Dalilin da muka soke tattaunawar nukiliya da Amurka — Iran
Published: 15th, June 2025 GMT
Iran ta sanar da soke zaman tattaunawa da ya kamata ta yi da Amurka kan batun nikiliyarta a Oman yau Lahadi saka makon hare-haren da Isra’ila ta kai mata a ranar Juma’a.
Bayanai sun ce a wannan Lahadin ce ya kamata a gudanar da ganawa ta shida tsakanin wakilan Amurka da na Iran a birnin Musqat na Oman.
Sai dai kakakin Ministan harkokin wajen Iran, Esmaeil Baqaei ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, Amurka ta nuna fuska biyu, inda a gefe guda take tattaunawar cimma masalahar jingine ƙera nukiliya da Iran, amma a ɗaya gefen kuma ta goyi bayan harin da Isra’ila ta kai mata.
Iran ta zargi Amurka da goyon bayan harin da Isra’ila ta kai mata, sannan kuma ta ce tattaunawar yarjejeniyar dakatar da ƙera makamin ƙare dangi na nukiliya da take yi da Amurkar ba ta da wani amfani.
A nasa ɓangaren, Ministan harakokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya ce babu buƙatar ci gaba da tattaunawa da aka faro tsakiyar watan Afirilun wannan shekara lura da harin dabbanci da Isra’ila ta kai mata.
Kafofin yaɗa labarai da dama a Iran sun shaida cewa guda daga cikin masu baiwa jagoran addinin musluncin Iran ayatoAllah Ali Khamenei kuma mai taka muhimmiyar rawa a tattaunawar, Ali Shamkhani, na daga cikin waɗanda su ka ji rauni a hare-haren na Isra’ila.
Tun farko Isra’ila ce ta fara kai wa Iran hari kan cibiyoyin nukiliyarta tare da halaka manyan hafsoshin tsaronta, cikin daren Alhamis zuwa wayewar garin Juma’a, kuma ta ci gaba da kai farmaki da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa, mafarin buɗe kofar wani sabon rikici a tsakanin ƙasashen biyu da suka jima suna adawa da juna tsawon shekaru.
Harin ramuwar gayya da Iran ta kai wa Isra’ila da safiyar Asabar ya halaka mutane uku, tare da jikkata wasu da dama a biranen Jerusalem da Tel Aviv, inda hukumomin Isra’ila ke ci gaba da gargaɗin ‘yan kasar su nemi mafaka.
A wani jawabi da jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya gabatarwa al’ummar kasar ranar Juma’a, ya ce ba za su saurara wa Isra’ila ba sakamakon munin abin da ta aikata musu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Iran Isra ila nukiliya da Isra ila ta kai mata
এছাড়াও পড়ুন:
Nijar da Rasha sun ƙulla yarjejeniyar makamashin nukiliya
Jamhuriyar Nijar da ƙasar Rasha a ranar Litinin, 28 ga watan Yulin 2025 sun ƙulla yarjejeniya game da makamashin nukiliya da kuma haƙar yuraniyom.
Kamfanin dillancin labaran Nijar (ANP) ya ruwaito cewa ƙasashen biyu sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar ce bayan ganawar shugaban Nijar, Janar Abdourahamane Tiani, da wata babbar tawagar Rasha ƙarƙashin jagorancin Ministan Makamashi, Mista Sergei Tsivilev.
Ambaliya ta yi ajalin mutum 30 a China Jami’ar Jihar Gombe za ta fara sabbin darussa 6 a fannin noma“Muhimmiyar manufarmu ita ce mu ƙara inganta rayuwar mutanen Nijar da na Rasha,” in ji Sergei, kana ya bayyana cewa sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya game da makamashin nukiliya da haƙar yuraniyom.
“Mun amince cewa za mu horar da manyan jami’ai waɗanda za su iya aiki a fannonin tallafinmu irin na makamashi da noma da lafiya da ilimi, kuma za mu horar da injiniyoyi tun a makarantu domin su ci gaba da karatunsu a jami’o’in da ke Tarayyar Rasha,” in ji shi.
Ganawar ta mayar da hankali ne kan dangantaka tsakanin Tarayyar Rasha da Nijar, in ji rahoton na ANP.
Bayan ganawar dai Ministan na Rasha ya bayyana godiyarsa ga shugaba da mutanen Nijar domin irin tarbar da aka yi masa.
“Mun ga bayanai da dama game da damarmakin da ke akwai a cikin Nijar, kuma a halin yanzu mutanenmu na ƙoƙarin aiki kan damarmakin da ke nan a Nijar,” in ji Mista Sergei Tsivilev, wanda shi ne shugaban ɓangaren Rasha a hukumar haɗakar gwamnatoci da ƙasashen AES.
“Shugaban ƙasar ya kuma sanar da mu cewa shi zai zaɓi shugaba na ɓangare ɗaya na hukumar haɗakar gwamnatocin nan ba da jimawa ba domin ayyukanmu da ‘yan uwanmu na Nijar su yi ta tafiya babu tangarɗa,” in ji shi.