Muhimman abubuwa 7 da Najeriya ta fada yayin jawabinta a taron MDD
Published: 25th, September 2025 GMT
A yayin taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya (UNGA) karo na 80, Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya gabatar da jawabin Najeriya a madadin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Jawabinsa ya ƙunshi kira ga gyare-gyare, adalci a harkokin tattalin arziki, da goyon bayan zaman lafiya da haɗin kai na duniya.
Ga muhimman batutuwa bakwai da Najeriya ta jaddada a yayin jawabinta a wannan taron:
Bai wa Najeriya kujera a Kwamitin Tsaro na majalisarNajeriya ta buƙaci samun kujerar dindindin a Kwamitin Tsaro/Sulhu na majalisar, tana mai cewa rashin wakilcin Afirka a matakin yanke shawara na duniya yana rage kimar tsarin.
Shettima ya jaddada cewa rawar da Najeriya ke takawa a harkar zaman lafiya da tsaro ta cancanta a ba ta kujerar dindindin a kwamitin.
“Bukatar mu ta kujerar dindindin… kira ne na adalci, wakilci, da gyaran da zai dawo da martabar wannan majalisar da ke ɗauke da burin haɗin kai na duniya.”
A cikin kalamai masu ƙarfi, Shettima ya jaddada goyon bayan Najeriya ga samar da mafita ta kasashe biyu a rikicin Isra’ila da Falasdinu.
Ya buƙaci a bai wa Falasdinawa ’yanci da mutunci kamar sauran al’ummar kowacce kasa, yana mai kiran halin da ake ciki a yankin a matsayin babban tabo ga muradun duniya.
“Muna fada ba tare da wata shakka ba, cewa mafita ta kasashe biyu ita ce hanya mafi mutunci da za ta kawo zaman lafiya mai ɗorewa ga al’ummar Falasdinu.”
Gyara tsarin kuɗi na duniyaShettima ya buƙaci a sake fasalin tsarin kuɗi na duniya don ya dace da halin da ƙasashe masu tasowa ke ciki.
Ya soki tsarin bashi da saka hannun jari da ke tauye ci gaban ƙasashe masu tasowa musamman na Afirka.
Najeriya ta soki yadda ake cin moriyar ma’adinan Afirka ba tare da amfani da su wajen bunƙasa al’umma ba. Shettima ya buƙaci a samar da ayyukan yi da masana’antu a yankunan da ake haƙar ma’adanan, tare da bunkasa haɗin gwiwa.
“Za mu ƙarfafa tsarin duniya idan ƙasashen da ke samar da ma’adanan duniya suka ci moriyar su ta fuskar zuba hannun jari, haɗin gwiwa, sarrafa su a gida da samar da ayyukan yi.”
Rage tazarar fasaha a AfirkaShettima ya gabatar da shirin haɗin gwiwa na duniya don rage gibin tazarar da aka yi wa nahiyar Afirka a fannin fasaha.
Ya buƙaci haɗin gwiwa tsakanin gwamnatoci, masana, da kamfanoni masu zaman kansu don tabbatar da cewa ci gaban fasaha ya shafi kowa.
Yaki da yaɗa labaran karyaShettima ya bayyana haɗarin da ke tattare da kirkira da kuma yada labaran ƙarya, musamman a ƙasashen da ke da raunin tsarin dimokuraɗiyya.
Ya buƙaci a samar da matakan kariya da za su tabbatar da gaskiya da amincewa a duniyar fasaha.
Kira kan samar da kotun kuɗi ta duniyaNajeriya ta buƙaci a kafa kotun duniya da za ta rika duba harkokin kuɗi da warware rikice-rikice a tsakanin ƙasashe.
Wannan, a cewar Shettima, zai ƙara gaskiya da bin doka a harkokin kuɗi na duniya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Najeriya ya buƙaci a haɗin gwiwa Ya buƙaci a Najeriya ta Shettima ya
এছাড়াও পড়ুন:
Ramaphosa ya soki kalaman Trump na cewa ba zai gayyaci shi a taron G20
Shugaban Afirka ta kudu, Cyril Ramaphosa ya soki kalaman takwaransa na Amurka Donald Trump na cewa ba zai gayyace shi taron kasashen gungun G20 mafiya karfin tattalin arziki na duniya a shekara mai zuwa a Florida.
Ramaphosa ya ce abin takaici ne yadda Trump ke ci gaba da daukar matakai bisa labaran da ba na gaskiya ba ko kuma aka yi musu kwaskwarima.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ba zai gayyaci Afirka ta kudu taron na badi ba, da Amurka zata karbi bakunci, kuma ya nanata sukar da yake yi wa Afirka ta kudun, kan zargin cewa an aikata kisan kiyashi a Afirka ta Kudu a kan tsirarun fararen fata.
Amurka ta kauracewa taron na G20 na bana a Johannesburg, inda shugabanni suka amince da matakan da aka ayyana na magance matsalar dumamar yanayi da sauran matsaloli na duniya, duk da kin yardar Amurka.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka ECOWAS ta yi Allah wadai da juyin mulki a Guinea Bissau November 27, 2025 Faransa, Jamus, Italiya, da Burtaniya sun yi tir da “karuwar rikici” a yammacin kogon jodan November 27, 2025 Rasha A Shirye Take Ta Taimaka Wa Najeriya A Fada Da Ta’addanci November 27, 2025 Palasdinawa Sun Karbi Gawawwakin Shahidai 15 Daga ‘Yan Mamaya November 27, 2025 Makaman Iran Masu Linzami Ne Kandagarkon Dake Takawa Makiya Birki November 27, 2025 Najeriya: Allah Ya Yi Wa Babban Malamin Addini Shehu Dahiru Bauchi Rasuwa November 27, 2025 An Zabi Iran A Cikin Majalisar Zartarwa Ta Hukumar Yaki Da Makamai Masu Guba Ta Duniya CWC November 27, 2025 HKI Tana Amfani Da Tsagaita Wuta A Gaza Don Sake Shata Kan Iyakokin Yankin November 27, 2025 Yawan Falasdinawa Da Suka Yi Shahada Na Karuwa Saboka Keta Yarjeniyar Tsagaita Wuta November 27, 2025 An Rutsa Da Tsohon shugaban Kasar Najeriya A Guine Bissau Bayan Juyin Mulki November 27, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci