Leadership News Hausa:
2025-05-01@04:36:19 GMT

Muhimman Abubuwan Da Ya Kamata A Sani A Kan Kiwon Kifi

Published: 1st, March 2025 GMT

Muhimman Abubuwan Da Ya Kamata A Sani A Kan Kiwon Kifi

Bayanai Hudu Da Ya Kamata A Sani Dangane Da Kiwon Kifi A Nijeriya:

1- Kimanin Kashi 40 Kacal Ake Iya Cimma Bukatar Samar Da Shi A Nijeriya:

A cewar wata kididdiga ta Bankin Duniya, Nijeriya a 2018, ta samar da yawan Kifin da ya kai kimanin 1,169,478, wanda ya kai kimanin kashi 40 cikin 100, wanda bukatarsa da ake da ita a Nijeriya a shekara daya, ta kai kimanin tan miliyan 3.

4, inda sauran wanda ake bukatar fitarwa waje ya kai kashi 60 cikin 100.

2- Kamun Tarwada A Nijeriya Fitacciyar Sana’a Ce:

Samar da Tarwada a Nijeriya, ya karu daga tan miliyan 21,700 a 1999 zuwa tan miliyan 316,700 a 2015, wanda ya karu da sama da kashi 1,400 a cikin shekaru 25 da suka wuce.

Shugaban kungiyar masu kamun Tarwada na kasa (CAFAN), Cif Tayo Akingbolagun a cikin sanarwar da ya fitar a taron shekara na kungiyar ya bayyana cewa, Nijeriya a 2016 ta samar da sama da tan 370,000 na Tarwada.

3- Nijeriya Ce Ta Uku Kan Gaba A Afirka Wajen Kamun Kifi:

Wani rahoto na 2018 da Bankin Duniya ya fitar ya nuna cewa, jimillar Kifin da aka samar a duniya ya nuna cewa, a yanzu Nijeriya ce ta uku da ke kan gaba a Afirka wajen samar da Kifi, inda ta samar da kimanin tan 1,169,478.

4- Kiwon Kifi Na Bunkasa Tattalin Arzikin Nijeriya Da Kashi 3.24:

A cewar wasu bayanai da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta fitar a zango na daya na 2021, fannin Kiwon Kifi ya bayar da gudunmawa ga tattalin arzikin Nijeriya da kimanin kashi 3.24.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Bai Dace A Mika Wuya Ga Wanda Ya Nuna Fin Karfi Da Matakan Haraji Ba

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Amurka ta sake laftawa wasu kamfaninin mai na Iran takunkumi
  • NEMA Ta Karɓi ‘Yan Nijeriya 203 Da Suka Maƙale A Libya
  • Cinikayyar Hidima Ta Kasar Sin Ta Matukar Bunkasa A Rubu’in Farko Na Nana
  • Abubuwan Da Na Gani A Yankin ‘Hero Bay’ Da Ke Cikin Kasar China
  • Mutanen da talauci ya yi wa katutu zai ƙaru a Nijeriya — Bankin Duniya
  • Sin Za Ta Aiwatar Da Matakan Daidaita Samar Da Guraben Ayyukan Yi Da Raya Tattalin Arziki
  • Bai Dace A Mika Wuya Ga Wanda Ya Nuna Fin Karfi Da Matakan Haraji Ba
  • Shekara 10 ina sayar da sassan jikin ɗan Adam — Wanda ake zargi
  • Ma’aikata 240 na karɓar albashi biyu, wasu 217 na amfani da lambar BVN ɗaya a Kano
  • Iran Da Rasha Sun Jaddada Yin Aiki Tare A Fagen Kiwon Lafiya