Majalisar Ɗinkin Duniya ta sake tallafawa Ilimin mata
Published: 1st, October 2025 GMT
Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya ya jaddada ƙudirinsa na yin aiki tare da Gidauniyar Malala a ƙoƙarinta na ci gaba da bunƙasa ilimi da magance ƙalubalen da ke hana miliyoyin yara, musamman ’yan mata rashin zuwa makaranta.
Da yake yi wa Malala Yousafzai maraba a ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya, Babban jami’in kula da ayyukan jin ƙai a ofishin Mohammed Malick Fall, ya ce Majalisar Ɗinkin Duniya zata yi aiki tare da gidauniyar Malala, wacce ta samu kyautar lambar yabo ta Nobel.
“Majalisar Ɗinkin Duniya ta sake jaddada goyon bayanta ga asusun Malala wajen ganin ‘ya’ya mata da yawa suna samun ingantaccen ilimi, kuma ba za a bar kowanne yaro a baya ba,’’in ji Mista Fall.
Jami’in Majalisar Ɗinkin Duniya ya jagoranci tawagar da ta ƙunshi Wakilai daga UNICEF, UNESCO, UNDP, UNFPA da mata na Majalisar Ɗinkin Duniya a wajen taron.
Ya jaddada cewa sauyi mai ma’ana a tsakanin al’umma ya ta’allaka ne kan irin jarin da aka saka a harkar ilimi musamman na ’ya’ya mata da kuma ƙarfafa musu gwiwa.
Ya ƙara da cewa, “tare da gwamnati da abokan hulɗar mu, mun ƙuduri aniyar wargaza duk wasu matsalolin da ke hana yara, musamman ma masu rauni damar samun ingantattacen ilimi.
Muhimman abubuwan da ke kawo cikas ga ilimi a Nijeriya sun haɗa da rashin tsaro, taɓarɓarewar tattalin arziki, sauyin yanayi da kuma nau’in yanayin zamantakewa da al’adu.
Sai ya yi kira da a ƙara sa himma wajen samar da daidaiton jinsi da kuma ƙarfafa haɗin kan al’umma wanda su ne gimshiƙin hanyoyin samun ci gaba mai ɗorewa.
Malala, wacce ta zo Abuja a ranar 26 ga watan Satumba don taron shekara-shekara na Hukumar Kula da Asusun Malala, ta sake nanata irin rawar da Nijeriya ke takawa wajen bunƙasa na Asusun na 2025 zuwa 2030.
“Nijeriya ce ƙasa mai bada fifiko ga asusun Malala, tun daga shekarar 2014, inda aka zuba jarin sama da Dala miliyan 8 daga ƙungiyoyi na haɗin gwiwa da kuma ƙaƙarin da Nijeriya take na daƙile shingayen da ke hana yara mata zuwa makaranta,” in ji ta.
Ta zayyana dabarun gidauniyar asusun Malala a Nijeriya, waɗanda suka haɗa da tabbatar da cewa ’yan mata masu aure da masu juna biyu za su iya komawa makaranta don haɓaka tallafin ilimi da tabbatar da biyan buƙatun ’yan mata da kuma yin amfani da ilimi a matsayin hanyar warware matsalar auren yara.
Shugabar Gidauniyar Malala a nan Nijeriya, Nabila Aguele ta nanata ƙudurin gidauniyar na ganin dukkan ’yan mata za su iya samun damar kammala karatu na tsawon shekara 12 a Nijeriya.
Ta jaddada aniyar gidauniyar na mayar da hankali ga kan ƙarfafa haƙƙin ’ya’ya mata don ganin aƙalla sun samu ilmin sakandire kafin aure.
Yayin da take Abuja, Yousafzai za ta tattauna da ‘yan mata matasa da masu fafutukar neman ilimi da gidauniyar Malala ke tallafawa domin jin ta bakinsu da kuma labaransu da burinsu da kuma irin sauye-sauyen da suke son gani a yankunansu.
Za ta kuma haɗu da manyan jami’in gwamnati da shugabannin ƙungiyoyin fararen hula don samun sauye-sauyen manufofi da kuma yin haɗin gwiwa don bunƙasa ci gaban ilimin ’ya’ya mata a faɗin ƙasar nan.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gidauniyar Malala Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya Majalisar Ɗinkin Duniya gidauniyar Malala
এছাড়াও পড়ুন:
Hukumar Kwallon Kafa Ta Kasar Turkiyya Ta Dakatar Da ‘Yan Wasa 1024 Saboda Laifin Caca
Kamar ‘yan wasa da masu horarwa, an hana jami’an wasa shiga ayyukan yin caca bisa ga ka’idojin TFF, da kuma na FIFA da hukumar gudanarwa ta Turai (Uefa), masu gabatar da kara na Turkiyya sun bayar da umarnin tsare mutane 21 ciki har da alkalai 17 da shugabannin kungiyoyin kwallon kafa biyu a wani bangare na babban bincike kan yin caca da kuma shirya yadda sakamakon wasa zai iya fitowa.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA