Dangote da na gwamnatin jihar Jigawa, domin wannan gudummawa ta faranta ran daruruwan iyalai ba kawai a Jigawa ba har da sauran sassan ƙasar nan gaba ɗaya,” in ji Kore.
A nasa jawabin, Mukaddashin Shugaban Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa (SEMA), Alhaji Muhammad Murtala, ya ce Gidauniyar Dangote ta kawo buhunan shinkafa 40,000 masu nauyin kilo 10, domin rabawa talakawa da mabukata.
Maiunguwa, wanda kuma shi ne Daraktan Harkokin Gudanarwa da Kuɗi na hukumar, ya ce a ƙarƙashin gwamnatin Namadi, hukumar ta raba tallafi ga al’ummomi da iftila’i ko matsanancin talauci ya shafa.
Wakilin Gidauniyar Aliko Dangote, Alhaji Mustapha Umar, ya ce gidauniyar tana ba da tallafi ga al’ummomi a faɗin Najeriya domin rage wa marasa ƙarfi raɗaɗi.
Ya ce, “Dangote na shirye koyaushe ya taimaka wa ‘yan Najeriya ta hannun Gidauniyar Aliko Dangote, wadda aka ƙirƙira domin aiwatar da ayyukan jinƙai.”
Radio Nigeria ya ruwaito cewa Gidauniyar ta bayar da buhunan shinkafa 500 masu kilo 10 da tabarma 100 ga al’ummar Batakashi da ke yankin Garki a jihar Jigawa, waɗanda gobara ta shafa.
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa ce ta jagoranci aikin rabon kayan tallafin.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Gidauniyar Dangote Jigawa Gidauniyar Aliko Dangote
এছাড়াও পড়ুন:
DAGA LARABA: “Abba Al-Mustafa Ba Shi Da Hurumin Dakatar Da Fina-finanmu”
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Dangantaka na ƙara rincaɓewa tsakanin masu shirya finafinai Kannywood da Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano, wacce daya daga cikin jaruman fina-finan Kannywood Abba El-Mustapha, ke jagoranta.
A baya-bayan nan, hukumar ta dakatar da fina-finai masu dogon zango guda 22, bayan saɓaninta da wasu masu shirya fina-finai, inda take zargin cewa fina-finansu sun ƙetare iyaka.
Sai dai masu shirya fina-finan sun bayyana cewa sam hukumar ba ta da hurumin dakatar da waɗannan finafinai.
NAJERIYA A YAU: Yadda Za Ku Kula Da Lafiyar Jikinku DAGA LARABA: Tasirin Mulkin Karɓa-Karɓa A NajeriyaShirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan rigimar da ta balle tsakanin hukumar da masu shirya finafinai masu dogon zango.
Domin sauke shirin, latsa nan