2025-10-28@06:24:10 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1049
«yankunan Falasdinawa»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da aikin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana a Kasuwar Dutse Ultra-Modern Market, inda ya cika alkawarin gwamnatinsa na samar da tsaftataccen makamashi ga ‘yan kasuwa a jihar Jigawa. Aikin wanda Hukumar Samar da Tattalin Arzikin Kasa da Samar da ayyukan yi ta Jihar Jigawa ta gudanar, ya hada shaguna 300 da wutar lantarki daga na’urorin hasken rana da aka sanya a cikin kasuwar, inda kowane shago kuma an saka masa fanka amfani da hasken rana kyauta. Da yake jawabi a wajen bikin kaddamar da kasuwar a hukumance, Malam Umar Namadi ya ce shirin zai saukaka harkokin kasuwanci, da rage kashe kudi, da kuma bunkasa ribar ‘yan kasuwa. ...
Kasashen duniya sun fara yabawa kungiyar Hamas kan amincewa da shirin zaman lafiya na Trump. Qatar mai shiga tsakanin Isra’ila da Hamas a yakin Gaza ta yaba da matakin da kungiyar ta dauka. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Qatar Maged al-Ansari, wanda kuma ya goyi bayan kiran da Donald Trump ya yi na tsagaita bude wuta ya ce ” Qatar na maraba da sanarwar da Hamas ta yi cewa ta amince da shirin na Shugaba Trump.” A nata bangare Masar tana kallon wannan a matsayin “ci gaba mai kyau.” Kuma tana fatan a sakamakon haka, bangarorin biyu “za su himmatu wajen aiwatar da shirin Shugaba Trump da kuma kawo karshen yakin,” in ji ma’aikatar harkokin wajen kasar a shafin Facebook. Ita...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Fira ministan kasar malesiya Anwar Ibrahim da na Pakistan shehbaz sharif suna tir da matakin da HKI ta dauka kan jiragen tawagar Sumud Flotilla ajiya Alhamisi a shafukansu na X , bayan da jagororin tawagar suka sanar da cewa sojojin HKI sun kama jiragen ruwa guda 14 dake dauke da yan kasashen waje da kayayyakin agaji zuwa yankin Gaza. Haka zalika shugaban kasar Bolivia da takwaransa na kasar Cuba suna yi Allah wadai da Isra’ila , haka su ma ministocin harkokin wajen spaniya jose manueal dana kasar irish simon harris sun bayyana damuwarsu matuka game da halin da tawagar ta flotilla ke ciki a hannun Israi’la na kokarin hana su isa yankin gaza. Ita dai tawagar Sumud Flotilla tana dauke...
Sule ya bayyana cewa, “ilimi shi ne abu mafi mahimmanci da gwamnatinsa ta fi mayar da hankali akai, hakan ne ya sa aka ware kashi 36 cikin 100 na kasafin kuɗin jihar na shekarar 2025 ga sashen ilimi”. Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta dawo da tallafin karatu na ƙasashen waje, inda a halin yanzu take ɗaukar nauyin ɗalibai 155 da ke karatu a fannoni daban-daban a ƙasashe daban-daban na duniya. Ya ƙara bayyana cewa, gwamnatin jihar na ɗaukar nauyin ɗaliban jinya da kuma wasu a jami’o’i daban-daban a faɗin ƙasar. “Mun kuma biya kuɗin rajistar jarabawar kammala sakandire ta kasa (NECO) ta shekarar 2025 ga ɗalibai sama da 24,000 na makarantun sakandare na gwamnati, domin...
Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa, ya taya gwamnati da al’ummar Nijeriya murnar cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai, inda ya bayyana ranar a matsayin abin tunawa da hadin kai, juriya, sadaukarwa da suka gina kasar. A sakonsa na fatan alheri, Gwamna Namadi ya ce bikin ba wai kawai lokacin yin tunani ne kan irin gwagwarmayar da iyayen da suka kafa kasar suka yi ba, har ma wata dama ce ta sabunta sadaukarwar hadin gwiwa don samar da zaman lafiya, ci gaba, da wadata. “A yau, muna bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai cikin alfahari da godiya. Wannan ranar tana tunatar da mu sadaukarwar da jaruman mu suka yi a baya, wadanda hangen nesa...
Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya ya jaddada ƙudirinsa na yin aiki tare da Gidauniyar Malala a ƙoƙarinta na ci gaba da bunƙasa ilimi da magance ƙalubalen da ke hana miliyoyin yara, musamman ’yan mata rashin zuwa makaranta. Da yake yi wa Malala Yousafzai maraba a ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya, Babban jami’in kula da ayyukan jin ƙai a ofishin Mohammed Malick Fall, ya ce Majalisar Ɗinkin Duniya zata yi aiki tare da gidauniyar Malala, wacce ta samu kyautar lambar yabo ta Nobel. PENGASSAN ta dakatar da yajin aiki, ta gargaɗi mat An yi garkuwa da tsohon Shugaban SUBEB na Jihar Neja “Majalisar Ɗinkin Duniya ta sake jaddada goyon bayanta ga asusun Malala wajen ganin ‘ya’ya mata da yawa suna samun...
Kwamitin Shura na Jihar Kano, ya ta dakatar da Malam Lawan Shuaibu Triumph daga yin wa’azi har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan zarginsa da yin ɓatanci ga Annabi Muhammad (S.A.W). Sakataren kwamitin, Alhaji Shehu Wada Sagagi ne, ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a yau Laraba. PENGASSAN ta dakatar da yajin aiki, ta gargaɗi matatar Dangote Jihar Gombe ta fara aiwatar da dokar hana kiwo da daddare “Yau mun sake yin zama domin karɓa da kuma nazarin zarge-zargen da ake yi wa Sheikh Lawal Shuaib Abubakar, wanda aka fi sani da Triumph. Mun saurari sauti da kuma kallon bidiyon da aka turo. “A cikin tattaunawarmu, mun yi bincike mai zurfi. Mun yanke cewa...
Kwamitin Shura na Jihar Kano, ya ta dakatar da Malam Lawan Shuaibu Triumph daga yin wa’azi har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan zarginsa da yin ɓatanci ga Annabi Muhammad (S.A.W). Sakataren kwamitin, Alhaji Shehu Wada Sagagi ne, ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a yau Laraba. PENGASSAN ta dakatar da yajin aiki, ta gargaɗi matatar Dangote Jihar Gombe ta fara aiwatar da dokar hana kiwo da daddare “Yau mun sake yin zama domin karɓa da kuma nazarin zarge-zargen da ake yi wa Sheikh Lawal Shuaib Abubakar, wanda aka fi sani da Triumph. Mun saurari sauti da kuma kallon bidiyon da aka turo. “A cikin tattaunawarmu, mun yi bincike mai zurfi. Mun yanke cewa...
Kwamitin Shura na Jihar Kano, ya ta dakatar da Malam Lawan Shuaibu Triumph daga y’in wa’azi har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan zarginsa da yin ɓatanci ga Annabi Muhammad (S.A.W). Sakataren kwamitin, Alhaji Shehu Wada Sagagi ne, ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a yau Laraba. PENGASSAN ta dakatar da yajin aiki, ta gargaɗi matatar Dangote Jihar Gombe ta fara aiwatar da dokar hana kiwo da daddare “Yau mun sake yin zama domin karɓa da kuma nazarin zarge-zargen da ake yi wa Sheikh Lawal Shuaib Abubakar, wanda aka fi sani da Triumph. Mun saurari sauti da kuma kallon bidiyon da aka turo. “A cikin tattaunawarmu, mun yi bincike mai zurfi. Mun yanke cewa...
Xi Jinping da sauran shugabannin sun yi tattaki zuwa gaban ginin, inda ya gyara furannin dake cikin kwandunan. Sannan ya zagaya ginin a wani mataki na nuna girmamawa. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ali Larijani, sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran, wanda ya ziyarci kasar Lebanon domin halartar bikin zagayowar shahadar Sayyid Hassan Nasrallah, ya gana da babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem. Babban labarin jaridar Pars Today na cewa, Ali Larijani, sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya gana da babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qasem a ranar Lahadin da ta gabata. A wajen taron, Larijani ya jaddada goyon bayan Iran ga kasar Labanon da tsayin daka, inda ya yi misali da umarnin Imam Khumaini da Ayatullah Khamenei Jagoran juyin juya halin Musulunci tare da goyon bayan gwamnati da al’ummar Iran. Ya jaddada cewa Iran a shirye take ta ba da tallafi ga Lebanon da juriya “a kowane...
Shugabannin ƙungiyar manyan ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya (PENGASSAN) da wakilan Matatar Dangote na halartar wani taron gaggawa tare da wakilan Gwamnatin Tarayya. Shugaban ƙungiyar PENGASSAN, Festus Osifo, tare da Babban Sakataren Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (TUC), Nuhu Toro, ne ke jagorantar ɓangaren ƙungiyoyin ƙwadago, yayin da Ministan Ƙwadago da Ayyuka, Maigari Dingyadi da wasu jami’ai ke wakiltar Gwamnatin Tarayya. Ya zama tilas ɗalibai su gabatar da ‘Project’ kafin rajistar NYSC — Tinubu Gwamnatin Tarayya ta ayyana hutu ranar Laraba Aminiya ta ruwaito cewa tun a ranar Lahadin da ta gabata ce Gwamnatin Tarayya ta gayyaci shugabannin PENGASSAN da na ɓangaren Matatar Dangote zuwa wannan taro sakamakon rikicin da ke tsakanin ɓangarorin biyu. Sai dai, duk da...
