NAJERIYA A YAU: Ayyukan Da Fasahar AI Za Ta Raba Mutane Da Su Nan Ba Da Jimawa Ba
Published: 19th, September 2025 GMT
Mutane da dama na nuna damuwa game da mmakomar ayyukansu tun bayan fitowar fasahar AI.
Sai dai yayin da wasu manazarta suke ganin fasahar za ta raba mutane da ayyukansu, wasu kuwa gani suke yi wannan ba abu ne mai yiwuwa ba.
NAJERIYA A YAU: Wadanne Kalubale Gwamna Fubara Zai Fuskanta Bayan Dawowa Mulkin Ribas? DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin NajeriyaShirin Najeriya A Yau na wanna lokaci zai yi nazari ne kan sayyukan da fasahar AI za ta iya raba mutane da su.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji Sun Raba Takin Zamani Ga Manoma A Katsina
Rundunar Brigade ta 17 na Sojojin Najeriya da ke Katsina ta raba buhunan takin zamani ga manoma a ƙauyuka shida da ke kusa da sansanin Natsinta, cikin Jibia da Katsina.
Kwamandan brigade ɗin, Birgediya Janar Babatunde Omopariola, ya ce an yi hakan ne don ƙarfafa dangantakar sojoji da al’umma, tare da taimaka musu wajen noma, lafiya da ilimi.
Ya kuma nemi haɗin kan jama’a wajen bayar da bayanai da sintiri domin tabbatar da tsaro a jihar.
A madadin al’umma, shugaban ƙauyen Katoge, Malam Abubakar Bala, ya gode wa sojojin, inda ya bayyana cewa takin zai taimaka wajen bunkasa noma, kuma sun dade suna amfana da tsaro da taimakon sojoji a yankin.
Kauyukan da suka amfana da rabon takin sun hada da Natsinta, Katoge, Garke, Dan-negaba, Unguwar Sarkin Aiki, da Tsangaya.
Daga Isma’il Adamu