Mai Ba Da Shawara Ga Jagora Ya Bayyana Cikakken Ikon Tawagar Masu Tattaunawan Iran A Zaman Shawarwari Da Amurka
Published: 20th, April 2025 GMT
Mai ba da shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Masu sasantawa Iran a birnin Roma suna da cikakken ikon gabatar da shawara kan matsayin kasarsu
Ali Shamkhani mai ba da shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi nuni da cewa: Masu gudanar da shawarwari na Iran sun tafi birnin Roma ne domin yin shawarwari karo na biyu da Amurka kan batun makamashin nukiliyar kasar Iran.
Shamkhani ya yi nuni da cewa: Masu shiga tsakani na Iran suna neman cimma cikakkiyar yarjejeniya bisa ka’idoji guda tara: tsanani, samar da lamuni, dage takunkumi, yin watsi da tsarin Libya/UAE, kaucewa barazana, gaggauta yin shawarwari, dakile masu shirga karya kan Shirin makaman nukiliyar Iran -irin haramtacciyar kasar Isra’ila- da saukaka zuba jari. Iran ta zo ne domin cimma daidaiton yarjejeniya, ba ta mika wuya ga bakaken manufofin Amurka ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Takht Ravanji: Iran Ba Za Ta Taba Yin Tattaunawa Akan Dakatar Da Tace Sanadarin Uranium Ba
Mataimakin ministan harkokin waje mai kula da bangaren siyasa, ya bayyana cewa; Ko kadan ba a bijiro da batun dakatar da tace sanadarin uranium a Iran ba, ko kuma batun makamanta masu linzami.
Mataimakin ministan harkokin wajen na Iran ya tabbatar da cewa, wadannan abubuwan biyu wato dakatar da ci gaba da tace sanadarin uranium da kuma makamai masu linzami, jan layi ne da jamhuriyar musulunci ta Iran ba za ta bari a ketara su ba ba kuma za ta bari a bude tattaunawa akansu ba.
Kwamitin da yake kula da tsaron kasa da kuma siyasar waje a majalisar shawarar musulunci ta Iran a karkashin jagorancin dan majalisar Ibrahim Ridhazi ya yi taro a ranar Lahadin da ta gabata, inda aka gayyaci mataimakin ministan harkokin wajen domin jin ta bakinsa akan abubuwan da suke faruwa a tattaunawar da ake yi ba kai tsaye ba da Amurka.
Ridha’i ya fada wa ‘yan jarida cewa Takht Ravanji ya kammadar da rahoto akan yadda tattaunawar take gudana a tsakanin Amurka da Iran da kasar Oman take shiga Tsakani.
Haka nan kuma ya ce; Tace sanadarin Uranium a cikin gida wani jan layi ne da ba za a tsallake shi ba.