Bana shekara ce ta cika shekaru 80 da samun nasarar yakin da al’ummar Sin suka yi da mamayar dakarun kasar Japan, da yakin duniya na kin tafarkin murdiya. Ranar 30 ga watan Satumba ita ce ranar tunawa da jarumai ta kasar. A safiyar ranar, shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran shugabannin JKS da na kasar, tare da wakilai daga sassa daban-daban, za su ajiye furanni don jinjinawa jarumai da suka sadaukar da rayukansu saboda kasa a filin Tian’anmen. A lokacin, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG zai watsa wannan biki kai tsaye.(Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
Majalisar Dinkin Duniya ta sake sanyawa Iran takunkumin rashin adalci a hukumance A hukumance Majalisar Dinkin Duniya ta sake kakabawa Iran takunkumi mai tsauri kan shirinta na makamashin nukiliya da take gudanarwa ta hanyar lumana, ta hanyar amfani da tsarin da aka fi sani da “Snapback”. Matakin na Majalisar Dinkin Duniya ya samo asali ne daga zargin karya da ake yi wa Iran na karya yarjejeniyar makamashin nukiliyar da aka kulla a shekarar 2015 da Amurka, da Birtaniya, da Rasha, da Faransa, da China da kuma Jamus. Wannan shawarar dai ta zo ne duk da irin jajircewar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi kan yarjejeniyar, da ficewar Amurka daga cikinta a shekara ta 2018, da kuma kasashen Turai uku,...
Kasashe 77 Ne Na Duniya Suka Fice A Lokacin Jawabin Fira Ministan Isra’ila A Taron Majalisar Dinkin Duniya
Kasashen duniya 77 ne suka kauracewa jawabin fira ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a Majalisar Dinkin Duniya Wani bincike da Isra’ila ta gudanar ya nuna cewa kasashe 77 ne suka fice daga zauren Majalisar Dinkin Duniya a lokacin da fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benyamin Netanyahu ke jawabi ga babban zauren Majalisar a birnin New York. Jaridar Yedioth Ahronoth ta Isra’ila ta ruwaito cewa: Bayan duba kasashen da suka kaurace wa jawabin, an gano cewa: “dukkan makwaftan Isra’ila hudu, baya ga Saudiyya” na daga cikin mutane 77 da suka kauracewa taron, lamarin da ya sa Netanyahu ya yi magana a wani zauren da ke kusa da babu kowa. Sabanin haka jaridar yahudawa ta yabi wakilan Bahrain da Hadaddiyar Daular Larabawa da...
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bar birnin New York na Amurka, bayan kammala wakiltar Shugaba Bola Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 (UNGA). Ya nufi Jamus domin ganawa da jami’an Bankin Deutsche kan batutuwan haɗin gwuiwa da zuba jari a shirye-shiryen ci gaban Nijeriya. A yayin taron UNGA, Shettima ya samu yabo daga Sakatare-Janar na MDD, António Guterres, bisa ƙoƙarin Nijeriya na neman kujerar dindindin a Kwamitin Tsaro. Haka kuma ya gabatar da damar zuba jari a fannin makamashin mai darajar dala biliyan 200, tare da ƙarfafa haɗin gwuiwa da Birtaniya kan harkokin kasuwanci da tsaro da kuma ƙaura (ci rani). Gwamna Yusuf Ya Aike Da Sunayen Kwamishinoni Zuwa Majalisar Dokokin Jihar Kano UNGA: Tinubu Ya...
Kamaru Kasar Kamaru tana da alaka sosai da Isra’ila. Daraktan fannin tsaro na Cibiyar Nazarin Tsaron Kasashen Afirka da tsare-tsare a Geneba, Dabid Otto ya ce Isra’ila na kallon Kamaru a matsayin daya daga cikin kawayenta na kusa a Afirka. Ya ce “Kamaru ba za ta yi gangancin lalata alakar diflomasiyya da ke tsakaninta da Isra’ila ba.” Ya ce alakarsu na da kwari sosai, kuma ya shafi batu ne na tsaro. “Isra’ila ta taimaka sosai kuma tana ci gaba da taimakawa wajen kare gwamnatin Kamaru,” in ji shi. Isra’ila ta bayar da horo, kuma ana da amannar cewa tana ci gaba da bai wa dakaru na musamman na Kamaru horo, wani abu da ke tabbatar da tsaron shugaban kasar....
Ko za ka fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinka? An haife ni a unguwar Tudun Nufawa dake Kano Municipal, na yi karatun firamare a jakara ‘Special Pramary School’, na yi sakandare a Gwammmaja 2. Sannan babban Sakandare a ‘GSS Dala’. Na yi karatun ‘Diploma’ a fannin ‘computer’, sannan na yi ‘National Diploma’ akan lafiyar hakori ‘Dental Surgery Technician’. Ya batun iyali, shin akwai ko babu? Ina da Aure, mata ta daya da ‘ya’ya biyar biyu maza uku mata. Wane rawa ka ke takawa a cikin masana’antar Kannywood? Na farko zan iya cewa ni ‘film maker’ ne, amma nafi karfi a ‘directing’. Sannan ina ‘Camera’ ina rubutu, Ina ‘acting’, Ina ‘Editing’. Me ya ja hankalinka har ka tsunduma...
Tawagar Gwamnatin Tsakiya Na Ci Gaba Da Ziyartar Jami’ai Da Mazauna Yankuna Da Dama Na Jihar Xinjiang
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Da dama daga cikin tawagogin da suke halartar taron babban zauren MDD na shekara-shekara sun fice a yayin da Fira ministan HKI ya fara jawabi, domin nuna kin amincewa da kisan kiyashin yankin Gaza. A jawabin nasa wanda tsirarun mutane su ka saurare shi, ya soki kasashen Faransa, Birtaniya, Australia da Canada da su ka bayyana amincewarsu da kasar Falasdinu. Wani kwamiti da MDD ta kafa na bincike akan abinda yake faruwa a Gaza, ya tabbatar da cewa sojojin Isra’ila” suna aikata laifukan yaki cikin ganganci. HKI tana kara yin bakin jini a tsakanin kasashen duniya saboda yakin Gaza da kuma yadda ta ke take dokokin kasa da kasa. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A yayin da shugabanni da wakilan gwamnatocin kasashe ke ci gaba da jawabi a babban zauren MDD, firaministan Isra’ila shi ma ya gabatar da nasa jawabi da yammacin yau, saidai ya ci karo da ihu da kuma ficewa daga zauren daga wasu wakilan kasashe dake zamne a zauren. Jakadun kasashen Musulmi, Larabawa, Afrika da Latin Amurka ne suka ficewa, sannan wasu daga Turai suka bi su. Amurka ce da wasu kawayenta daga yankin Pacific, da wasu kasashen kalilan ne suka rage a zauren. An kuma rawaito yin zanga zanga a birnin New York ta goyan bayan falasdinu da kuma neman kawo karshen yakin Gaza. Netanyahu ya kwashe sama da mintina 45 yana jawabi inda ya tabo batutuwa da dama, a...
Reform ya kuma ce yana shirin hana wani wanda ba dan Biritaniya ba damar samun walwala. Jam’iyyar ta yi ikirarin cewa shirin nasu zai yi tanadin fam biliyan 234 cikin shekaru da dama. Chancella Rachel Reebes ta ce tanadin da aka ba da shawarar “ba shi da tushe a zahiri” kuma tuni gwamnati ta fara duban hana walwalar bakin haure. Jagoran kawo sauyi a Burtaniya, Nigel Farage, ya ce bai kamata Birtaniya ta zama “bankin abinci na duniya ba”. Da yake kaddamar da sabbin manufofin, Farage ya ce: “Ba a gare mu ba ne mu bane a ce mutane na shigowa daga ko’ina cikin duniya.” A karkashin tsarin na yanzu, bakin haure na iya neman izinin zama na dindindin bayan...
Kwararan bayanai na nuni da cewa tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya fara tattaunawa da Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, kan shirin komawa jam’iyyar. Majiyoyi daga cikin APC a Kano sun bayyana cewa Kwankwaso ya rubuta wasiƙa zuwa sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa a Abuja, yana sanar da aniyarsa ta komawa jam’iyyar. An rufe wurin haƙar zinare a Kebbi Sauya Sheƙa: Kwankwaso ya gindaya sharuɗa kafin sake komawa APC Sai dai Aminiya ba ta iya tabbatar da hakan ba ya zuwa lokacin hada wannan rahoton. Wata majiya daga sakatariyar APC ta ƙasa kuma ta tabbatar da cewa ana ci gaba da tattaunawa tsakanin Kwankwaso da Farfesa Nentawe kan sauya shekar, kuma maganar ta yi nisa...
Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta amince da ƙarin kasafin kuɗi na shekarar 2025 na Naira biliyan 75 na kasafin kuɗin jihar da ƙananan hukumomi. An amince da kasafin kuɗin ya zama doka ne a yayin zaman majalisar wanda mataimakin Shugaban Majalisar Hon. Sani Isiya ya jagoranta. Ana zargin mai shagon kemis da ya yi wa ’yar shekara 14 fyaɗe a Filato An kashe ’ya’yan magoya bayan Gwamna Zulum Matakin ya biyo bayan amincewa da rahoton kwamitin kasafin kuɗi na Majalisar wanda Hon Ibrahim Hamza Adamu ya gabatar. Ƙarin kasafin kuɗin da aka amince da shi ya ƙunshi Naira biliyan 58 na Gwamnatin Jiha da kuma Naira biliyan 17 na Ƙananan Hukumomi 27, wanda ya ƙunshi kashe kuɗaɗe na yau da...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa tattaunawa da kuma diblomasiyya basa da amfani idan har kasashen E3 sun maida takunkuman tattalin arziki a kan kasarsa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a lokacinda yake ganawa da shugaban kasar Swiss Karin Keller-Sutter a gefen taron babban zauren MDD karo na 80. Ya ce mata ‘muna maraba da tattaunawa ko diblomasiyya amma idan kasashe E3 suka maida takunkuman MDD a kan kasar mu tattaunawa da diblomasiyya basu da amfani a wajemmu’. Wadannan kasashen turai 3 ko traiko dai sun tada baton maido da takunkuman tattalin arziki na MDD ne a cikin watan Augustan da ya gabata, bayan sun ga Amurka da HKI sun...
