An harbe ’yan sanda 3 har lahira a Kogi
Published: 10th, September 2025 GMT
Wasu mahara sun harbe jami’an ’yan sanda uku har lahira da safiyar ranar Laraba a wata madakatar mota da ke garin Egbe, a Ƙaramar Hukumar Yagba Yamma a Jihar Kogi.
Kakakin rundunar jihar, SP William Aya, ne ya tabbatar da harin.
Babban layin wutar lantarki ya sake faɗuwa Injin niƙa ya yi ajalin matar aure mai ’ya’ya 6 a GombeYa ce harin ya faru ne a kan iyakar Jihar Kogi da Jihar Kwara.
SP Aya, ya ƙara da cewa, Kwamishinan ’yan sandan jihar, Miller Dantawaye, ya tura tawaga ta musamman domin bincika yankin domin kama waɗanda suka kai harin.
“Ina tabbatar muku cewa ’yan sandanmu uku sun mutu a Egbe yau.
Kwamishina ya tura tawaga ta musamman, kuma muna bibiyar waɗanda suka kai harin. Za a kama su duka,” in ji Aya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda hari mahara
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yansanda Sun Ceto Mutum Ɗaya, Sun Kama Mace Da Zargin Garkuwa Da Mutane A Dajin Kwara
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Tinubu Ya Yi Wa Shugabannin Tsaro Ado Da Sabbin Muƙamai October 30, 2025
Manyan Labarai Sheikh Gumi Ya Yabi Tinubu Kan Afuwar Da Ya Yi Wa Maryam Sanda October 30, 2025
Manyan Labarai Yadda Ta Gudana A Taron Karɓar Ƴan Majalisa Shida Da Suka Koma APC October 30, 2025