Kungiyoyin Gwagwarmayar Falasdinawa Sun Yi Allah Wadai Da Harin Mamayar Isra’ila Kan Kasar Yemen
Published: 7th, July 2025 GMT
Kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa sun yi Allah wadai da hare-haren zaluncin da yahudawan sahayoniyya suka kai kan kasar Yemen
Kungiyar Jihadin-Islami ta Falasdinawa da sauran kungiyoyin gwagwarmayar Musulunci na Falasdinu sun yi Allah wadai da hare-haren wuce gona da irin da yahudawan sahayoniyya suka kai kan tashar jirgin Ruwan Hodeida na kasar Yemen, tare da jaddada goyon bayansu ga shugabancin kasar da sojojin kasar da kuma al’ummar kasar ta Yemen.
Kungiyar fafutukar ‘yantar da Falasdinu ta fitar da wata sanarwa inda ta tabbatar da cewa: “Kazamin harin wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya suka kai kan kasar Yamen, wanda ya shafi kayayyakin more rayuwa na fararen hula da tashoshin wutar lantarki da tashar jiragen ruwa na Hodeidah da Ras Issa da kuma Salif, wani sabon laifi ne na ha’inci da ya kara yawan muggan laifukan ‘yan mamaya a yanki.”
Sanarwar ta kara da cewa: Wannan mummunan wuce gona da iri na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Yemen da dakarunta ke samun nasarori a jere wajen karya martabar makiya ‘yan sahayoniyya da kutsawa cikin zurfin dabarun na yaki da kuma kafa madaidaicin matakin da ya dace wanda ke nuna ‘yancin kai na mutanen da ba su san yadda za su ja da baya ba.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Yemen
এছাড়াও পড়ুন:
Ayatullahi Khatami Ya Ce Hukuncin Da Ya Cancanci Trump Da Netanyahu Shi Ne Kisa Saboda Zubar Da Jinin Bil’Adama
Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehra mya bayyana cewa: Hukuncin shari’a da ya hau kan Trumpm da Netanyahu shi ne kisa
Limamin da ya jagoranci sallar juma’a a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran a yau ya bayyana cewa: Amurka da karen da suka horar sun yi barazana ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kuma wannan wauta ce. Hakika dokar Musulunci ta Trump da Netanyahu ita ce mutuwa. Sun kashe mutane fiye da 55,000 a Gaza. Su suka kai Qasim Sulaimani da yin shahada da sauran abokansa. Su ne masu aiwatar da kisan kai da ayyukan fasadi a duniya. Sun yi wa Jagoran juyin juya halin Musulunci da al’ummar Iran barazana. Abin farin cikin shi ne, dukkanin hukumomin addini na birnin Qum da Najaf sun tashi tsaye tare da yin Allah wadai da wannan gurbatacciyar tunani. Sannan a baya-bayan nan Ayatullah Nasir Makarem Shirazi da Ayatullahi Nuri sun yi tofin Allah tsine kan wannan barazana da bayyana hakan a matsayin shelanta yaki.
Hujjatul-Islam Ahmad Khatami a cikin hudubar sallar juma’ar a birnin Tehran, yayin da yake ishara da harin da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta kai harin wuce gona da iri kan kasar Iran ya ce: martani da dakarun Iran suka mayar kan gwamnatin yahudawan sahayoniyya abu ne da ke gwada karfinsu na mayar da martini kan dukj wani mai girman kai da dagawa.
AYatullahi Hatami ya kara da cewa: Son kasa da kare Musulunci so ne ga Allah. Kuma kishin kasa wani bangare ne na Imani, don haka ya karfafa al’umma kan Shirin kare kasarsu da kimar daular Musulunci daga duk wani dan mamaya mai kiyayyaya da kyawawan dabi’un addini.