A yayin taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya (UNGA) karo na 80, Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya gabatar da jawabin Najeriya a madadin Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Jawabinsa ya ƙunshi kira ga gyare-gyare, adalci a harkokin tattalin arziki, da goyon bayan zaman lafiya da haɗin kai na duniya. Gwamnatin Tarayya za ta fara farautar masu takardun bogi a wajen aiki UNGA: Yau Shettima zai gabatar da jawabin Najeriya a MDD Ga muhimman batutuwa bakwai da Najeriya ta jaddada a yayin jawabinta a wannan taron: Bai wa Najeriya kujera a Kwamitin Tsaro na majalisar Najeriya ta buƙaci samun kujerar dindindin a Kwamitin Tsaro/Sulhu na majalisar, tana mai cewa rashin wakilcin Afirka a matakin yanke shawara na duniya yana rage...
Shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta kasar Iran Muhamamd Islami ya bayyana cewa nan gaba kadan Iran za ta rika samar da megawatti 5000 na wutar lantarki daga tashar Nukiliya dake Bushehr. Kamfanin dillancin labarun “Mehr’ ya ambato shugaban hukumar makamashin Nukiliyar na Iran yana cewa; Ba da jimawa ba, tashar ta Nukilkiya dake Bushehr za ta zama cikin Shirin da za ta iya bayar da wutar lantarki mai karfin megawatti 5000, tare da cewa, yin hakan yana a karkashin tsarin da ake da shi akan Shirin Nukiliya a Iran. Har ila yau ya kara da cewa; A lokacin ziyarar da mu ka kai zuwa kasar Rasha, mun yi tattaunawa akan aiki tare a fagen fasahar Nukiliya. Bugu da kari ya...
Shugaban gwamnatin riƙon ƙwaryar Syria Ahmed al-Sharaa ya shaida wa babban taron Majalisar Dinkin Duniya cewa ƙasarsa ta sake ƙwato matsayinta a idon duniya. Wannan ne karon farko cikin kusan shekaru 60 da wani shugaban Syria ya yi jawabi a taron MDD. Siyasa ba ta yiwuwa da rowa — Gwamna Buni Za a gudanar da taron kiwon lafiya na farko a Gombe Al-Sharaa ya zama shugaban Siriya na farko da ya yi jawabi a Majalisar Dinkin Duniya tun bayan da Noureddine Attasi ya yi jawabi a shekara ta 1967, jim kaɗan bayan yaƙin Larabawa da Isra’ila, a lokacin da Damashka ta rasa iko da tuddan Golan wanda Isra’ila ta ƙwace a shekarar 1981. Al Sharaa ya ce yaƙin basasa ya...
Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya ce a matsayin Sin na babbar kasa mai tasowa dake sauke nauyin dake wuyanta, ba za ta nemi wani sabon matsayi na musamman, ko fifiko yayin tattaunawar cimma matsaya ta yanzu, da ma ta nan gaba, dangane da harkokin kungiyar cinikayya ta duniya WTO. Li, ya yi wannan tsokaci ne yayin taron manyan jami’ai dangane da shawarar nan ta tsarin shugabanci da Sin ta gabatar, a gefen babban taron MDD karo na 80 dake gudana yanzu haka. A yau Laraba, ma’aikatar cinikayya ta Sin ta kira taron manema labarai, inda mataimakin ministan cinikayya na Sin Li Chenggang, ya bayyana wannan muhimmiyar matsaya ta Sin, a matsayin alkawari dake mayar da hankali ga yanayi da...
An kammala shirin gudanar da taron lafiya karo na farko a tarihin Jihar Gombe, wanda za a fara a ranar 2 ga Oktoba. Da yake zantawa da manema labarai wannan Larabar a Gombe, Kwamishinan Lafiya, Dakta Habu Dahiru, ya bayyana cewa, za a gudanar da taron na tsawon kwanaki biyu domin tattauna matsalolin bangaren lafiya da zummar samo mafita. An sake raba Naira biliyan 5 haƙƙoƙin ’yan fansho a Kano Komawar Natasha majalisa ya nuna haɗin kai zai iya yaƙar rashin adalci — Atiku Ya ce, taron zai samu halartar manyan baki ciki har da Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Remi Tinubu; Mataimakiyar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Hajiya Amina Mohammed; Ministan Lafiya, Farfesa Ali Pate; tare da wasu abokan hulda, ‘yan...
Shugaban Colombia Gustavo Petro ya yi kira da a kafa rundinar soji ta kasa da kasa don ‘yantar da Falasdinu da adawa da ‘yan mulkin kama karya da Amurka da NATO ke yadawa. A jawabin da ya gabatar a zauren MDD, Petro ya bukaci kasashen da ke adawa da kisan kiyashi da su hada karfi da karfe, domin kare rayukan al’ummar Palasdinu. “Muna bukatar sojoji masu karfi da suka kunshi kasashen da ba su amince da kisan kare dangi ba, Dole ne mu ‘yantar da Falasdinu,” in ji shi. Petro ya kuma bayyana damuwarsa kan yadda ayyukan Washington da NATO ke gurgunta mulkin dimokuradiyya da kuma taimakawa wajen sake dawo da mulkin kama-karya a duniya. Kiran da Petro na...
Fitaccen mawakin nan na kudancin Najeriya David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya ba matarsa Chioma kyautar sabuwar motar alfarma kirar Mercedes-Benz G-Wagon ta shekarar 2025. Wannan motar mai tsada, wadda aka kaddamar da ita kwanan nan a kasuwar duniya, tana da farashin sama da $150,000 (kimanin Naira miliyan 240). Yada labaran karya a intanet babban laifi ne a Musulunci – Sheikh Ibrahim Khalil UNGA: Yau Shettima zai gabatar da jawabin Najeriya a MDD Sabuwar motar ta 2025 na dauke da sabon fasali mai ban sha’awa da kuma Zubin da ya sa ta fi tsofaffin nau’ikan da suka gabace ta inganci. A wani bidiyo da Davido ya wallafa a shafinsa na Instagram a ranar Laraba, an ga lokacin...
Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima a ranar Laraba zai gabatar da jawabin Najeriya a taron Babban Zauren Majalisar Dinkin duniya (UNGA) karo na 80 da ke gudana a birnin New York na Amurka. Zai yi jawabin ne a madadin Shugaban Kasa Bola Tinubu tsakanin karfe 3:00 na yamma zuwa 9:00 na dare agogon birnin New York. Mun ci ribar Naira biliyan 601 a watanni shidan farkon 2025 – Bankin GT Dalilin da muke goyon bayan Tinubu kan karɓo bashi — Majalisar Wakilai Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa ana sa ran Najeriya za ta bayyana sabbin kudurorinta na kasa (NDCs) da aka sabunta a karkashin yarjejeniyar Paris yayin wannan jawabi. A baya, Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima,...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya tattauna da fira ministan Norway game da alakar kasashen biyu da ci gaban kasa da kasa Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi wanda ke ziyara a birnin New York domin halartar taron shekara shekara na Majalisar Dinkin Duniya ya gana da fira ministan kasar Norway Jonas Gahr Støre. A yayin ganawar da aka yi a ranar Talata, bangarorin biyu sun tattauna kan dangantakar da ke tsakanin kasashen Iran da Norway, tare da yin musayar ra’ayi kan ci gaban yankin da kasa da kasa. Taron dai ya yi tsokaci kan matsalar jin kai da Falasdinawa ke fuskanta daga sojojin mamayar Isra’ila sakamakon kisan kiyashin da ake ci gaba da yi a zirin Gaza da kuma...
Yarima mai jiran gado na Masarautar Saudiyya, Sheikh Muhammad bin Salman, ya jagoranci sallar jana’izar fitaccen malamin addini, Sheikh Abdulaziz bin Abdullah bin Muhammad Al-Sheikh. Shafin Inside Haramain ya ruwaito cewa an gudanar da jana’izar ce a Masallacin Imam Turki bin Abdullah da ke birnin Riyadh. CBN ya rage kuɗin ruwa zuwa kashi 27 cikin 100 Kotu ta hana NUPENG rufe Matatar Ɗangote Aminiya ta ruwaito cewa za a yi masa Salatul Ga’ib a Masallacin Harami na Makkah da kuma Masallacin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama da ke Madina. A wannan Talatar Allah Ya yi wa Babban Mai Ba da Fatawar na Saudiyya rasuwa yana da shekara 82. Fadar Masarautar ƙasar da kuma Shugaban Majalisar Malaman Masallata Haraman Makkah da...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa dandalin jawabi a MDD wata dama ce ta kasashen duniya su bayyana ra’ayinsu kuma Iran zata bayyana ra’ayinta a gobe Laraba 23 ga watan Satumba na wannan shekara ta 2025. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka jim kadan fafin ya shiga jirgi zuwa birnin NewYork a safiyar yau talata. Ya ce duniya a halin yanzu tana fuskantar danniya da babakere na wasu tsirarun kasashe a duniya. Sannan gaskiya mai dacin da ke faruwa a halin yanzu shi yadda yara da jarirai da suke mutuwa a gaza, a kisan kiyashin da HKI take aiwatarwa a Gaza kimani shekaru 2 da suka gabata. Sannan yayi allawadai da...
