Li Qiang Ya Gana Da Tawagar Membobin Majalisar Wakilai Ta Amurka
Published: 22nd, September 2025 GMT
A yau Lahadi 21 ga wannan wata da yamma, firaministan kasar Sin Li Qiang ya gana da tawagar membobin majalisar wakilai ta kasar Amurka da Adam Smith ya jagoranta a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing.
A yayin ganawar, Li Qiang ya bayyana cewa, Sin da Amurka manyan kasashe ne dake da muhimmanci sosai a duniya, kiyaye dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka mai dorewa yadda ya kamata ya dace da moriyar kasashen biyu da begen kasa da kasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Dattawa ta dakatar da tantance sabon Ministan Tinubu
Majalisar Dattawa ta dakatar da aikin tantance Dokta Kingsley Tochukwu Udeh, SAN, wanda Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa domin zama minista, sakamakon rashin gabatar mata da rahoton jami’an tsaro a kansa.
Shugaban Majalisar Dattawan, Godswill Akpabio, ne ya bayyana haka yayin zaman majalisar na ranar Laraba, inda ya ce ba za su ci gaba da tantancewar ba sai an samu cikakken rahoto daga hukumomin tsaro.
Zan ci gaba da siyasa har ƙarshen rayuwata – Shekarau Abba ya yaba wa sojoji kan hallaka ’yan bindiga 19 a KanoA ranar Talata ce Shugaba Bola Tinubu ya aike wa majalisar sunan Mista Udeh, ɗan asalin Jihar Enugu cikin wata wasiƙar neman sahalewarta.
“Ina farin cikin miƙa sunan Dokta Kingsley Tochukwu Ude, SAN, domin tabbatar da shi a matsayin minista. Ina fatan majalisar za ta yi la’akari da wannan buƙata cikin gaggawa kamar yadda aka saba,” in ji wasiƙar shugaban ƙasan.
Tinubu ya naɗa Udeh ne bayan murabus ɗin da tsohon Ministan Kimiyya, Uche Nnaji ya yi, bayan zargin da aka yi masa na gabatar da takardar shaidar kammala karatu ta bogi, wanda kuma shi ne minista ɗaya kacal daga Jihar ta Enugu
Mista Udeh wanda yanzu haka shi ne Antoni-Janar kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Enugu, ya shahara da ƙwarewa a fannin doka da kare haƙƙin ɗan Adam.