Fursunoni 9 Sun Tsere Daga Gidan Gyara Hali A Jihar Kwara, An Cafko Guda Daya
Published: 20th, April 2025 GMT
An samu rahoton cewa, Fursunoni tara a gidan yari na Oko Erin a jihar Kwara a ranar 19 ga watan Afrilu, sun tsere. Majiyoyin leken asiri sun shaida wa Zagazola Makama cewa, da misalin karfe 10:00 na dare, wani ma’aikaci a gidan, mai suna Joseph Issa, ya sanar da faruwar lamarin. Rugujewar Gini A Legas: Adadin wadanda Suka Mutu Ya Kai Biyar, An Ceto 20 Wang Yi Ya Yi Bayani Kan Ziyarar Shugaba Xi Jinping A Vietnam Da Malaysia Da Cambodia Ba tare da bata lokaci ba, ‘yansanda suka yi gaggawar isa wurin, inda suka sake kama daya daga cikin wadanda suka tsere, mai suna Abdul Raman Misa mai shekaru 15.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno
Sojojin Najeriya sun kashe aƙalla mayakan ƙungiyar ISWAP 8, ciki har da manyan kwamandojinta biyu a Jihar Borno.
Wata majiyar leƙen asiri daga rundunar haɗin kai ta OPHK ta bayyana cewa an kashe ’yan ta’addan ne a wata arangama da suka yi da sojojin a kan hanyar Maiduguri zuwa Baga a safiyar ranar Litinin.
DSS ta maka Sowore da Facebook a Kotu kan cin zarafin Tinubu Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabalaA cewar majiyoyin, an yi arangamar ce a kusa da Garin Giwa da ke gab da ƙauyen Kauwa, lokacin da ’yan ta’addan suka yi wa dakarun da ke sintiri kwanton ɓauna.
“A yayin wannan artabu, an kashe ’yan ta’adda takwas, ciki har da Munzirs biyu (kwamandojin filin daga na ƙungiyar) da kuma Qaid ɗaya (shugaban sashe).
“An kashe Modu Dogo, Munzir daga Dogon Chukun, wani Munzir da ba a bayyana ba, da Abu Aisha, shugaban sashe (Qaid) daga Tumbun Mota,” in ji wata majiya.
Majiyar ta ƙara da cewa wasu mayaƙa da dama sun samu raunuka, musamman waɗanda suka tsere da ƙafa bayan sun yi watsi da babura 14 da sojojin suka ƙwato.