Bayan Taron UNGA 80, Shettima Ya Nufi Jamus Don Tattaunawa Da Bankin Deutsche
Published: 28th, September 2025 GMT
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bar birnin New York na Amurka, bayan kammala wakiltar Shugaba Bola Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 (UNGA). Ya nufi Jamus domin ganawa da jami’an Bankin Deutsche kan batutuwan haɗin gwuiwa da zuba jari a shirye-shiryen ci gaban Nijeriya.
A yayin taron UNGA, Shettima ya samu yabo daga Sakatare-Janar na MDD, António Guterres, bisa ƙoƙarin Nijeriya na neman kujerar dindindin a Kwamitin Tsaro.
Ya kuma jaddada buƙatar garambawul a Majalisar Ɗinkin Duniya, inda ya buƙaci a baiwa Afrika ikon sarrafa arziƙin ma’adanan da darajarsu ta kai dala biliyan 700. Shettima ya kuma tattauna da gidauniyar Gates kan faɗaɗa kiwon lafiya da ilimi, kana ya jawo hankalin masu zuba jari kan kasuwar dala tiriliyan 3.4 na African Continental Free Trade Area (AfCFTA).
Mataimakin Shugaban Ƙasar ya bar filin jirgin sama na John F. Kennedy (JFK) inda ministoci da jami’an ofishin jakadancin Nijeriya suka raka shi. An tabbatar da cewa zai dawo gida kai tsaye bayan kammala aiyukansa a Jamus.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya yi wa Maryam Sanda afuwa
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa Maryam Sanda afuwa, wadda aka yanke wa hukuncin kisa a shekarar 2020 bisa laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello, ɗan tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Alhaji Haliru Bello.
Maryam,’ mai shekara 37, ta shafe shekaru shida da watanni takwas a gidan yarin Suleja kafin yi mata afuwa.
Talauci da tsangwama na hana yara mata karatu a Gombe — Kwamishina Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaroRahotanni sun nuna cewar an yi mata afuwar ne bayan yin nadama da aikata kyakkyawan halaye.
Iyayen Maryam sun roƙi gwamnati da ta sake ta saboda ’ya’yanta biyu da ta ke da alhakin kula da su, tare da alƙawarin sauya halayenta.
Shugaba Tinubu, ya kuma yi wa wasu mutane afuwa da suka haɗa da Manjo Janar Mamman Vatsa, Ken Saro-Wiwa, da kuma Sir Herbert Macaulay.
Gaba ɗaya mutane 175 ne shugaban ya yi musu afuwa, ciki har da masu manyan laifuka, tsoffin fursunoni, da waɗanda suka yi kyakkyawan tuba.
Wannan shi ne karon farko da Shugaba Tinubu ya yi amfani da ikon yafe laifi don tausaya wa waɗanda suka aikata laifuka tun bayan hawansa mulki.