29. Florian Wirtz (Liverpool) 28. Virgil van Dijk (Liverpool) 27. Declan Rice (Arsenal) 26. Erling Haaland (Man City) 25. Denzel Dumfries (Inter Milan) 24. Fabian Ruiz (PSG) 23. Jude Bellingham (Real Madrid) 22. Alexis Mac Allister (Liverpool) 21. Serhou Guirassy (Borussia Dortmund) 20. Lautaro Martinez (Inter Milan) 19. Joao Neves (PSG) 18. Scott McTominay (Napoli) 17. Robert Lewandowski (Fc Barcelona) 16. Vinicius Jr (Real Madrid) 15. Viktor Gyokeres (Arsenal) 14. Desire Doue (PSG) 13. Harry Kane (Bayern Munchen) 12. Kvicha Kvaratskhelia (PSG) 11. Pedri Gonzalez (Fc Barcelona) 10. Nuno Mendes (PSG) 9. Gigio Donnarumma (Man City) 8. Cole...
Dangane da halin da ake ciki game da rikicin Falasdinu da Isra’ila, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana a yau Litinin 22 ga wata cewa, karfin soja ba zai iya samar da zaman lafiya ba, kuma tashin hankali ba zai iya samar da tsaro ba. Kasar Sin tana son yin hadin gwiwa tare da kasashen duniya wajen ci gaba da jajircewa a kan tsagaita bude wuta da kawo karshen yakin da ake yi a zirin Gaza, da kuma matukar nuna goyon baya ga tabbatar da adalci ga al’ummar Falasdinawa wajen maido da hakkinsu na kasa, da kuma kara azamar warware matsalar Falasdinu tun da wuri ta hanyar samar da cikakkiyar mafita, mai adalci...
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Jinjinawa Tawagar Kokawar Greco-Roma Ta Iran Murnar Lashe Gasar Cin Kofin Duniya
Jagoran juyin juya halin Musulunci yana taya tawagar kokawa ta Greco-Roma ta Iran murnar lashe gasar cin kofin duniya Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya taya tawagar kokawa ta Greco-Roman ta kasar Iran murnar nasarar da ta samu a gasar cin kofin duniya, yana mai godiya ga ‘yan wasa da masu horar da ‘yan wasa da masu gudanarwa da suka sanya farin ciki a zukatan al’ummar Iran da kuma abin alfahari ga kasar Iran. A cikin sakon nasa, Jagoran ya ce: Ina taya matasan kokawa murna. Ƙudurin ku da himma a cikin kokawa na Greco-Roman sun kawo farin ciki ga zukatan mutane da kuma alfahari ga ƙasar. Ina rokon Allah Ya ba ku daukaka da nasara,...
A kowane wata, hauhawar farashi ta kan kai kashi 0.74, yayin da a watan Agusta, hauhawar farashin abinci ya kasance kashi 1.65. A shekara-shekara, hauhawar farashi yana raguwa da kashi 12.03 idan aka kwatanta da kashi 32.15 da aka samu a watan Agusta 2024. Hukumar ƙididdiga ta bayyana cewa duk da hauhawar farashin na nan, saurin ƙaruwar farashin kayayyaki yana raguwa idan aka kwatanta da watannin da suka gabata. Dangane da iƙirarin tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, cewa Ƴan Nijeriya na “mutuwa da yunwa kullum,” Fasua ya ce: “Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, kawai ya sanya siyasa ce cikin lamarin a ƙoƙarinsa na son ya samu shiga ofishin shugaban ƙasa, ni kuma ba na yin tsokaci a harkokin...
A yau Lahadi 21 ga wannan wata da yamma, firaministan kasar Sin Li Qiang ya gana da tawagar membobin majalisar wakilai ta kasar Amurka da Adam Smith ya jagoranta a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing. A yayin ganawar, Li Qiang ya bayyana cewa, Sin da Amurka manyan kasashe ne dake da muhimmanci sosai a duniya, kiyaye dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka mai dorewa yadda ya kamata ya dace da moriyar kasashen biyu da begen kasa da kasa. Sin tana son yin kokari tare da kasar Amurka wajen girmama juna, da zama tare cikin lumana, da yin hadin gwiwar samun moriyar juna. Kana kasar Sin tana son kasar Amurka ta yi hadin gwiwa tare da ita don sa...
Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas ta bayyana cewa, laifukan da HKI take tafkawa akan jami’an kiwon lafiya suna da bukatar duniya ta yunkura cikin gaggawa. A wata sanarwa da kungiyar ta Hamas ta fitar a jiya Asabar wacce ta kunshi wannan bayanin ta kuma ce; Sojojin mamaya suna ci gaba da rusa sauran cibiyoyin kiwon lafiya da su ka saura a yankin Gaza,haka nan kuma kai wa likitoci da ma’aikatan kiwon lafiya hari. Kungiyar ta Hamas ta bayyana abinda HKI take yi a karkashin ci gaba da rusa duk wani abu mai amfani a yankin Gaza. Wani sashe na sanarwar kungiyar ta Hamas ya kuma ambaci cewa; Ya zuwa yanzu adadin likitoci da ma’aiaktan kiwon lafiya da HKI ta kashe...
Sanarwar ta ƙara da cewa, an bayar da ƙarin kayayyakin da za a raba a matsayin tallafin ne daga Hukumar Kula da Ilimi ta Duniya (UBEC) da UNICEF. A jawabinsa a wajen taron, Gwamna Lawal ya sake nanata cewa gwamnatinsa ta zo ne da aikin ceto da sake gina jihar. Ya ce: “Tun da farko mun gane cewa hanya mafi inganci wajen dawo da Zamfara kan turba ita ce saka hannun jari a zukatan al’ummarmu. “A yau, a cikin wannan alƙawari, na yi farin cikin sanar da raba kayayyakin koyo da koyarwa 408,137 da gwamnatin jihar Zamfara ta sayo kai-tsaye. “Wannan shi ne ɗaya daga cikin mafi girma na zuba jari a cikin albarkatun koyarwa da...
A ɓangare ɗaya kuma Turkiyya na ƙara nuna damuwa bayan harin da Isra’ila ta kai a birnin Doha. Mai magana da yawun ma’aikatar tsaro ta Turkiyya, Rear Admiral Zeki Akturk ya yi gargaɗin cewa “Isra’ila za ta iya faɗaɗa hare-harenta baya ga Ƙatar. Za ta iya ingiza yankin baki ɗaya cikin bala’i.” Mece ce shawarar da Masar ta bayar? Shawarar da Masar ta bayar ya ƙunshi samar da tsarin haɗe ayyukan sojin ƙasa da na sama da cibiyoyin tsaro, tare da haɗe cibiyoyin horaswa da ayyukan soji. Haka nan kuma ƙasashen ne za su yanke hukunci kafin amfani da dakarun bayan tattaunawa a tsakaninsu. Kafar yaɗa labarai ta Al Akhbar da ke Lebanon ta ce a ƙarƙashin tsarin, Masar ta...
“Sanarwar jan hankaki – Taron bogi ‘convocation’ a Nijeriya – Jami’ar ba ta ba Dauda Kahutu Rarara digirin girmamawa ba”. A yau (Lahadi) ne aka sanar da Jami’ar EAU labarin wani biki da kafafen yada labarai na Nijeriya suka rahoto ƙaryar cewa, Jami’ar ta gudanar da wani taro a ranar Asabar a Hotel din ‘NICON Luxury’ Abuja, Nijeriya. Jami’ar ba ta ba da izinin gudanar da wani taro a wannan wuri a ranar ba, kuma an shirya wannan taron ne ta hanyar damfara ba tare da sanin ko izinin Jami’ar ba. Waɗanda suka shirya wannan taron sun yaudari wasu da yardar cewa suna wakiltar Jami’ar EAU, amma wannan gaba ɗaya ƙarya ce kuma ba su da ikon yin...
Rahotanni daga Islamabad sun nuna cewa gwamnatin kasar tana kwatanta yarjejeniyar tsaro da ta kulla da kasar Saudiya ,da irin wadda ke tsakanin dakarun tsaron kasashen turai da kuma kungiyar tsaro ta nato. Kasashen saudiya da Pakistan sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro tsakaninsu a wata ganawa da aka yi tsakanin prime minisata shehabaz sharif na Pakistan da takwaransa na kasar Saudiya Mohammad bn Salman a birnin Riyadh a ranar laraba da ta gabata inda suka kirata da yarjejeniya kan dabarun kasa, Musadik ya fadi cewa yarjejeniyar bata barazana ga kowa, kuma bata gayyaci wani ya kai wa kowa hari ba, amma kamar idan wata kasa dake cikin kungiyar kwance ta nato akai kai mata hari to kamar an kai...
Jakadan Iran A Majalisar Dinkin Duniya Ya Ce: Kwamitin Sulhu Ya Rasa Damar Tattaunawa Da Fahimtar Juna
Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Kwamitin sulhun Majalisar ya rasa damar tattaunawa da fahimtar juna a yau Jakadan kasar Iran kuma wakilin din-din-din a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani, ya yi tsokaci kan rashin amincewa da daftarin kudiri na ci gaba da dage takunkumin da aka kakabawa Iran a taron kolin na yau, sakamakon matsin lamba daga kasashen Amurka da Turai. Irawani ya bayyana a yayin taron kwamitin sulhun a jiya Juma’a cewa: Kwamitin sulhun ya yi watsi da damar tattaunawa da fahimtar juna, yayin da Rasha da China bisa gaskiya suka gabatar da wani madaidaicin kudiri na tsawaita kudurin Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 2231 da kiyaye tsarin diflomasiyya. Ya ce: “Maimakon amincewa da...
