Hasashen Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Kaduna Ta Ƙaddamar Da Shirin Ko-ta-kwana
Published: 12th, September 2025 GMT
“Gwamnatin Jihar Kaduna ta shirya tsaf domin ɗaukar matakin gaggawa kan kowanne yanayi da ka iya tasowa sakamakon wannan hasashen yanayi. An umurci KADSEMA da ta yi aiki tare da dukkan hukumomi masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cikakken shiri. Ana roƙon jama’a da su bi dukkan umarnin kariya, su share magudanan ruwa, kuma su guji wuraren da ambaliya ke yawan faruwa a wannan lokaci,” in ji Maiyaki.
Hakazalika, sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (KADSEMA), Dakta Usman Hayatu Mazadu, ya jaddada muhimmancin kasancewa cikin shiri da kuma bin matakan kariya da ke cikin sanarwar.
“Hasashen yanayi ya nuna cewa za a samu guguwar iska da ruwan sama mai yawa musamman a ranakun Laraba da Alhamis. Muna roƙon jama’a da su guji fita ba dole ba yayin ruwan sama mai ƙarfi, su daina ƙoƙarin tuƙi cikin hanyoyin da ruwa ya mamaye, sannan su nisantar da yara daga guraren da ruwa ke taruwa. Manoma kuma su gaggauta ɗaukar matakan kare amfanin gona da wuraren ajiya,” in ji Dakta Mazadu.
“Mun tura tawagar gaggawa zuwa shiyyoyi daban-daban, kuma ana ƙarfafa gwiwar jama’a da su rika hanzarta bayar da rahoton duk wani lamari na ambaliya ko wata gaggawa da ke barazana ga rayuka ta hanyar amfani da layukan gaggawa na hukuma na KADSEMA,” in ji shi.
Gwamnatin ta kuma yi kira ga jama’a da su kasance cikin natsuwa amma a kasance cikin shiri, tana mai jaddada bukatar haɗin kan al’umma wajen rage haɗurran da ke tattare da yanayin da ake sa ran zai faru.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Dan Majalisar Jema’a/Sanga, Daniel Amos, Ya Koma Jam’iyyar APC
Harkokin siyasa na Kudancin Kaduna ya dauki wani salo yayin da dan majalisar da ke wakiltar mazabar Jema’a/Sanga a majalisar tarayya, Hon. Dan Amos, ya sanar da komawarsa jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar PDP, yana mai cewa ya dauki wannan mataki ne domin ya hada kai da gwamnatocin jiha da na tarayya don cigaban yankin.
Yayin da yake jawabi ga manema labarai a Kafanchan kafin karbar sa a hukumance tare da Sanata Marshall Katung, Amos ya bayyana cewa wannan mataki ya biyo bayan dogon shawarwari da aka yi da shugabannin al’umma, kungiyoyin addini, kwararru da kuma sarakunan gargajiya a fadin mazabarsa.
Ya ce jam’iyyar PDP, wacce a da take da karfi sosai a Kaduna, ta ragu saboda rikice-rikicen cikin gida da suka dade suna faruwa, wanda hakan ya janyo ficewar mambobi da kuma rasa goyon bayan talakawa a fadin kasa.
“Mun dauki lokaci muna tattaunawa da mutane a matakai daban-daban – daga tsarin jam’iyya zuwa kungiyoyin addini da na kwararru – kuma abin da muka cimma shine, don amfanin jama’armu, ya dace mu nemi wata madogara ta daban,”
“Ya zama sauki mu shiga APC saboda muna ganin irin kokarin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Uba Sani ke yi wajen hada yankin Kudancin Kaduna cikin shirin cigaba da ci gaba da kasa.” in ji Amos.
Dan majalisar ya yaba wa Shugaba Tinubu bisa nadin ɗan asalin yankin, Janar Christopher Musa, a matsayin Babban Hafsan Tsaro (CDS) da kuma amincewa da a kafa Jami’ar Kimiyyar Aiki ta Tarayya da Asibitin Tarayya (Federal Medical Centre) a yankin.
Ya kuma gode wa Gwamna Uba Sani saboda gudanar da mulki cikin hadin kai, gina ababen more rayuwa, da bude kofa ga kowa, wanda ya ce ya karfafa zumunci da bai wa kowane bangare na jihar damar shiga.
“Shugaban kasa da gwamna suna nuna shugabanci na hada kan jama’a. Wannan ya sa muka ga dacewar mu hade da su domin mu samu karin cigaba a yankinmu,” in ji Amos.
Amos ya karyata jita-jitar cewa ya koma APC don son kai ko muradin siyasa, yana mai cewa wannan mataki ne na Allah da kuma na amfanin jama’ar Kudancin Kaduna.
“Ba don bukatar kaina ba ne, amma don mu tabbatar da yankinmu ya ci gajiyar dimokuradiyya. Ina da yakinin cewa tarihi zai tuna da mu bisa wannan mataki na jarumta da muka dauka,” ya kara da cewa.
Dan majalisar, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Ayyukan Majalisa, ya tabbatar wa mazaunar mazabarsa cewa komawarsa APC ba za ta canza manufarsa ta kyakkyawan wakilci ba, yana mai cewa ya shiga jam’iyyar mai mulki ne don kara daraja, ba don kawo rarrabuwar kawuna ba.
Ya bayyana fatan cewa da hadin kai tsakanin jama’a da gwamnati, Kudancin Kaduna zai ci gaba da samun cigaba a bangaren ababen more rayuwa, ilimi, da tsaro.
An shirya taron karbar Amos, Sanata Katung, da sauran wadanda suka koma daga PDP zuwa APC a ranar 1 ga Nuwamba a Kafanchan, kuma manyan baki da ake sa ran halarta sun hada da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, da kuma shugabannin jam’iyyar APC daga fadin kasar nan.
Radio Nigeria ta ruwaito cewa wannan sauyin jam’iyya ya nuna babban sauyi a siyasar jihar Kaduna, wanda ya kawo karshen rinjayen PDP da ta yi sama da shekaru 25 a Kudancin jihar.
Daniel Karlmax