Ko za ka fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinka?

An haife ni a unguwar Tudun Nufawa dake Kano Municipal, na yi karatun firamare a jakara ‘Special Pramary School’, na yi sakandare a Gwammmaja 2. Sannan babban Sakandare a ‘GSS Dala’. Na yi karatun ‘Diploma’ a fannin ‘computer’, sannan na yi ‘National Diploma’ akan lafiyar hakori ‘Dental Surgery Technician’.

 

Ya batun iyali, shin akwai ko babu?

Ina da Aure, mata ta daya da ‘ya’ya biyar biyu maza uku mata.

 

Wane rawa ka ke takawa a cikin masana’antar Kannywood?

Na farko zan iya cewa ni ‘film maker’ ne, amma nafi karfi a ‘directing’. Sannan ina ‘Camera’ ina rubutu, Ina ‘acting’, Ina ‘Editing’.

 

Me ya ja hankalinka har ka tsunduma cikin masana’antar Kannywood?

Tun daga kallon indiya ‘da’ da ake yi Asabar da Lahadi, sannan na kasance ina san kallon irin fina-finan ‘cartoon’ a lokacin muna makarantar sakandare a shekarun baya wajan 1996, mai suna Bakandamiyar Rikicin Duniya’. Ana yin wasu fim din hausa wadanda suka fara jan hankalina wajan tunanin ina da abin da zan iya a harkar fim. Akwai wani yayana wanda muke yin komai tare mai suna Hassan Mijinyawa, muka yi shawara akan yadda za mu kirkiri wani fim da za mu yi. Muna cikin shirye-shirye mu akwai wani daya daga cikin dan’uwan mu ya yi karatun da ya shafi fim, aikin jarida yana ba mu karfin gwiwa sai Allah ya karbe shi wato ya rasu a shekara 1998 mai suna Yusif Mijinyawa. Sai muka yi shiru zuwa wani lokaci, kafin 2000 muka dawo da karfin mu inda muka fara yin aikin fim ka’in da na’in.

 

Za ka yi kamar shekara nawa da fara harkar fim?

A kallla shekara ashirin da biyar.

 

Ya gwagwarmayar farawar ta kasance?

Maganar kantawaye ni dai ban santa ba, dan ba a yi min ba.

 

Ya batun iyaye lokacin da za ka sanar musu kana sha’awar shiga harkar fim, ko akwai wani kalubale da ka fuskanta daga gare su?

Gaskiya ni dai ban samu wata matsala ba sai dai kawai nasihohi da kuma lallai mutun ya kula da kansa da addini sa kada kayi wani abu da zai keta ma mutumci sun bani goyan baya dari bisa dari.

 

Mu dan koma baya kadan, cikin abubuwan da ka lissafo wanda kake taka rawa cikin masana’antar, da wane bangare ka fara?

Daraktin, kuma har yanzu shi ne wanda na fi so.

 

Kafin ka fara daraktin, shin ka koya ne a wajen wani, ko kuwa ka shiga masana’antar ne da iyawarka?

E, gaskiya farkon shiga ta ganin yadda ake yi nayi na fara, amma daga baya na je sani online da ‘workshop’ da wasu karatuttuka da suka shafi harkar fim.

 

Ya farkon fara daraktin dinka ya kasance?

E, gaskiya ban sami wani kalubale ba, saboda wadanda na fara aiki da su sun bani hadin kai, sosai duk da cewa duk inda ka fara dole akwai ‘yan masaloli da na fuskanta wajan rashin sabo. Ace ni ne nake daraktin wasu manyan jarumai akwai abinda ya taimakamin a lokacin na dau kwararrun ma’aikata.

 

A wane fim ka fara daraktin, kuma ya karbuwar fim din ya kasance, ga masu kallo?

Akwai wani fim na kamfani na mai suna ALLURA shi ne na fara daraktin, kuma a lokacin ya samu karuwa domin muna siyar da ‘right’ na CD tun daga siyarwa masu buga wannan CD aka maida kudi aka ci riba, ya karbu sosai a wajan mutane.

