Sojoji Da Masu Gadin Gandun Daji Zasu Murkushe Masu Aikata Laifuka A Kwara
Published: 7th, July 2025 GMT
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya ce an samar da isassun matakan tsaro domin kawar da wasu gungun miyagu da ke aikata munanan laifuka a jihar.
AbdulRazaq ya bayyana hakan ne yayin da ya bayyana wa masu ruwa da tsaki daga yankin Lafiagi na jihar Kwara ta Arewa kan dimbin kokarin gwamnatin jihar a wani taro da aka gudanar a Ilorin.
Gwamnan ya amince da damuwar al’ummar tare da tabbatar musu da matakin da gwamnati ke jagoranta kan lamarin.
Ya ce sojojin Najeriya za su ci gaba da kai hare-hare a dazuzzukan da aka gano a matsayin sansanin ‘yan ta’adda a Kwara ta Arewa da Kudu.
Gwamna AbdulRazaq ya ce ayyukan za su hada da sabbin jami’an tsaron dazuzzukan da aka horas da su a wuraren da aka kebe.
Ya kara da cewa, ayyukan za su fatattaki ‘yan ta’addan daga maboyarsu tare da dawo da kwanciyar hankali a yankunan da abin ya shafa, ya kuma kara da cewa za a yi taka-tsan-tsan don hana ’yan ta’adda yin katsalandan a wasu wurare.
Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin jihar na hada hannu da ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro domin kawar da barazanar da ake fuskanta a sassan jihar, musamman ma kauyukan da aka gano a kananan hukumomin Ifelodun, Edu da Patigi.
COV/ALI MUHAMMAD RABIU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Gangamin Wayar Da Kai Kan Laifuka A Intanet
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Hukumar Kwastam Ta Tara Naira Biliyan ₦658.6 A Watan Satumba — DG Na NOA October 13, 2025
Labarai Zargin Batanci: An Sasanta Da Malam Lawal Triumph Da Majalisar Shura Ta Kano October 13, 2025
Manyan Labarai Rundunar Ƴansanda Ta Kama Gaggan Ƴan Fashi 9 A Kano October 13, 2025