Matasa 8 Sun Sami Tallafin Kasuwanci Na Miliyan 2 A Jigawa
Published: 19th, September 2025 GMT
Matasa takwas a jihar Jigawa sun lashe tallafin kasuwanci na Naira miliyan biyu daga British Council ƙarƙashin shirin Youth Connect.
Kowane ɗaya daga cikinsu ya samu Naira dubu dari biyu da hamsin domin fara ayyukan kasuwanci.
An gudanar da shirin ne tare da haɗin gwiwar Kings Trust International, CITAD, da gwamnatin jihar Jigawa.
Matasa tamanin aka horas a tsawon makonni takwas kan kasuwanci, fasahar zamani da kuma ƙwarewar tallatawa, inda daga cikinsu guda takwas suka fito a matsayin zakaru.
Wakilin British Council, Dr. Yahaya Janga, ya shawarci matasan da su yi amfani da horon da suka samu da kuma tallafin wajen kafa kasuwanci mai dorewa. Ya kuma yaba wa gwamnatin Jigawa da sauran abokan hulɗa da suka tallafa wa shirin.
Shi ma Daraktan CITAD, Farfesa Yunusa Zakari Ya’u, ya ce shirin na nufin bai wa matasa ƙwarewar da zata taimaka musu wajen samun ayyukan yi da kuma dogaro da kai.
A nasa jawabin, Kwamishinan Matasa da Wasanni na Jigawa, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya ce gwamnatin jihar na baiwa ci gaban matasa muhimmanci, tare da jan hankalin waɗanda suka ci gajiyar da su yi amfani da tallafin yadda ya dace.
Waɗanda suka ci nasarar, sun gode wa British Council, Kings Trust International da CITAD bisa wannan damar da suka samu.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga sun sako ma’auratan da suka sace a Katsina bayan biyan N50m
Wani ɗan kasuwa a Jihar Katsina mai suna Anas Ahmadu da matarsa, Halimatu wadda ke ɗauke da juna biyu, da kuma ’yarsu mai shekaru biyu, sun kuɓuta daga hannun ’yan bindiga, bayan sun shafe kwanaki 21 a hannunsu.
An sako su ne a daren ranar Laraba bayan biyan kuɗin fansa Naira miliyan 50, kamar yadda wani ɗan uwansu ya bayyana wa Aminiya.
Gobara ta kashe manyan jami’an hukumar FIRS 4 a Legas NAJERIYA A YAU: Wadanne Kalubale Gwamna Fubara Zai Fuskanta Bayan Dawowa Mulkin Ribas?“Alhamdulillah! Anas, Halimatu da ’yarsu sun kuɓuta. Yanzu haka suna kan hanyarsu ta zuwa gida, amma sai da aka biya ’yan bindigar kuɗin fansa Naira miliyan 50,” in ji shi.
An sace su ne a ranar 26 ga watan Agusta, 2025 a gidansu da ke Filin Canada Quarters, a Jihar Katsina.
Da farko, mahafan sun nemi Naira miliyan 600, daga baya suka rage kuɗin zuwa miliyan 100, sannan daga ƙarshe suka amince aka biya su miliyan 50.
Saboda dalilan tsaro, ’yan uwansu ba su bayyana inda aka sako su ba.