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce jam’iyyarsa a shirye ta ke, ta haɗa kai da APC, idan an shirye karɓar sharuɗansu. Kwankwaso, ya faɗi haka ne a gidansa da ke Miller Road a Kano, lokacin da ya karɓi baƙuncin tsohon jigon APC a jihar, Buhari Bakwana, tare da wasu jiga-jigai. Babu wani hari da aka kai sakatariyar NUJ a Yobe — ’Yan Sanda An cafke mutum 6 kan tono gawa a kabari don yin asiri a Gombe Ya bayyaa musu yadda shi da wasu ’yan siyasa wajen kafa jam’iyyar APC a 2013 kuma sun sha wahala kafin kafuwarta. “Babu wanda zai faɗa min irin wahalar da muka sha wajen kafa APC....
Matasa takwas a jihar Jigawa sun lashe tallafin kasuwanci na Naira miliyan biyu daga British Council ƙarƙashin shirin Youth Connect. Kowane ɗaya daga cikinsu ya samu Naira dubu dari biyu da hamsin domin fara ayyukan kasuwanci. An gudanar da shirin ne tare da haɗin gwiwar Kings Trust International, CITAD, da gwamnatin jihar Jigawa. Matasa tamanin aka horas a tsawon makonni takwas kan kasuwanci, fasahar zamani da kuma ƙwarewar tallatawa, inda daga cikinsu guda takwas suka fito a matsayin zakaru. Wakilin British Council, Dr. Yahaya Janga, ya shawarci matasan da su yi amfani da horon da suka samu da kuma tallafin wajen kafa kasuwanci mai dorewa. Ya kuma yaba wa gwamnatin Jigawa da sauran abokan hulɗa da suka tallafa...
Mutane da dama na nuna damuwa game da mmakomar ayyukansu tun bayan fitowar fasahar AI. Sai dai yayin da wasu manazarta suke ganin fasahar za ta raba mutane da ayyukansu, wasu kuwa gani suke yi wannan ba abu ne mai yiwuwa ba. NAJERIYA A YAU: Wadanne Kalubale Gwamna Fubara Zai Fuskanta Bayan Dawowa Mulkin Ribas? DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya Shirin Najeriya A Yau na wanna lokaci zai yi nazari ne kan sayyukan da fasahar AI za ta iya raba mutane da su. Domin sauke shirin, latsa nan
An sabunta wannan ƙididdiga kusan shekaru shida kamar yadda ya kamata a yi. Abin da ya kamata mu mai da hankali a kai shi ne, ƙididdiga da bayanai su kasance masu sahihanci kuma a yawaita samun su. “An sabunta ƙididdigar, kuma ya nuna mana ainihin halin da muke ciki. Don haka, duk wani ra’ayi na son zuciya da wani ke ganin ya kamata mu kasance kusa da kashi 30, wannan ra’ayinsu ne kawai. Muhimmin abu shi ne an sabunta ƙididdiga watanni da dama da suka wuce, kuma abin da muke gani yanzu shi ne raguwar hauhawar farashi da ta ci gaba.” Fasua ya kuma ambaci cewa Naira ta samu tagomashi a kwanakin baya kuma farashin mai na hauhawa a kasuwar...
A ranar 18 ga watan Satumban shekarar 1931, sojojin Japan suka tarwatsa wani sashi na layin dogo dake karkashin ikonsu, a kusa da birnin Shenyang, tare da zargin sojojin kasar Sin da aikata barna, domin su fake da hakan wajen kai hari barikin sojojin Sin dake kusa da birnin na Shenyang a daren ranar, da kuma hakan ne suka kaddamar da mamayar da suka kitsa cikin kasar Sin. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa (SEMA) tare da haɗin gwiwar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) da Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF sun shirya horar da aikin ceto yayin ambaliya, a Ƙaramar Hukumar Auyo. Taron horaswar ya haɗa masu ruwa da tsaki daga hukumomi daban-daban, inda aka bai wa mahalarta ƙwarewa da ilimin da ya dace domin samun nasarar ceto da kuma kai dauki ga al’ummomin da ambaliya ta shafa. A yayin horon, an gudanar da darussa kan dabarun bincike da ceto, bayar da taimakon farko, da hanyoyin kwashe jama’a daga wuraren da ambaliya ta shafa. Wannan shiri ya nuna jajircewar SEMA, NEMA, da UNICEF wajen horar da...
A kokarin ta na ci gaba da zaburar da ma’aikatan ta, Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce za ta shirya taron bitar sanin makamar aiki ga jami’an ta dake dawainiya da alhazai a gida da kuma kasa mai tsarki. Darakta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed umar labbo ya bayyana haka bayan kamala taro na musamman da shugabannin sassa na hukumar da aka gudanar a shelkwatar hukumar dake Dutse babban birnin jihar. Yayi bayanin cewar, hukumar zata bada bitar ne ga jami’an da kuma shugabannin shiyya-shiyya kan hanyoyin kara kula da walwala da jin dadin maniyyata da kuma dabarun magance kalubale yayin gabatar da aikin hajji. Yana mai cewar bada horo na da matukar mahimmaci duba da yadda...
Rundunar ‘yan Sandan Jihar Jigawa ta bada sanarwar nasarar cafke wani sojan bogi da ƙarin wasu mutum biyu da ake zargi da satar mota a ƙauyen Sabon Sara. Kamar yadda Kakakin rundunar ’yan sanda na Jigawa, SP Shiisu Lawan Adam ya sanarwa manema labarai a garin Dutse cewa, an kama matashin sojan bogin da abokansa da ake zargin su da satar mota a ƙauyen Sabon Sara, cikin ƙaramar hukumar Kafin Hausa. Kasar Albania ta nada mutum-mutumi a matsayin minista Gwamnatin Gombe ta gyara hanyoyin kiwo domin daƙile rikicin manoma da makiyaya A cewar majiyar an kama sojan bogin mai suna Kabiru Musa da abokan aikinsa Umar Ali da Sabi’u Bashir, dukkansu ‘yan asalin Jihar Kano. A cewar kakakin rundunar waɗannan...
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana matukar alhininsa kan asarar rayuka da aka yi a gobarar da ta tashi a ranar Talata a Afriland Towers da ke Broad Street, a Legas. A cikin wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara kan yada labarai, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce shugaba Tinubu ya jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa, da kuma hukumomi da ma’aikatan hukumar tara haraji ta tarayya (FIRS), United Capital, United Bank for Africa (UBA) Plc, da kuma Afriland Properties Limited. Ya kuma jajanta wa wadanda suka rasa ‘yan uwansu a wannan bala’in, tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa. Shugaba Tinubu ya yaba da matakin da hukumomin gaggawa...
Ministan Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziƙi, Wale Edun, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta raba wa talakawa Naira biliyan 330 a matsayin tallafi. Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Abuja, inda ya ce an raba kuɗin ne ta Ofishin Tsare-tsaren Jin-ƙai na Ƙasa (NASSCO), domin rage wa talakawa wahalar cire tallafin mai da sauyin musayar kuɗaɗen waje. An kashe ’yan ta’addan IPOB da yawa a Imo — ’Yan Sanda ’Yan bindiga sun sako ma’auratan da suka sace a Katsina bayan biyan N50m A cewarsa, aƙalla gidaje miliyan 19.7 (sama da mutum miliyan 70) aka sanya a Rajistar Tsarin Tallafa Wa Talakawa, kum tallafin ya kai ga gidaje miliyan 15. “Zuwa yanzu, gidaje miliyan 8.5 sun samu aƙalla Naira...
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar wa kungiyar mafarauta/Yanbulala reshen jihar Jigawa na rundunar a shirye ta ke ta shirya wani horo na kara musu karfin gwiwa ga mambobinsu. Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Dahiru Muhammad ya bayar da wannan tabbacin ne a yayin wani taro da aka yi da mafarauta/Yanbulala na yankin wanda Lamido Wada ya jagoranta a Dutse babban birnin jihar. Ya bayyana cewa, Rundunar za ta hada gwiwa da wadanda abin ya shafa domin fuskanatar kalubalen zirga-zirga don daukar matakin da ya dace. A cewarsa, rundunar ta ci gaba da shirye-shiryen ‘yan sanda da al’umma ke tafiyar da su ta hanyar samar da hadin gwiwa mai karfi da masu ruwa da tsaki da suka himmatu...
Dan wasan kokawa mai nauyi na Iran ya samu lambar zinare ta farko a gasar cin kofin duniya. Wasan karshe da na rarrabuwar kawuna na manyan nau’ikan nau’ikan nauyi hudu na gasar kokawa ta duniya da aka yi a yammacin Lahadi a Zagreb. A cewar Pars Today, Amirhossein Zare daga Iran wanda ya taba zama zakaran duniya sau biyu kuma ya samu lambar azurfa da tagulla a gasar Olympics, ya fafata da Georgi Meshvildishvili, wanda ya samu lambar tagulla daga gasar Olympics ta Paris da ke wakiltar Azarbaijan a wasan karshe. Zare ya yi nasara da ci 5-0, inda ya samu lambar zinare ta uku a gasar cin kofin duniya. Bugu da kari, a wannan gasar, Ahmad Mohammadzadeh Javan dan...
