Martanin Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Kan Ta’addancin ‘Yan Sahayoniyya ya Shiga Rana Ta Biyu
Published: 15th, June 2025 GMT
Martanin Iran game da ta’addancin haramtacciyar kasar Isra’ila na ci gaba a rana ta biyu
Ana ci gaba da mayar da martani mai girma na Iran game da harin da haramtacciyar kasar Isra’ila take kaiwa da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka ciki.
‘Yan mintoci da suka gabata a zaman wani bangare na biyu na “Alkawarin Gaskiya Na 3”, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta harba daruruwan makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka kan haramtacciyar kasar Isra’ila.
An harba wadannan makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka ciki da kuma jiragen sama masu saukar ungulu daga Tehran da sauran garuruwan kasar Iran a matsayin wani mataki na murkushe laifuffukan da yahudawan sahayoniyya suka aikata a kan yankunan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kuma a zaman wani bangare na biyu na “Alkawarin Gaskiya na 3”.
Kafofin yada labaran yahudawan sahayoniyya sun watsa rahoton tashin gobara da hayaki a birnin Haifa da ke arewacin Falasdinu da aka mamaye.
An ga wuta da hayaki na tashi bayan da makamai masu linzami na Iran sun afkawa matatar mai ta Haifa da ke arewacin Falasdinu da aka mamaye. Sannan a cewar bayanan farko, an kashe fiye da mutane 10 a Haifa.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: jiragen sama
এছাড়াও পড়ুন:
Pezeshkiya: Iran A Shirye Take Don Mu’amala Amma Bazata Bar Hakkinta Ba
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa Iran a shirye take ta fadada hulda da kasashen turai, amma kuma wannan ba zai sa ta saryar da hakkinta na sarrafa makamashin nukliya karshen dokokin kasa da kasa wadanda suka amince mata ta yi haka ba.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a yau Litinin a lokacinda yake ganaw da sabon jakadan kasar Faransa a Tehran pierre Cochard wanda ya mika masa tarkardun fara aikinbsa.
Shugaban ya kara da cewa an takurawa kasar Iran dangane da shirinta na makamashin nukliya a bayan. Amma daga yanzun kuma ba zata amince da irin takurawa ta bay aba.
Ya kuma bayyana cewa tattaunawa tsakanin Iran da kasashe uku na turai wato Faransa da Jamus da kuma Burtaniya, saboda samun fahintar juna da kuma daukewa kasar takunkuman tattalin arzikinn da turawan suka dora mata.