Ko Ƙasashen Musulmi Za Su Iya Kafa Ƙawancen Tsaro Don Tunkarar Abokan Gaba?
Published: 21st, September 2025 GMT
A ɓangare ɗaya kuma Turkiyya na ƙara nuna damuwa bayan harin da Isra’ila ta kai a birnin Doha.
Mai magana da yawun ma’aikatar tsaro ta Turkiyya, Rear Admiral Zeki Akturk ya yi gargaɗin cewa “Isra’ila za ta iya faɗaɗa hare-harenta baya ga Ƙatar. Za ta iya ingiza yankin baki ɗaya cikin bala’i.”
Mece ce shawarar da Masar ta bayar?
Shawarar da Masar ta bayar ya ƙunshi samar da tsarin haɗe ayyukan sojin ƙasa da na sama da cibiyoyin tsaro, tare da haɗe cibiyoyin horaswa da ayyukan soji.
Haka nan kuma ƙasashen ne za su yanke hukunci kafin amfani da dakarun bayan tattaunawa a tsakaninsu.
Kafar yaɗa labarai ta Al Akhbar da ke Lebanon ta ce a ƙarƙashin tsarin, Masar ta ce za ta samar da dakaru 20,000, sannan Saudiyya za ta zamo ta biyu mafi bayar da gudumawa.
Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi ya tattauna da ƙasashe da dama a kan wannan batu, kuma akwai yiwuwar harin da Isra’ila ta kai a Doha zai iya farfaɗo da maganar.
An taɓa samun irin wannan ƙawance a lokuta daban-daban tsakanin ƙasashen yankin, kamar a lokacin yaƙin yankin Gulf da kuma yaƙe-yaƙen da aka yi a Isra’ila.
An taɓa ƙulla irin wannan ƙawancen tsaro a baya tsakanin ƙasashen Larabawa da na Musulmi wadda ake kira ‘Central Treaty Organisation’, wadda aka yi wa laƙabi da Yarjejeniyar Baghdad. Yarjejeniyar ta yi aiki daga shekara ta 1955 zuwa 1979.
Ƙasashen Larabawa sun yi mummunar suka kan harin da Isra’ila ta kai a Ƙatar
Firaiministan Iraƙi Mohammed Shia al-Sudani ya kuma yi kira da a samu ‘ƙawancen soji na ƙasashen Musulmai’.
Kafar yaɗa labarai ta Turkiyya, TRT World, ta ambato shi na cewa akwai buƙatar ɗaukar mataki na bai-ɗaya kan abubuwan da Isra’ila ta aikata a Gaza da kuma Ƙatar a baya-bayan nan.
Al-Sudani ya ce harin da Isra’ila ta kai a Doha, wanda ya kashe mambobin Hamas biyar da wani babban jami’in tsaron Ƙatar “taka dokokin duniya ne mai matuƙar mamaki” kuma tunatarwa ce kan cewa abubuwan da Isra’ila ke aikatawa barazana ce ga tsaron ɗaukacin yankin.
”Babu wani dalili da zai hana ƙasashen Musulmai haɗa kai domin samar da ƙawancen soji guda ɗaya domin kare kansu,” kamar yadda ya shaida wa tashar talabijin ta Al Jazeera, inda ya buƙaci ƙasashen Larabawa da na Musulmai su samar da haɗaka ta siyasa da tsaro da kuma tattalin arziki.
Ya kamata a hukunta Isra’ila – in ji Ƙatar
“Lokaci ya yi da duniya za ta kawo ƙarshen baki biyu da ake yi sannan a hukunta Isra’ila kan laifukan da ta tafka,” in ji ministan harkokin waje na Ƙatar, gabanin taron da ƙasashen suka yi a ranar Litinin, kamar yadda sashen BBC Persia ya ruwaito.
Ya ce “Ya kamata Isra’ila ta sani cewa wannan yaƙi da take da ƴ an’uwanmu, Falasɗinawa, da nufin korar su daga ƙasarsu, ba zai yi nasara ba.”
Ƙatar ta yi martani da kakkausan harshe bayan harin da Isra’ila ta kai mata ranar 9 ga watan Satumba, kuma ta jaddada cewa yanzu a shirye take kan ko ma mene ne zai faru.
Ɗaya daga cikin manyan jami’an Hamas, Bassem Naim, ya ce ƙungiyar na fatan cewa za a samu “wani ƙwaƙƙwaran mataki na bai-ɗaya daga ƙasashen Larabawa da na Musulmai” kan Isra’ila.
Amurka na da sansanin sojin samanta mafi girma a faɗin Gabas ta tsakiya ne a Ƙatar. Baya ga haka, Ƙatar ta taka muhimmiyar rawa wajen tattaunawar sulhu tsakanin Amurka da Masar da kuma Isra’ila da Hamas.
Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio wanda ya kai ziyara Isra’ila, ya nuna fushinsa kan harin da Isra’ila ta kai a Ƙatar, sai dai ya bayyana cewa wannan ba zai lalata kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin Amurka da Isra’ila ba.
Dama dai akwai ruɗani kan abin da mai magana da yawun fadar shugaban Amurka ta White House, Caroline Leɓitt ta ce game da bayanin da aka yi wa Ƙatar kan harin. Fadar White House ta ce ‘an sanar da Ƙatar kafin kai harin’, sai dai Firaiminstan Ƙatar ya ce ya ‘samu bayanin ne minti 10 bayan kai harin’.
Shin abu ne mai yiwuwa ƙasashen Larabawa su kafa ƙawance kamar NATO?
Batun kafa ƙawancen soji tsakanin ƙasashen Larabawa, mai kama da ƙawancen NATO, abu ne da ya daɗe, sai dai masana ba su da ƙwarin gwiwar cewa abu ne da zai yiwu.
Premanand Mishra, malami a cibiyar zaman lafiya da warware rikice-rikice ta Nelson Mandela a jami’ar Jamia Millia Islamia da ke Indiya, ya ce “An taɓa tattaunawa kan kafa ƙungiyar NATOn Larabawa, kuma Saudiyya ta bai wa batun muhimmanci sosai. Har ma an taɓa naɗa tsohon babban hafsan soji na Pakistan, Raheel Sharif a matsayin shugabanta, to amma sai batun ya gaza ci gaba.”
Ya ce “Muradun tsaro na dukkanin ƙasashen sun sha bamban ta yadda zai yi wahala a samu matsaya ɗaya a tsakaninsu.
Misali, Saudiyya da Iran za su iya watsi da bambance-bambancen da ke tsakaninsu? Domin idan har za a yi haɗakar soji, to akwai buƙatar yin musayar bayanan sirri.”
Duk da cewa akwai ƙoƙarin da aka yi a baya-bayan man na sulhuntawa tsakanin Saudiyya da Iran, babu tabbas kan ko an cimma wata matsaya mai ƙwari da za ta ita samar da ƙawance tsakanin ƙasashen yankin.
Premanand Mishra ya ce wannan shawara ta ƙawancen soji ta samo asali ne daga Masar, abin da ya rage shi ne a ga ko akwai ƙwaƙwarar aniyar aiwatarwa. Sannan kuma ko ƙasashen Yamma, musamman Amurka da ƙawancenta na NATO za su bari a aiwatar da shawarar”
Ya ce tabbas akwai batun kafa NATOn Larabawa a baya, kuma za a ci gaba da samun irin wannan batu a nan gaba, amma akwai shakku kan ko za a iya aiwatarwa.
Dr Mudassir Ƙamar, ƙaramin farfesa a Cibiyar nazarin yankin yammacin Asia a jami’ar Jawaharlal Nehru da ke birnin Delhi na Indiya, ya ce ƙasashen Larabawa na da ƙungiyoyi da dama da suka haɗu a ciki, kamar ƙungiyar Arab League, da OIC da kuma GCC.
Bayan haka akwai dakarun yaƙi da ta’addanci da ke ƙarƙashin jagorancin Saudiyya, to amma matsalar ita ce yadda za a warware matsalolin da ke tsakanin ƙasashen na Larabawa.
Mudassir Ƙamar ya ce “zai yi matuƙar wahala Isra’ila, wadda yanzu ba ta shiri da ƙasashen Larabawa da dama ta kawar da kai daga duk wani yunƙuri na samar da irin wannan ƙawance.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: harin da Isra ila ta kai a ƙasashen Larabawa da ƙawancen soji da ƙawance irin wannan
এছাড়াও পড়ুন:
Talata ce ɗaya ga watan Rabi’ul Thani — Sarkin Musulmi
Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya ayyana gobe Talata, a matsayin ranar ɗaya ga watan Rabi’ul Thani, 1447 bayan hijira, wanda ya kawo ƙarshen watan Rabi’ul Awwal, 1447, daidai da ranar 23 ga Satumba, 2025.
Sanarwar ta fito ne a wata takarda da Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaid, wanda shi ne shugaban kwamitin da ke bai wa Majalisar Sarkin Musulmi shawara kan al’amuran addini, ya sanya wa hannu ya kuma raba wa manema labarai.
A sanarwar, Sarkin Musulmi bai fayyace wuraren da aka ga sabon watan ba, sai dai ya bayyana cewa ya gamsu da sahihan rahotannin da aka gabatar, lamarin da ya sa ya ayyana ganin watan a hukumance.
Ya yi addu’ar Allah Ya kawo zaman lafiya da ci gaba mai dorewa a Najeriya.