Za a gudanar da taron kiwon lafiya na farko a Gombe
Published: 24th, September 2025 GMT
An kammala shirin gudanar da taron lafiya karo na farko a tarihin Jihar Gombe, wanda za a fara a ranar 2 ga Oktoba.
Da yake zantawa da manema labarai wannan Larabar a Gombe, Kwamishinan Lafiya, Dakta Habu Dahiru, ya bayyana cewa, za a gudanar da taron na tsawon kwanaki biyu domin tattauna matsalolin bangaren lafiya da zummar samo mafita.
Ya ce, taron zai samu halartar manyan baki ciki har da Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Remi Tinubu; Mataimakiyar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Hajiya Amina Mohammed; Ministan Lafiya, Farfesa Ali Pate; tare da wasu abokan hulda, ‘yan majalisar tarayya, masana harkar lafiya, kungiyoyin farar hula da kuma kafafen yaɗa labarai.
Dakta Dahiru ya ƙara da cewa, a yayin taron, gwamnati za ta ƙaddamar da cibiyar kiran gaggawa ta lafiya da kuma tura motocin daukar marasa lafiya (ambulance), domin ba da agaji cikin gaggawa a dukkan sassan jihar.
A cewarsa, wannan sabon tsarin zai bai wa jama’a damar kiran hukumomin lafiya cikin sauri domin daukar marasa lafiya zuwa asibiti ba tare da bata lokaci ba.
“Wannan shiri zai sauya tsarin ba da agajin gaggawa a Gombe, kuma taron alama ce ta sabon babi a yunƙurin gwamnati na inganta harkokin lafiya a jihar,” in ji shi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Farfesa Ali Pate jihar Gombe Kiwon Lafiya
এছাড়াও পড়ুন:
Kwalara ta kashe mutum 10 a Ƙaramar Hukumar Adamawa
Kwamishinan lafiya na Jihar Adamawa, Dokta Felix Tangwami ya bayyana cewa, cutar kwalara a Ƙaramar hukumar Mubi ta yi sanadin mutuwar mutane 10, inda ya buƙaci mazauna yankin da su kula da tsaftar jikinsu.
Da yake yi wa Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) bayani a Yola ranar Laraba, Tangwami ya ce marasa lafiyan sun mutu ne a gida maimakon a cibiyoyin lafiya.
Majalisar Dokokin Amurka na neman a hukunta ’yan kungiyar Miyetti-Allah An kashe babban limami a Kwara saboda zargin maitaYa ƙara da cewa, gwamnatin jihar tare da haɗin gwiwar hukumar lafiya ta duniya (WHO) sun ɗauki matakin gaggawa don daƙile ɓarkewar cutar.
“Tun daga farko, mun ɗauki matakin gaggawa a kan lamarin, kasancewar mu a can, kuma ba za a iya musanta hakan ba,” in ji shi.
Kwamishinan ya ƙara da cewa, waɗanda suka ziyarci cibiyoyin kiwon lafiya sun samu kulawa, inda aka kwantar da majinyata 25 a ranar Talata 4 ga watan Nuwamba, yayin da wasu da dama kuma an sallame su tare da wayar da su kan harkokin tsafta.
Ya bayyana cewa, an tura jami’an kula da cututtuka na jihar, da Daraktan kula da cututtuka a Hukumar kula da kiwon lafiya a matakin farko, da masu aikin sa-kai zuwa Mubi domin gudanar da ayyuka da kuma wayar da kan jama’a.
Sun kuma gano waɗanda abin ya shafa a cikin unguwanni don tabbatar da sun samu kulawar lafiya.
Tangwami ya kuma yi kira ga shugabannin gargajiya da su goyi bayan ƙoƙarin gwamnati ta hanyar ƙarfafa gwiwar mazauna yankin da su gaggauta neman magani a cibiyoyin lafiya.