Gwamnatin Jigawa ta amince da sabon tsarin ka’idojin aiki domin aiwatar da shirin kula da lafiyar mata masu juna biyu, da jarirai da ƙananan yara kyauta a cibiyoyin lafiya na jihar. Kwamishinan Yaɗa Labarai, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya bayyana haka bayan zaman majalisar zartarwa da aka gudanar a gidan gwamnati Dutse. Ya ce ka’idojin za su taimaka wajen inganta nagartar hidima, fayyace karewar ma’aikata, da kuma tabbatar da gaskiya, da bin doka da tsari a asibitoci. Kwamishinan ya ƙara da cewa matakin ya dace da manufar gwamnatin jihar na rage mace-macen mata da yara da kuma tabbatar da samun ingantacciyar kulawa ga kowa. Ya ce za a fara aiwatar da tsarin nan take, tare da horas da shugabannin asibitoci...
Rahotannin da suke fitowa daga Gaza sun ce, fiye da Falasdinawa 35 ne su ka yi shahada daga Safiyar yau Laraba zuwa tsakiyar rana,sanadiyyar hare-haren da HKI take kai wa. Hakan tana faruwa ne a daidai lokacin da ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta yi gargadi akan cewa asibitocin yankin sun kusa daina aiki baki daya. Tashar talabijin din ‘aljazira’ ta kasar Qatar ta ce,adadin wadanda su ka yi shahada har zuwa marecen yau sun kai 51,38 daga cikinsu a cikin birnin Gaza kadai. A gefe daya rahoton tashar talbijin din ta ‘aljazira’ ya bayyana cewa; HKI ta yanke hanyoyin sadarrwa na “Internet’ a fadin Gaza, haka nan kuma ta hana hukumar lafiya ta duniya ( w.h.o) shigar da makamashi...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da ƙarin kasafin kuɗi na Naira Biliyan 75 na shekarar 2025, ga gwamnatin jiha da kuma ƙananan hukumomi 27. Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan zaman majalisar da aka gudanar a gidan gwamnati dake Dutse, babban birnin jihar. Ya bayyana cewa, wannan ƙarin kasafin kuɗi ya samo asali ne daga ƙarin kuɗaɗen shiga domin biyan buƙatun kuɗaɗen da suka taso, da kuma ƙarfafa manyan fannoni da za su kawo ci gaba mai ɗorewa a faɗin jihar. Alhaji Sagir Musa Ahmed ya ce, majalisar ta amince da Naira Biliyan 58 ga gwamnatin jiha da kuma Naira Biliyan 17 ga Kananan Hukumomi 27,...
A daidaikun kasuwannin Abuja da wasu manyan birane na ƙasar nan, an bayyana yadda farashin doya ke ƙara hawa fiye da yadda ake tsammani. Wannan na faruwa ne duk da cewa yanzu sabuwar doya ta fara shigowa kasuwa, bisa al’ada, a duk shekara fitowar sabuwar doya kan karya farashin wanda yake kasuwa. Sai dai a bana, wasu daililai na sa farashin doya kara hawa. NAJERIYA A YAU: Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau Uku wannan shine batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba akai. Domin sauke shirin, latsa nan
Gwamnatin Tarayya ta ce Najeriya na rasa sama da Dala Biliyan 10 duk shekara sakamakon asarar amfanin gona bayan girbi. Ministan Noma Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka a wajen kaddamar da shirin Hanyar Inganta Noma da Kayayyakin Mire Rayuwa a Yankunan Karkara G.R.A.I.N a ƙaramar hukumar Birnin Kudu ta Jihar Jigawa. Ya ce asarar na faruwa ne saboda rashin ingantattun wuraren ajiya, karancin ababen more rayuwa, sauyin yanayi da kuma ambaliya. Kyari ya bayyana cewa noma na bada gudunmawar kashi 24 bisa 100 na Jimillar Darajar Kayayyaki da Ayyuka da Kasa ta Samar a Cikin Shekara GDP, inda ƙananan manoma ke samar da sama da kashi 70 bisa 100 na abincin da ake ci a ƙasa....
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Matakin hana malaman da ba su da rajista hawa mumbari a Neja yana ci gaba da yamutsa hazo a ciki da wajen jihar. Yayin da wasu suke ganin wannan mataki bai dace ba, wasu kuwa gani suke faduwa ta zo daidai da zama, wato matakin ya zo a daidai lokacin da ake bukata. NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar Ruwa DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau Uku Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kan tanadin Dokar Kasa game da wannan batu. Domin sauke shirin, latsa nan
JMI ta zama zakara a gasar damben girgajiya ta kasa da kasa bayan ta fara shiga gasar shekaru 12 da suka gabata . Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi yana taya tawagar yan damben murna da nasarar da suka samu, ya kumakara da cewa wannan shi ne nasara ta wasannan kasa-da kasa har guda 6 wadanda Iran take samun lambobin zakara a cikinsu a wannan shekarar. Labarin ya kara da cewa yan damben Iran sun sami wannan nasarar kwana guda kafin a kammala gasar. An bayyana nasarar da yan damben Iran suka samu ne a jiya Litinin da yamma a birnin Zagreb inda aka gudanar da gasar. Sun sami lambobin...
Babban daraktan kamfanin dillancin labaran kasar Qatar ya bayyana cewa taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC da ke tafe yana nuni da wani muhimmin sauyi na hadin kan kasashen larabawa da musulmi dangane da laifukan da ake aikatawa kan al’ummar Palastinu. A cewar Pars Today, dukkanin idanuwa a ranakun Lahadi da Litinin (15-16 ga Satumba, 2025) za su kasance a Doha, babban birnin kasar Qatar, wanda zai karbi bakuncin taron gaggawa na shugabannin kasashen Larabawa da na Islama, don ba da amsa ga baki daya kan harin da Isra’ila ta kai kan Qatar. Ana gudanar da wannan taron gaggawa ne a cikin yanayi na musamman na yanki da na duniya kuma ya biyo bayan harin da...
Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar
“Sauran motocin da ke cikin ayarin, ciki har da wacce ke ɗauke da shugaban majalisar, da ƙyar suka iya tsayawa wanda tsakaninsu mitoci kaɗan ne daga wurin da haɗarin ya afku,” in ji wani ganau. Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa, an garzaya da jami’an ‘yansandan da suka samu raunuka zuwa babban asibitin Gumel a sume amma daga baya sun farfaɗo. Da yake magana kan lamarin, mataimakin shugaban majalisar, Aqeel Akilu, ya yi godiya ga Ubangiji cewa, ba a rasa rayuka ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko...
Tawagogin Sin Da Na Amurka Sun Sake Tattaunawa Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya A Rana Ta Biyu
A yau Litinin ne tawagogin kasashen Sin da Amurka, suka sake tattaunawa a rana ta biyu, game da batutuwan tattalin arziki da cinikayya a birnin Madrid na kasar Sifaniya. A jiya Lahadi, sassan biyu sun gudanar da zaman farko ne a fadar Santa Cruz, inda ofishin ministan harkokin wajen kasar ta Sifaniya yake. A cewar kakakin ma’aikatar cinikayyar kasar Sin, sassan biyu za su tattauna batutuwan da suka hada da matakin Amurka na kakaba jerin haraji daga bangare guda, da keta matakan kayyade fitar da hajoji, da batun dandalin TikTok. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don...
Majalisar dattawa ta dakatar da Sanata Akpoti-Uduaghan a ranar 6 ga Maris, 2025, na tsawon watanni shida. Duk da cewa an kalubalanci lamarin a kotu, amma babbar kotun tarayya ba ta bayar da wani umarni na soke dakatarwar ba ko kuma tilasta sake dawo da ita bakin aiki. A ranar 4 ga Satumba, 2025, Sanatar ta sanar da ofishin magatakarda akan aniyar ta na ci gaba da ayyukan majalisa, nan take, ofishin ya mika wasikar ga shugabannin majalisar dattawan. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
Lawal ya ƙara da cewa, ɗaukacin guraren da Jiragen Ruwa ke tsaya, akwai launin da kuma lamba da aka amince,manyan motocin za su rinƙa yin amfani da su, domin yin zirga-zirga a Tashar ta Apapa. “Misali, a APMT, manyan motocin za su rinƙa yin amfani da lamba 001 mai ɗauke launin ruwan bula, inda kuma a ENL Consortium, za su rinƙa yin amfani da lambApapaETO bisa nufin rage cunkoso a ciki da kuma wajen Tashar ta Apapa.ɗauke da launin rawaya,” Inji Lawal. Ya bayyana cewa, wannan sabon garanbawul ɗin da aka yi, za ta taimaka wajen matsalar ƙetarawa hanyar da manyan motocin ke fuskanta a Tashar ta Apapa. Lawal ya ci gaba da cewa, bisa nazarin da aka gudanar a...
Wani gini mai hawa uku da ake ginawa ya rufta kan mutane a unguwar Yaba, da ke Jihar Legas. Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), ta ce ginin ya rufta ne da misalin ƙarfe 8 na dare. Gwamnatin Kuros Riba ta bankaɗo ma’aikatan bogi 800 HOTUNA: Mahaifiyar Dangote ta halarci gasar karatun Alƙur’ani ta Shetty a Kano Shaidu sun ce akwai mutane biyar zuwa shida a cikin ginin lokacin da abin ya faru. NEMA ta ce ta ceto mutum huɗu, kuma an garzaya da su asibiti domin kula da lafiyarsu. Sai dai hukumar ta ce ba a tabbatar da adadin waɗanda har yanzu suke ƙarƙashin ginin ba, yayin da ake ci gaba da aikin ceto.
