Kasashe 77 Ne Na Duniya Suka Fice A Lokacin Jawabin Fira Ministan Isra’ila A Taron Majalisar Dinkin Duniya
Published: 28th, September 2025 GMT
Kasashen duniya 77 ne suka kauracewa jawabin fira ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a Majalisar Dinkin Duniya
Wani bincike da Isra’ila ta gudanar ya nuna cewa kasashe 77 ne suka fice daga zauren Majalisar Dinkin Duniya a lokacin da fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benyamin Netanyahu ke jawabi ga babban zauren Majalisar a birnin New York.
Jaridar Yedioth Ahronoth ta Isra’ila ta ruwaito cewa: Bayan duba kasashen da suka kaurace wa jawabin, an gano cewa: “dukkan makwaftan Isra’ila hudu, baya ga Saudiyya” na daga cikin mutane 77 da suka kauracewa taron, lamarin da ya sa Netanyahu ya yi magana a wani zauren da ke kusa da babu kowa.
Sabanin haka jaridar yahudawa ta yabi wakilan Bahrain da Hadaddiyar Daular Larabawa da suka ci gaba da zama a zauren taron inda suka saurari jawabin Netanyahu, duk kuwa da takun saka tsakanin bangarorin biyu dangane da yakin da ake ci gaba da yi a zirin Gaza da kuma burin wasu mambobin kawancen Netanyahu na mamaye yammacin kogin Jordan.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Majalisar Dinkin Duniya Ta Sake Kakabawa Iran Takunkumin Rashin Adalci September 28, 2025 Shugaban Majalisar Shawarwar Musulunci Ya Ce: Iran Ba Zata Kimanta Takunkumin Da Aka Kakaba Mata Ba September 28, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 149 September 28, 2025 Takunkuman MDD kan Iran sun fara aiki September 28, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (A) 148 September 28, 2025 Nijar ta yi Tir da kasashen ketare kan tada zaune tsaye a Sahel September 28, 2025 Italiya : Mutane da dama sun jikkata yayin arangama da masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinu September 28, 2025 Isra’ila ta kashe Falasdinawa kusan 100 a hare-haren da ta kai a Gaza September 28, 2025 Pezeshkian: Iran za ta dauki matakan da suka dace domin shawo kan takunkumi September 28, 2025 Afirka ta Kudu da Sin sun kara habaka huldar tattalin arziki don tukarar harajin Amurka September 28, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Majalisar Dinkin Duniya
এছাড়াও পড়ুন:
Isra’ila Tana Ci Gaba Da Rushe Gidaje A Yankin Gaza
Da safiyar Yau Laraba ne sojojin Haramtacciyar kasar Isra’ila su ka kai hare-hare a yankuna daban-daban na zirin Gaza, tare da rushe gidaje da dama. Sojojin mamayar sun yi amfani da jiragen sama marasa matuki da kuma tankokin yaki domin rushe gidajen. A arewacin Gaza da gabashin Jabaliya sojojin na mamaya sun yi amfani da manyan bindigogi akan gidajen fararen hular. A unguwar “Tuffah” ma an ga yadda sojojin mamayar su ka aike da jiragen yaki marasa matuki.A can kudancin Gaza kuwa jiragen yakin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ne su ka kai hare-hare akan barin Bani-Suhaila a gabashin Khan-Yunus,a lokaci daya kuma manyan bingigoginsu su ka bude wuta akan iyaka.
Tun bayan da aka tsagaita wutar yaki a cikin watan Oktoba ne, Sojojin mamayar Haramtacciyar Kasar Isra’ilan suke ci gaba da kai hare-hare akan Gaza ba tare da kakkautawa ba. Daga tsagaita wutar zuwa yanzu adadin Falasdinawan da su ka yi shahada a sanadiyyar hare-haren na ‘yan sahayoniya sun haura 300.
Hukumar agaji a yankin na Gaza ta yi gargadi akan cincirindon ‘yan hijira da suke rayuwa a cikin hemomin da babu kayan da rayuwa take da bukatuwa da su domin ci gaba. Ruwan sama yana ci gaba da sauka a yankuna mabanbanta na Gaza da sanyi yake karuwa ba tare da samar da na’urorin dumama hemomin ba.
Kakakin kungiyar agaji a Gaza Mahmud Basal ya ce; Suna samun dubban koke daga Gaza cewa hemomin da mutane suke rayuwa a ciki ba su dace da rayuwa ba ko kadan.Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Uganda: An Kama Fiye Da ‘Yan Hamayyar Siyasa 300 A Lokacin Yakin Neman Zabe November 26, 2025 Reuters: Kungiyar Likitoci Ba Da Iyaka Ba Ta Fice Daga Asibitin Darfur Bayan Bude Wa Ma’aikatanta Wuta November 26, 2025 Shugaban Iran: Kasuwar jarin cikin gida sirrin nasarorin gwamnati na tattalin arziki November 26, 2025 Larijani: Hadin gwiwar Iran da Pakistan na taimaka wa zaman lafiya a yankin November 26, 2025 Al-Houthi ya yi ta’aziyyar shahadar babban kwamanda na Hizbullah November 26, 2025 UNIFIL: Isra’ila tana sabawa wa kudurorin MDD a cikin Lebanon November 26, 2025 Matsalolin Tsaro A Yankunan Bakin Ruwa A Kasar Siriya Ya Kai Ga Zanga-Zangar Lumana November 26, 2025 Aljeriya Ta Bukaci Kasashen Duniya Su Dauki Mataki Don Kawo Karshen Ta’asan HKI A Yankin Asiya Ta Kudu November 26, 2025 Shugaban Majalisar Koli Ta Taron Kasa Iran Ya Yabawa Pakistan Saboda Goyon Bayanta November 26, 2025 EU da AU na taro kan diyya ga laifukan mulkin mallaka da cinikin bayi November 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci