’Yan Boko Haram sun kashe mutum 9, skun Jikkata 4 a Borno
Published: 7th, July 2025 GMT
An kashe mutane tara tare da jikkata wasu huɗu a wani da mayakan Boko Haram suka kai yankin a Malam Fatori da ke Jihar Borno.
Gwamna Babagana Zulum, wanda baya kasar a halin yanzu, ya tura tawaga ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Ƙananan Hukumomi, Sugun Mai Mele, domin jajanta wa waɗanda abin ya shafa da kuma tantance halin da ake ciki.
Mai Mele ya jaddada aniyar Gwamna Zulum na jajircewa wajen tabbatar da tsaron Malam Fatori saboda muhimmancinsa.
Ya sanar da shirin tura manyan injina domin tona ramuka a kusa da hedikwatar ƙaramar hukumar don hana hare-hare nan gaba daga Boko Haram da ISWAP.
Turji: Sai ka sako mutanen da ka sace za a yi sulhu — Gwamnatin Sakkwato Sarkin Ibadan ya rasu yayin da ake shirin bikin cikarsa shekara guda a mulkiHaka nan kuma ya gargaɗi mazauna yankin kan haɗin gwiwa da ’yan tawaye, inda ya yi barazanar “sakamakon Ubangiji” ga duk masu haɗin gwiwa.
An bayar da tallafin kuɗi, inda aka bai wa duk gidan da suka asa yan uwa ₦500,000, yayin da waɗanda suka jikkata huɗu kowannensu ya samu ₦250,000.
A halin yanzu, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Tsaro na Cikin Gida, Usman Tar, ya sanar da shirin sake tsugunar da ƙarin iyalai 3,000 da suka rasa matsugunansu a Malam Fatori, wanda hakan zai kai ga jimlar gidaje 5,000 da aka sake tsugunar da su.
Tar ya tabbatar wa mazauna yankin ci gaba da ƙoƙarin gwamnati na samar da matakan tsaro da kayan aiki don dawwamammen dawowar su, yana mai kira gare su da su ci gaba da kasancewa a faɗake tare da kai rahoton duk wani abu da ba a aminta da shi ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Boko Haram
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin Mamayar Isra’ila Suna Ci Gaba Da Kashe Masu Neman Karbar Kayan Agaji A Gaza
Sojojin mamayar Isra’ila sun mayar da cibiyoyin bada agaji zuwa filin yakin kashe Falasdinawa a Zirin Gaza
Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da mayar da cibiyoyin bayar da agajin jin kai zuwa wani mummunan tarko na aiwatar da kisan kiyashi kan Falasdinawa, wanda hare-haren baya-bayan nan da suka kai kan fararen hula sunka yi sanadiyar hasarar rayuka da dama tare da jikkata wasu masu yawa. Wannan mummunan al’amari ya janyo gargadin Majalisar Dinkin Duniya cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana kai wa masu fama da yunwa hari.
Jiragen yakin gwamnatin mamayar Isra’ila da kuma amfaniu da manyan bindigogi suna barin wuta kan mai uwa da wabi kan Falasdinawa da suka taru domin karbar kayan jin kai. Gwamnatin mamayar Isra’ila ta bullo da wannan sabon hanya ce domin kashe Falasdinawa a matsayin tarko ga Falasdinawa, kuma ba ta sha yin ci gaba da wannan ta’asa domin babu mai iya hana ta ko tofin yin Allah wadai da ita.
Wani magidanci da ya dawo daga karbar agaji da ‘ya’yansa biyu a Khan Yunus, ya fuskanci bude wuta inda dansa guda ya yi shahada dayan kuma yana nan rai kwai-kwai mutum kwai-kwai.
A cewar wata sanarwa da ma’aikatar harkokin cikin gida da tsaron kasa a zirin Gaza ta fitar, ta jaddada cewa: Daruruwan Falasdinawa ne suka yi shahada sakamakon harsashin sojojin mamayar Isra’ila a wuraren bada agajin jin kai zuwa yanzu.