A kowane wata, hauhawar farashi ta kan kai kashi 0.74, yayin da a watan Agusta, hauhawar farashin abinci ya kasance kashi 1.65.

A shekara-shekara, hauhawar farashi yana raguwa da kashi 12.03 idan aka kwatanta da kashi 32.15 da aka samu a watan Agusta 2024.

Hukumar ƙididdiga ta bayyana cewa duk da hauhawar farashin na nan, saurin ƙaruwar farashin kayayyaki yana raguwa idan aka kwatanta da watannin da suka gabata.

Dangane da iƙirarin tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, cewa Ƴan Nijeriya na “mutuwa da yunwa kullum,” Fasua ya ce:

“Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, kawai ya sanya siyasa ce cikin lamarin a ƙoƙarinsa na son ya samu shiga ofishin shugaban ƙasa, ni kuma ba na yin tsokaci a harkokin siyasa.

“Ba lallai bane ya yaba da nasarorin gwamnatin yanzu ba, amma dai ya kyautu mu tsaya kan gaskiya da tabbatattun bayanai.”

Fasua ya amince cewa kashi 20.12 har yanzu babban kaso ne, amma ya jaddada cewa waɗannan lambobin yanzu sun nuna sabuwar ƙididdigar da aka daɗe ana jira.

Ya bayyana cewa: “Hauhawar farashi na kashi 20.12 har yanzu mai girma ne a wasu fannonin tattalin arziki saboda abin da yake nufi shi ne farashin kayayyaki na ci gaba da hauhawa a wasu fannoni, amma ba kamar yadda aka saba ba.

An sabunta wannan ƙididdiga kusan shekaru shida kamar yadda ya kamata a yi. Abin da ya kamata mu mai da hankali a kai shi ne, ƙididdiga da bayanai su kasance masu sahihanci kuma a yawaita samun su.

“An sabunta ƙididdigar, kuma ya nuna mana ainihin halin da muke ciki. Don haka, duk wani ra’ayi na son zuciya da wani ke ganin ya kamata mu kasance kusa da kashi 30, wannan ra’ayinsu ne kawai.

Muhimmin abu shi ne an sabunta ƙididdiga watanni da dama da suka wuce, kuma abin da muke gani yanzu shi ne raguwar hauhawar farashi da ta ci gaba.”

Fasua ya kuma ambaci cewa Naira ta samu tagomashi a kwanakin baya kuma farashin mai na hauhawa a kasuwar duniya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Farashi hauhawar farashi

এছাড়াও পড়ুন:

Yadda PDP Ta Yi Asarar Kudancin Kaduna

“Mutanen duk sun manta da ‘yan garancin da suka yi gaba dayansu suka shiga wani sabon babi. Babban bango da ake ingina da shi ya fadi. Yanzu Kudancin Kaduna na jam’iyyar APC ne.”

Ya yi bayanin komawar manyan mutanen biyu zuwa APC wani kokarin ci gaba ne na shi Kakakin majalisar, ya ce SHugaban majalisar ya kara jadddad Sanata Katung da Honorabul. Amos “sun zabi lamarin kawo ci gaba ne. Sun zabi su ci gaba da kasancewa da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne da kuma APC. Wannan ba karamin sauya jam’iyya bane. Jirgizar kasa ce ta siyasa. Wani sabon babi ne ga siyasar Kudancin Kaduna, da kuma gaba dayan Nijeriya.”

“’Yan ‘uwana maza da mata wannan sauay shekar wani sako ne, wanda yake nuna lokacin rarrabuwar kai ya kare. Sako ne da yake nuna al’ummar kudancin Kaduna sun shirya tsaf, su kara yin ci gaba saboda ciyar da ci gaban Nijeriya.Sako ne da yake nuna APC yanzu wuri ne na hadin kai, wurin sa kai, da kuma ci gaba.

“Shugaban kasa ya nuna cewar a shirye yake wajen ci gaban Kudancin na Kaduna. Ya saurari kukan da aka dade na yi na kada a manta da su a rika tafiya tare da su, ya kuma yi abinda ya kamata wajen share masu hawaye da, yin ayyukan da suka dace.

“Jami’ar kimiyya ta gwamnatin tarayya da aka yi a Kachia, da wannan mulkin na Tinubu yayi wata manuniya ce mai nuna cewar da akwai fata ta gari da kuma farfado da sha’anin ci gaba. Bada dadewa za ta budewa dalibai hanya domin a fara daidata hanyar data kamata wajen zakulo masu ilimin kimiyya a nan gaba kadan, wadanda za su rika bullo da abubuwan ci gaba da kuma tunanin da me da me suka kamata ayi.

“Kafa Asibitin gwamnatin tarayya a Kafanchan ya nuna cewa gwamnatin ta damu kwarai akan kowa da kowa lamarin kula da lafiyar al’umma. Wajen kawo saukin samun inda za aje domin kulawa da lafiya cikin sauki da kuma daukaka lamarin kula da lafiyar al’umma na Kudancin Kaduna.

“Hakanan ma kafa barikin sojoji a Samarun Kataf wani sabon babi ne na kokarin samar da zaman lafiya da tsaro aka sa a gaba. Yin hakan ya nuna matuka gwamnati ta shirya kamar yadda ya dace wajen kare rayuwar al’umma, da wuraren da suke zama, da kuma kwantar masu da hankali na nuna an damu da tsaron wurin da kwanciyar hakalin al’ummar da suke wurin.

“Duk wadannan suna ganin gaskiya da akwai adalci wajen tunawa da su al’ummar wajen.Hakan ya nuna Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yana tafiyar da jagorancinsa na cika alkawari wajen yin abubuwan da suka dace. Shi Shugaba ne mai yin abinda ya yi kuduri a zuciyarsa kawo ci gaba wurin daya dace matuka.”

Shugaban har ila yau ya tabbatar da an sa ko kuma daukar ‘yan asalin wurin wato Kudancin Kaduna wuraren da za su kawo ci gaban wurin ta hanyar la’akari da menene muradin Shugaban kasa akan lamarin da ya shafi wurin.

“An nada Bishop Matthew Hassan Kukah a matsayin jagora kuam Shugaba na wadanda za su jagorancin tafiyar ta jami’ar kimiyya ta gwamnatin tarayya, Kachia. Farfesa Kurid Williams Barnabas shi ne mataimakin Shugaban jami’ar na farko.Wadannan nade- naden wata girmamawa ce ta Kudancin Kaduna. Don haka hakan ya nuna ana lura matuka ga lamarin daya shafi kwarewa da kuma aiwatar da gaskiya.”

Shugaban majalisar Wakilai Abbas yace maganar gaskiya Gwanan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani“a matsayi wani mutum ne da yake bada gudunmawar ci gaba,”inda ya kara da cewa’ “yadda yake tafiyar da lamurran gwamnatinsa tamkar budewa kowa kofa ne ya shigo a tafi tare da shi, saboda ya daidaita kawunan al’umma wadanda a shekarun baya basu ga Maciji da juna. Ya daukaka ci gaba da nuna ya fi duk wani lamarin siyasa da kuma hada kai maimakon, maida hankali kan ita siyasar.”

A kowane lokaci Shugaban majalisa yana yiwa ‘yan kudancin Kaduna a matsayin ‘yan’uwansa ne maza da mata, “Irin soyayyar da yake yiwa yankin ta nuna lamarin ya dade tare da samun ranar cika kudurin. Abokantakar da yake da Shugabannin wurin wani abu ne wanda ya kunshi biyayya da kuma amana da mutunta juna.

“Aiki tare da Shugaban kasa Tinubu, mun tabbatar da cewa kasafin kudin 2025 da aka yiwa shi sashen na Kudancin Kaduna wani sabon babi ne mai nuna lalle ba a manta dasu ba. Kudancin Kaduna yanzu wani wuri ne na ci gaban kasa. Ayyukan da aka yi ba ayi su bane domin saboda yau kadai bane. Tamkar wani zuba jari ne aka yi saboda gaba. Saboda ayyukan za su ilimantar bunkasawa da daukakawa, da kuma samarwa al’ummar yadda za su san mutane domin ai kowa ya san sabo, da Maza ma jari ne saboda gaba.

Ya gode wa Shugaban majalisar Tajudden Abbas saboda yadda yake aiki tare da shi domin tabbatar da ba a manta da kowa ba wajen samar da ayyukan gwamnati, saboda kamar yadda ya ce sun samu nasarori cikin shekaru biyu da rabi da suka gabata.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Rahotonni Jerin Gwarazan Taurarinmu! November 7, 2025 Labarai Zaben Kananan Hukumomi A Neja Ya Bar Baya Da Kura November 7, 2025 Labarai Gwamnatin Zamfara Ta Ɗauki Malaman Makaranta 500 Aiki November 7, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Matsalar Tsaro: Yadda Dabarun Uba Sani Suka Mayar Da Tsoro Zuwa Kyakkyawar Fata A Jihar Kaduna
  • Tinubu ya gana da Sarkin Musulmi a Aso Rock
  • Abin Da APC Za Ta Yi Da Rinjayen Kashi Biyu Bisa Uku A Majalisar Tarayya
  • Matsalar Tsaro: Mun samu gagarumin ci gaba a shekaru biyu – Tinubu
  • Matsalar Tsaro: Mun sami gagarumin ci gaba a shekaru biyu – Tinubu
  • Yadda PDP Ta Yi Asarar Kudancin Kaduna
  • Mun fara tattaunawa da Amurka kan barazanar Trump – Gwamnatin Tarayya
  • An rantsar da shugaban Kamaru Paul Biya karo na 8
  • Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax
  • Hafsan sojin sama ya umarci a yawaita yi wa ’yan ta’adda ruwan bama-bamai