Aminiya:
2025-11-18@07:28:14 GMT

An shiga taron gaggawa kan takun saƙar PENGASSAN da Matatar Dangote

Published: 30th, September 2025 GMT

Shugabannin ƙungiyar manyan ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya (PENGASSAN) da wakilan Matatar Dangote na halartar wani taron gaggawa tare da wakilan Gwamnatin Tarayya.

Shugaban ƙungiyar PENGASSAN, Festus Osifo, tare da Babban Sakataren Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (TUC), Nuhu Toro, ne ke jagorantar ɓangaren ƙungiyoyin ƙwadago, yayin da Ministan Ƙwadago da Ayyuka, Maigari Dingyadi da wasu jami’ai ke wakiltar Gwamnatin Tarayya.

Ya zama tilas ɗalibai su gabatar da ‘Project’ kafin rajistar NYSC — Tinubu Gwamnatin Tarayya ta ayyana hutu ranar Laraba

Aminiya ta ruwaito cewa tun a ranar Lahadin da ta gabata ce Gwamnatin Tarayya ta gayyaci shugabannin PENGASSAN da na ɓangaren Matatar Dangote zuwa wannan taro sakamakon rikicin da ke tsakanin ɓangarorin biyu.

Sai dai, duk da cewa an tsara fara taron da misalin ƙarfe 2:00 na ranara Litinin, an soma shi da misalin ƙarfe 3:50 na yamma saboda jinkirin isowar wasu manyan masu ruwa da tsaki, kafin daga bisani a shiga bayan labule.

Da yake jawabi a taron, Minista Dingyadi ya ce: “Abin da ke faruwa yau yana da matuƙar muhimmanci ga tattalin arziƙin ƙasa da tsaron ƙasa baki ɗaya, la’akari da cewa PENGASSAN ta shiga yajin aiki.”

Babu shakka a yayin da rikici yake ƙara sama a tsakanin ma’aikata da Matatar Dangote, PENGASSAN ta tsunduma wani yajin aikin da ya tsaida ayyuka a kusan duk harkar mai na Nijeriya.

Duk da ƙoƙari na tsomin baki a bangaren mahukuntan Najeriya dai daga duk alamu an yi tsaiwa irin ta gwamen jaki a tsakanin ’yan ƙungiyar PENGASSAN da ke cewa Matatar Dangote ba ta da ikon korar wasu ma’aikata sama da 800 bisa ’yancinsu na shiga ƙungiyar

Tun da sanyin safiyar yau dai ne ma’aikata suka rufe ofisoshi da hukumomi da ke kula da harkar man, wani abu da ke kama da kokari na aike sako.

Ma’aikatan dai sun rufe ofisoshin hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Najeriya (NMDPRA) da hukumar makamashi ta Najeriya (ECN), da kuma hukumar kula da haƙo man fetur ta NUPRC.

A halin yanzu, masana’antu da hukumomin mai na fuskantar matsin lamba saboda rufe wuraren aiki, yayin da jama’a ke bayyana damuwa kan yiwuwar tasirin wannan rikici ga farashin mai da samun man fetur a ƙasar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Matatar Dangote Gwamnatin Tarayya Matatar Dangote

এছাড়াও পড়ুন:

Shugaban Nukiliyar Iran Yace Amurka Da Israila Sun Shiga Sabon Mataki Mai Hadari

Shugaban hukumar makamashin nukiliya ta kasar iran Mohammad Eslami ya bayyana cewa harin da Amurka da isra’ila suka kai kan tashohin nukiliyar ta a tsakiyar watan yuli ya nuna cewa Amurka da kawayenta ciki har da isra’ila suna harin naurorin kimiyya na jamhuriyar musulunci ta iran ne.

Shugaban ya fadi hakan ne a wata hira da yayi da gidan talbajin din Al-Masirah na kasar Yamen inda ya jaddada” cewa ba’a taba kai irin wannan harin ba kan nauraron kimiyyar kasar a cikin tarihi, don haka yanayi kai harin yana nuna cewa Amurka da kawayenta sun shiga wani sabon mataki mai hadari, na karuwar tashin hankali kan yakin da suke yi da kimiyyar kasar iran.

A ranar 13 ga watan juni ne isra’ila ta kaddama da yaki kan kasar iran inda ta kashe manyan kwamandodjin sojojinta da masana nukuliya da sauran fararen hula ,

 bayan fiye da mako daya kuma Amurka ta shi ga cikin yakin kai tsaye inda tayi ruwan bama -bamai kan tashohin nukiliyar iran wanda hakan keta hurumin majalisar dinkin duniya da kuma yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukuliya NPT ne.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hamas Da Sauran Bangarorin Falasdinawa Sun yi Watsi Da Shirin Aikewa Da Dakarun Kasashen Waje A Yankin Gaza November 17, 2025 Nukiliya : Iran zata sake duba huldarta da IAEA idan aka dauki wani sabon mataki kanta November 17, 2025 Kwamitin tsaro zai kada kuri’a kan daftarin kudirin Trump kan Gaza November 17, 2025 Ansarullah Ta Yi Allah Wadai Da Sabunta Takunkumin MDD Kan Yemen November 17, 2025 Afirka ta Kudu na Binciken shigar wasu ‘yan gudun hijirar Falasdinu 153 cikin kasar November 17, 2025 Najeriya ba za ta buga kofin duniya ba karo na biyu a jere November 17, 2025 DRC: An Kulla Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Tsakanin Gwamnati Da Kungiyar M23 November 16, 2025 An Yi Kira A Bai Wa ‘Yan Hijira Saboda Sauyin Muhalli Kariya November 16, 2025  An Amince Da  Sauye-sauye A Tsarin Mulkin Kasar Benin November 16, 2025 Isra’ila Ta Kai Wa Sojojin MDD Hari A Kasar Lebanon November 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Sin Ba Ta Taba Bukatar Kamfanoni Su Tattara Ko Adana Bayanai Ba Bisa Ka’ida Ba Kuma Ba Za Ta Yi Hakan Ba 
  • An Bude Taron Tattaunawa Kan Wayewar Kai Tsakanin Sin Da Kasashen Larabawa Karo Na 11 A Beijing
  • Shugaban Nukiliyar Iran Yace Amurka Da Israila Sun Shiga Sabon Mataki Mai Hadari
  • ’Yan bindiga 5 Sun shiga hannun ’yan sanda a Kebbi
  • NAJERIYA A YAU: Matsayar Doka Kan Taron Da Jam’iyyar PDP Ta Gudanar
  • Ɗan Najeriya ya kashe mahaifinsa, ya yanki ƙannensa da wuƙa a Amurka
  • Gwamnatin Gombe ta bai wa alƙalai da Khadi-Khadi kyautar sabbin motoci 16
  • AU ta sake nanata cewa “Babu kisan kare dangi a arewacin Najeriya
  • Ma’aikatan lafiya sun tsunduma yajin aiki
  • Ma’aukatan lafiya sun tsunduma yajin aiki