 

Wane abu ne ya fi baka wahala a bangaren daraktin?

To abinda yake bani wahala ko kuma haushi shene jarumina yaki yin abinda aka sashi wannan yana sani inji aikin ya fita daga raina

Za mu cigaba mako me zuwa.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Kannywood fara daraktin masana antar

এছাড়াও পড়ুন:

Hukumar Hisbah Ta Kama Wasu Matasa Da Suka Yi Aure Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Kano

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wasu ma’aurata da wasu mutane biyar bisa zarginsu da gudanar da ɗaurin aure ba tare da izinin iyayensu ba ko kuma bin tsarin addinin Musulunci a unguwar Nasarawa da ke cikin birnin Kano. Wadanda ake zargin sun hada da ango mai suna Aminu mai shekaru 23 da amaryarsa Sadiya mai shekaru 22. Sauran wadanda aka kama su ne Umar mai shekaru 24 wanda ya kasance wakilin ango; Abubakar, mai shekaru 23, wanda ya kasance waliyyin amarya; Usaina, mai shekaru 21; da kuma wasu ‘yan mata guda biyu wadanda suka kasance shaidu a yayin ɗaurin auren. Ahmed Musa Ya Nemi Afuwar Ƙungiyar 3SC Akan Abinda Ya Faru Da ‘Yan Wasansu A Kano Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 236 A Jihohi 27 Da Birnin Tarayya Rahotanni sun bayyana cewa, an ɗaura auren ne akan sadaki Naira 10,000, ba tare da amincewar iyayen ma’auratan ba. Da yake tabbatar da faruwar lamarin, mataimakin babban kwamandan hukumar ta Hisbah, Dr. Mujaheeddeen Aminuddeen, ya ce an kama wadanda ake zargin ne biyo bayan korafe-korafen da ‘yan unguwar suka kai wa hukumar. Ya bayyana cewa, matakin da wadanda ake zargin suka ɗauka ya saɓawa koyarwar addinin Musulunci da kuma dokokin aure na jihar, yana mai jaddada cewa, hukumar ta Hisbah ba za ta amince da duk wani abu da ya saɓawa tsarin addini da na shari’a a jihar Kano ba. Dr. Aminudeen ya kara da cewa, a halin yanzu wadanda aka kama suna hannun Hisbah domin ci gaba da bincike. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Ra'ayi Riga Labarin Xinjiang A Zane: Aikin Yawon Shakatawa Na Kara Samar Da Arziki Ga Al’ummar Xinjiang October 13, 2025 Labarai Ba Gudu Ba Ja-da-baya Kan Ci Gaba Da Kwaskwarima Ga Tsarin Haƙar Ma’adanai – Minista October 13, 2025 Manyan Labarai Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 236 A Jihohi 27 Da Birnin Tarayya October 13, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ba Bu Dalilin Da ASUU Za Ta Fara Yajin Aiki, An Biya Duk Buƙatunsu – Ministan Ilimi 
  • Zaben Kamaru: Issa Tchiroma Bakary ya lashe yankunan da Biya ke da rinjaye
  • Hukumar Hisbah Ta Kama Wasu Matasa Da Suka Yi Aure Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Kano
  • Zuwa Kofin Duniya: Za A Yi Ta Ta Kare A Nahiyar Afirka
  • ASUU za ta fara yajin aikin mako 2 daga ranar Litinin
  • Neman Kudi Ne Ya Kawo Ni Masana’antar Kannywood Ba Fadakarwa Ba – Khadija Muhammad 
  • Me Ya Sa Jaruman Masana’antar Kannywood Ke Auren Sirri?
  • Tarihin Hassan Usman Katsina (1)
  • Wasu Daga Cikin Muhimman Alamomin Ciwon Kansa
  • Falasdinawa Daga Kudancin Gaza Sun Fara Komawa Gidajensu Da Aka  Rusa A Arewacin Yankin