Ma’aikatar kula da cinikayya ta Sin ta sanar a yau Juma’a cewa, biyo bayan amincewar kasashen Sin da Amurka, He Lifeng, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS kuma mataimakin firaministan kasar, zai jagoranci wata tawaga zuwa Spaniya daga ranar 14 zuwa 17 ga watan Satumba, domin tattaunawa da tawagar Amurka. A cewar ma’aikatar, bangarorin biyu za su tattauna kan haraje-harajen Amurka da yadda aiwatar da matakan kayyade fitar da kayayyaki da batun manhajar TikTok da sauran batutuwan tattalin arziki da ciniki. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
Sanarwar ta ƙara da cewa, SABER wani shiri ne na shekaru biyar, wanda ya dogara da aiki, wanda Bankin Funiya ke tallafawa, wanda aka tsara shi cikin tsanaki domin wargaza shingayen faɗuwar jari, da zaburar da sana’o’i masu zaman kansu, da samar da ayyukan yi masu ɗorewa ga al’ummar Zamfara. Za a raba Naira 150,000 ga mutum 2,000 a faɗin jihar domin tallafa wa ƙananan sana’o’i. Bugu da ƙari, mutane 1,000 a ƙanana da matsakaitan sana’o’i za su karbi Naira 500,000 kowanne. Haka kuma, mutane 60 daga matsakaita da manyan ‘yan kasuwa za su ci gajiyar tallafin Naira miliyan biyar kowannen su. A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya bayyana cewa, SABER ba wani abu ba ne na yau...
Mai ba da shawara ga Jagora kan harkokin kasa da kasan ya jaddada ccewa; Dole ne duniya ta daina yin shiru game da zaluncin ‘yan sahayoniyya Ali Akbar Velayati mai ba da shawara ga jagora kan harkokin kasa da kasa ya yi Allah wadai da wuce gona da irin da yahudawan sahayoniyya suka kai a kasar Qatar, yana mai cewa: Dole ne duniya ta daina yin shiru kan zaluncin yahudawan sahayoniyya saboda ba su san iyaka kan laifukansu ba. Velayati ya bayyana a shafinsa na twitter game da harin da gwamnatin ‘yan sahayoniyya suka kai wa kasar Qatar yana mai cewa: Keta dokokin kasa da kasa da keta alfarmar kasashe ya zama al’ada ga ‘yan sahayoniyya, kuma dole ne duniya...
Akalla Falasdinawa 48 ne suka yi shahada a harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai a zirin Gaza tun daga wayewar garin yau Juma’a Falasdinawa 48 ne suka yi shahada a ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan zirin Gaza tun daga wayewar garin yau Juma’a. Majiyoyi a asibitocin Gaza sun bayyana cewa: Shahidai 27 ne a kai zuwa asibitin Al-Shifa, shahidi daya zuwa asibitin Al-Ma’amoudiya, shahidai uku zuwa asibitin shahidan Al-Aqsa, da shahidai biyar zuwa asibitin Nasser. Wani Falasdine ya yi shahada kana wasu kuma suka jikkata lokacin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai hari a wani gida da ke unguwar Sheikh Radwan da ke arewacin birnin Gaza. Share 0...
A yayin da suka yi alƙawarin yin adawa da aiwatar da harajin, ƙungiyar ta ƙara da cewa: “Yajin aiki na kan tebur idan gwamnati ta yi ƙoƙarin watsi da wannan gargaɗi ta ci gaba da aiwatar da waɗannan manufofi. Don haka, TUC ta umarci dukkan kwamitocin jihohi, rassan ƙungiya, da tsarin ta a faɗin ƙasa da su kasance cikin shiri, sanya ido, kuma su jira ƙarin sanarwa wanda zai iya kai wa ga ɗaukar mataki mai ƙarfi idan gwamnati ta ƙi sauraron muradin jama’a.” Ƙungiyar ta kuma kira ga abokan hulɗarta – ƙungiyoyin farar hula, ƙungiyoyin ƙwararru, ɗalibai, ƙungiyoyin kasuwa, shugabannin addini da duk ƴan Nijeriya masu kishin ƙasa – da su tsaya tare da ita a wannan gwagwarmaya. “Tare,...
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya sha alwashin dakile kafa kasar falasdinawa yayin da ya sanya hannu kan yarjejeniyar gaggauta ci gaba da ginin matsugunan yahudawa a yankin El, na yamma da kogin Jordan da Isra’ilan ta mamaye. A jiya Alhamis ne Netanyahu ya sanya hannu kan yarjejeniyar, duk da kashedin da sassan kasa da kasa suka jima suna yi, cewa hakan zai gurgunta damar falasdinawa ta kafa kasa mai cin gashin kai. Yankin da Isra’ila ke fatan ginawa, mashigi ne a bangaren gabashin birnin Kudus, tsakanin birnin da yankin unguwar Ma’ale Adumim, ana kuma ganin gina shi zai haifar da mummunan tasiri, kasancewar hakan zai raba gabashin birnin Kudus da arewacin gabar kogin Jordan, wanda hakan zai dakile damar samar da dunkulalliyar kasar falasdinawa a nan...
“Gwamnatin Jihar Kaduna ta shirya tsaf domin ɗaukar matakin gaggawa kan kowanne yanayi da ka iya tasowa sakamakon wannan hasashen yanayi. An umurci KADSEMA da ta yi aiki tare da dukkan hukumomi masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cikakken shiri. Ana roƙon jama’a da su bi dukkan umarnin kariya, su share magudanan ruwa, kuma su guji wuraren da ambaliya ke yawan faruwa a wannan lokaci,” in ji Maiyaki. Hakazalika, sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (KADSEMA), Dakta Usman Hayatu Mazadu, ya jaddada muhimmancin kasancewa cikin shiri da kuma bin matakan kariya da ke cikin sanarwar. “Hasashen yanayi ya nuna cewa za a samu guguwar iska da ruwan sama mai yawa musamman a ranakun Laraba...
Da safiyar yau Alhamis ne aka gudanar da taron manema labarai game da taron tattaunawa karo na 12 na dandalin Xiangshan wanda za a gudanar a nan Beijing daga ran 17 zuwa 19 ga watan Satumban nan a cibiyar taro ta duniya ta Beijing, bisa taken “Hadin kai don kare tsarin duniya, da habaka ci gaban zaman lafiya”, inda za a gudanar da cikakken zama har sau 4 tare da kuma tarurruka 8 na rukuni-rukuni, da kuma taron shugabanni, da taron tattaunawa tsakanin matasan jami’an soja da masana, da na tattaunawa tsakanin manyan masana na Sin da na kasashen waje. Wakilan da za su halarci taron sun hada da na kasashe masu arziki, da manyan kasashe masu tasowa, da kananan...
Gwamnatin Belarus ƙarƙashin jagorancin Shugaba Alexander Lukashenko ta saki fursunoni siyasa 52 ciki har da fitaccen ɗan adawa, Mikola Statkevich da kuma ɗan jarida Ihar Losik, a wani yunƙuri da aka danganta da ruwa da tsakin Amurka. Shugaban Lithuania, Gitanas Nauseda, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X (Twitter), yana mai cewa: “Mutum 52 da aka daure bisa dalilan siyasa sun tsallako kan iyaka daga Belarus zuwa Lithuania lafiya.” Daruruwan magoya bayan NNPP sun tarbi Kwankwaso a Kalaba Kotu ta yanke wa jagoran Ansaru hukuncin ɗaurin shekaru 15 Ya ce yana “matuƙar godiya” ga gwamnatin Amurka da Shugaba Donald Trump bisa rawar da suka taka wajen sasantawa da cimma wannan matsaya. Daya daga cikin wadanda aka sako shi ne...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Za a kuma ƙaddamar da sabon shiri, Nigeria@65 Compendium, wanda zai zayyano ci gaban ƙasa a fannoni kamar shugabanci, tattalin arziƙi, da ci gaban ƙasa a tsawon shekarun. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar Zaɓen Nijeriya INEC ta amince da jam’iyyar ’yan haɗaka ta ADC, ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban Majalisar Dattawa, David Mark. Wannan tabbaci na zuwa ne bayan hukumar ta wallafa sunayen shugabannin jam’iyyar a shafinta na intanet, abin da ya kawo ƙarshen dogon jira da aka yi tun bayan ayyana ta a matsayin jam’iyyar haɗin kan ’yan adawa a ranar 2 ga Yuli. Masu zanga-zanga sun ƙone matar tsohon Firaministan Nepal Yadda zanga-zangar adawa da rashawa ta rikiɗe zuwa tarzoma a Nepal Tun a watan Yulin ne dai gamayyar ’yan adawa suka ayyana David Mark a matsayin shugaban jam’iyyar, tare da tsohon Gwamnan Osun, Rauf Aregbesola, a matsayin sakatarenta na ƙasa. Sai dai kafin yanzu, INEC ba ta sanya sunayensu a...
Babban Layin wutar lantarki na Najeriya ya sake faɗuwa. Wannan matsala ta haifar da katsewar wuta a wasu sassan ƙasar, wanda ya jefa masu amfani da lantarki cikin damuwa. Kotun Ghana ta ɗaure ’yan Najeriya 3 shekaru 96 saboda satar mota Mamakon ruwan sama ya hallaka mutum 3 a Zariya Bayanan da Hukumar Gudanar da Wutar Lantarki, sun nuna cewa wutar ta ragu daga megawat 2,917 zuwa megawat 1.5 daga tsakanin ƙarfe 11 na safe zuwa 12 na ranar Laraba. Kamfanin rarraba wuta na Abuja (AEDC), ya tabbatar da faruwar matsalar a saƙon da ya aike wa kwastomominsa. Ya ce wutar ta ɗauke ne sakamakon matsalar da aka samu daga layin ƙasa da misalin ƙarfe 11:23 na safe. “Saƙonmu zuwa...
