Leadership News Hausa:
2025-09-17@20:28:33 GMT

Tawagogin Sin Da Amurka Za Su Tattauna A Spaniya

Published: 13th, September 2025 GMT

Tawagogin Sin Da Amurka Za Su Tattauna A Spaniya

Ma’aikatar kula da cinikayya ta Sin ta sanar a yau Juma’a cewa, biyo bayan amincewar kasashen Sin da Amurka, He Lifeng, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS kuma mataimakin firaministan kasar, zai jagoranci wata tawaga zuwa Spaniya daga ranar 14 zuwa 17 ga watan Satumba, domin tattaunawa da tawagar Amurka.

A cewar ma’aikatar, bangarorin biyu za su tattauna kan haraje-harajen Amurka da yadda aiwatar da matakan kayyade fitar da kayayyaki da batun manhajar TikTok da sauran batutuwan tattalin arziki da ciniki. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Dakatar Da Shuka Kiyayya Da Tashin-Tashina A Tekun Kudancin Sin

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce Sin na kira ga Amurka, da ta gaggauta dakatar da shuka kiyayya, da haifar da tashin hankali, da rura wutar gaba a tekun kudancin kasar Sin, kana ta kyale a dawo da yanayin zaman lafiya da daidaito a yankin. Lin Jian, ya bayyana hakan ne yau Litinin, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, lokacin da aka yi masa tambaya kan batun.

Wasu rahotanni daga kafofin watsa labarai sun bayyana cewa, a baya bayan nan, sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, ya fitar da sanarwa dake cewa Amurka na goyon bayan kasar Philippines, game da watsi da ta yi da tsare-tsaren kasar Sin na kafa yankin kare muhallin halittu a tsibirin Huangyan Dao.

Lin ya ce “Mun gabatar da kakkarfan korafi a yau, dangane da kuskuren da Amurka ta tafka. Tsibirin Huangyan Dao yankin kasar Sin ne tun fil azal”, kuma kafa yankin kare muhallin halittu a tsibirin na karkashin ikon mulkin kai na Sin, wanda hakan ke nufin yana bisa turba, ya dace da doka, bai kuma cancanci suka ba. (Saminu Alhassan)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Bude Dandalin Tattauna Batutuwan Tsaro Na Xiangshan Karo Na 12 A Beijing 
  • Har Kullum Burin Sin Shi Ne Wanzar Da Daidaito Da Cimma Moriya Tare Da Amurka
  • An tattauna yadda za a inganta walwalar malamai a Gombe
  • Lakurawa Sun Hallaka Jami’in Kwastam A Jihar Kebbi
  • Ma’aikatar Shari’ar Iran Ta Sanar Da Rataye Dan Leken Asirin Hukumar Mossad Ta Isra’ila
  • Sin Da Amurka Sun Yi Tattaunawar Keke-da-keke Kan Batutuwan Cinikayya Da Manhajar TikTok
  • Tawagogin Sin Da Na Amurka Sun Sake Tattaunawa Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya A Rana Ta Biyu
  • Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Dakatar Da Shuka Kiyayya Da Tashin-Tashina A Tekun Kudancin Sin
  • Barcelona Ta Farfaɗo Zuwa Matsayi Na Biyu Bayan Lallasa Valencia A Johan Cruyff
  • Sin Da Amurka Sun Fara Gudanar Da Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya A Madrid