Wasu mahara sun harbe jami’an ’yan sanda uku har lahira da safiyar ranar Laraba a wata madakatar mota da ke garin Egbe, a Ƙaramar Hukumar Yagba Yamma a Jihar Kogi. Kakakin rundunar jihar, SP William Aya, ne ya tabbatar da harin. Babban layin wutar lantarki ya sake faɗuwa Injin niƙa ya yi ajalin matar aure mai ’ya’ya 6 a Gombe Ya ce harin ya faru ne a kan iyakar Jihar Kogi da Jihar Kwara. SP Aya, ya ƙara da cewa, Kwamishinan ’yan sandan jihar, Miller Dantawaye, ya tura tawaga ta musamman domin bincika yankin domin kama waɗanda suka kai harin. “Ina tabbatar muku cewa ’yan sandanmu uku sun mutu a Egbe yau. Kwamishina ya tura tawaga ta musamman, kuma muna...
Babban Layin wutar lantarki na Najeriya ya sake faɗuwa. Wannan matsala ta haifar da katsewar wuta a wasu sassan ƙasar, wanda ya jefa masu amfani da lantarki cikin damuwa. Kotun Ghana ta ɗaure ’yan Najeriya 3 shekaru 96 saboda satar mota Mamakon ruwan sama ya hallaka mutum 3 a Zariya Bayanan da Hukumar Gudanar da Wutar Lantarki, sun nuna cewa wutar ta ragu daga megawat 2,917 zuwa megawat 1.5 daga tsakanin ƙarfe 11 na safe zuwa 12 na ranar Laraba. Kamfanin rarraba wuta na Abuja (AEDC), ya tabbatar da faruwar matsalar a saƙon da ya aike wa kwastomominsa. Ya ce wutar ta ɗauke ne sakamakon matsalar da aka samu daga layin ƙasa da misalin ƙarfe 11:23 na safe. “Saƙonmu zuwa...
Ministan Kudi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun ya bayyana cewa ba za a fara aiwatar da shirin cire harajin man fetur na kashi 5 cikin 100 ba nan take. Ministan ya fadi hakan ne a ranar Talata a wani taron manema labarai a ofishinsa da ke Abuja. Ministan ya kuma ce ba za a fara aiwatar da harajin man fetur a watan Janairun 2026 ba lokacin da za a fara aiwatar da wasu harajin da shugaba Bola Tinubu ya sanya wa hannu a bana. Har yau, babu wani shiri na gaggawa na aiwatar da shirin fara cire harajin kashi 5 na man fetur da ‘yan kasa suke sha,” in ji Ministan a martanin da ya mayar dangane da cece-ku-ce...
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ba da izinin bayar da wani kaso na kudaden Khumusi ga al’ummar Gaza A matsayin martani ga kuri’ar raba gardama kan halaccin bayar da wani kaso na kudaden Khumusi ga al’ummar Gaza da ake zalunta, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamene’i ya ba da izini na addini na fitar da wani kaso na kudaden Khumusi don haka. A cikin cikakken labarin, a baya-bayan nan ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ba da izini na addini na ba da izinin bayar da wani kaso na kudaden Khumusi ga al’ummar Falastinu da ake zalunta a Gaza. Ga rubutun tambaya da amsar, kamar yadda gidan yanar gizon KHAMENEI.IR ya...
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa, rashin imanin da Amurka ke da shi ne ya sa yin shawarwari da wannan kasa ba shi da amfani. Wannan labarin daga Pars Today ya yi nazari kan matsayin Imam Khamenei dangane da mugun imanin Amurka da manufofinsa. Menene ra’ayin Imam Khamenei kan mugun imanin Amurka da manufofinsa? Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei a wata ganawa da yayi da dakarun Basij na Iran ya yi ishara da cewa Amurka ba ta cika alkawuran da ta dauka yana mai cewa: “A cikin JCPOA, sun ce, ‘Idan kun rage ayyukan masana’antar nukiliya ku, za mu yi waɗannan abubuwa: ɗage takunkumi, ɗaukar wasu ayyuka, yin wannan da wancan.’ Shin sun yi...
“Jared Sacks” da “Zukiswa Wanner,” marubuta da masu fafutukar al’adu da ke zaune a Cape Town, sun rubuta a cikin wata kasida ga Al Jazeera mai taken “Me yasa za mu je Gaza tare da jiragen ruwa na ‘Sumoud’ na duniya?”: Mun tashi don ci gaba da bege. Rasa bege na nufin watsi da mutanen Gaza da kuma mika su ga gwamnatin zalunci. “Jared Sacks” da “Zukiswa Wanner,” marubuta da masu fafutukar al’adu da ke zaune a Cape Town, sun lura a cikin wata kasida ga Al Jazeera mai taken “Me ya sa za mu je Gaza tare da jiragen ruwa na ‘Sumoud’ na duniya?”: A cikin watanni 23 da suka gabata, mun shaida yadda gwamnatin wariyar launin fata ta...
An samu damar tattauna muhimman abubuwa a babban taron kamar hanyoyin zuba jari a jihohin Ogun da Zamfara na Nijeriya da kuma yankin Bungoma na ƙasar Kenya. Manyan mambobin kwamitin sun tattauna damarmakin zuba jari a jihohin Ogun da Zamfara a Nijeriya yankin Bungoma na Kenya. A jawabin sa ga masu zuba hannun jari a duniya, Gwamna Lawal ya jaddada cewa gwamnatin sa ta himmatu wajen sauya labarin Zamfara daga ƙalubale zuwa wani babban matsayi mai cike da damarmaki. “Gwamnatina ta himmatu wajen samar da ingantaccen yanayi da ɗorewar yanayin zuba jari. Ina nan a yau a matsayin abokin tarayya, a shirye nake na ba ku cikakken haɗin kai don buɗe hanyoyin jin daɗin gare mu duka....
Kasashen larabawa da kungiyoyin kasa da kasa da wasu kasashen duniya sun yi tir da hare-haren da HKI ta kai kan birnin Doha babban birnin Qatar a kokarinta na kashe shuwagabannin kungiyar Hamasa a yau Talata. Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa babban sakataren MDD Antonio Gotterre ya yi tir da hare-haren da jiragen yakin HKI suka kai birnin Doha na kasar Qatar ya kuma bayyana cewa hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa. Haka ma babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa Ahmad Gaith ya yi tir da hare-haren da HKI ta kai gine-gine a Doka. Sannan kasashen Iran Saudia da Hadaddiyar daular Larabawa duk sun yi allawadai da hare-here. Gwamnatin kasar Turkiyya ta yi allawadai da...
Hukumomi sun shawarci jama’a su tabbatar da cewa gidajensu suna da tsaro da karko, tare da kaucewa gina gidaje a kan magudanan ruwa a wannan lokacin na damina. Hukumar Hasashen Yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta yi gargaɗin cewa Kirikasamma na daga cikin wuraren da za a iya fuskantar ambaliyar ruwa a bana. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin Tarayya, NUPENG Da Ɗangote Sun Fara Tattaunawa Don Kawo Ƙarshen Yajin Aikin Ma’aikatan Mai
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da jami’an Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA), wakilan kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC, shuwagabannin kamfanin ‘MRS Holdings Limited’ da kuma kungiyar ‘yan kasuwa ta kasa (TUC). Da yake bayyana bude taron, Minista Dingyadi ya jaddada aniyar gwamnati na sulhu a tsakanin kungiyar da masu gudanar da masana’antu. Ya bayyana bangaren mai da iskar gas a matsayin jigon tattalin arzikin Nijeriya, yana mai gargadin cewa tsawaita yajin aikin zai haifar da mummunan sakamako ga kasar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya...
Kasar Sin da Tarayyar Afrika (AU), sun yi alkawarin karfafa goyon bayan juna wajen gina tsarin jagorantar harkokin duniya bisa adalci tare da tabbatar da zaman lafiya a duniya. An yi alkawarin ne a ranar Juma’a yayin wani taron manyan jami’ai a Addis Ababa na Habasha, albarkacin cika shekaru 80 da Sinawa suka yi nasarar turje wa harin Japan da yakin duniya na II. Da yake jawabi ga taron, Jiang Feng, shugaban tawagar kasar Sin a AU, ya nanata bukatar tunawa da tarihi da karfafa hadin gwiwa a duniya domin shawo kan kalubalen tsaro da duniya ke fama da su. Da yake jawabi a madadin kwamishinar kula da harkokin lafiya da jin kai da ci gaban al’umma Amma Twum-Amoah, babban...
Daruruwan kungiyoyin sa kai ne suka gudanar da zanga-zanga a kasar malesiya domin nuna adawa da ziyarar shugaban Amurka Donal Trump a karshen watan gube saboda nuna goyon bayan isra’ila kan kisan kare dangi da take yi a Gaza, , sun bukaci gwamnati da ta soke gayyatar wanda suka bayyana shi a matsayin babban mai laifin yaki dake da hannu wajen kisan kare dangi da isra’ila ke yi wa alummar Gaza, da hakan ya sabama dukkan dokokin kasa da kasa. Mazu zanga zangar sun daga kwalaye da a ciki aka rubuta cewa trump kada ka zo,kuma mafiywancin wadanda suka halarci zanga-zangar mata ne da yara, kuma kungiyar dake nuna goyon bayan falasdinu ce ta jagoranci zanga-zangar, fira ministan malesiya anwar...