HausaTv:
2025-09-17@21:50:20 GMT

Netanyahu, ya sha alwashin dakile kafa kasar falasdinawa

Published: 12th, September 2025 GMT

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya sha alwashin dakile kafa kasar falasdinawa yayin da ya sanya hannu kan yarjejeniyar gaggauta ci gaba da ginin matsugunan yahudawa a yankin El, na yamma da kogin Jordan da Isra’ilan ta mamaye.

A jiya Alhamis ne Netanyahu ya sanya hannu kan yarjejeniyar, duk da kashedin da sassan kasa da kasa suka jima suna yi, cewa hakan zai gurgunta damar falasdinawa ta kafa kasa mai cin gashin kai.

Yankin da Isra’ila ke fatan ginawa, mashigi ne a bangaren gabashin birnin Kudus, tsakanin birnin da yankin unguwar Ma’ale Adumim, ana kuma ganin gina shi zai haifar da mummunan tasiri, kasancewar hakan zai raba gabashin birnin Kudus da arewacin gabar kogin Jordan, wanda hakan zai dakile damar samar da dunkulalliyar kasar falasdinawa a nan gaba.

Tun a shekarun 1990 ne aka gabatar da aniyar gudanar da ginin wannan yanaki na El, sai dai an dakatar da aiwatar da shi sakamakon adawa daga Isra’ilawa na gida da mazauna ketare. Daga bisani Netanyahu ya sake farfado da batun a shekarar 2012, tare da sake bijiro da shi gabanin babban zaben kasarsa na shekarar 2020.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Araghchi ya caccaki kasashen Turai kan yin biris da cin zarafin Amurka da Isra’ila kan Iran September 12, 2025 Venezuela ta yi gargadi game da karuwar sojojin Amurka a cikin tekun Caribbean September 12, 2025 Kwamitin Sulhu ya yi Allah-wadai da harin da aka kai kan Qatar September 12, 2025 Al-Houthi: Sakamakon samun goyon baya Isra’ila tana ci gaba da aikata laifuka a yankin September 12, 2025 Kasashen Iran da Tunisiya sun amince da fadada alaka yayin da FM Araghchi ya ziyarci kasar Tunisiya September 12, 2025 Rundunar Sojin Iran Ta Bayyan Cikekken Goyon Baya Ga Kasar Qatar September 11, 2025 Shugaban Iran Yace Makiya Suna Son gwara Kan Musulmi Don Sace Arzikinsu September 11, 2025 Qatar Ta Bukaci A Gurfanar Da Netanyahu A Gaban Kuliya Don Fuskantar Adalci September 11, 2025 Hamas Ta Ce Hare-Haren Isra’ila A Doha Ba zai Sauya Kome A Gaza Ba September 11, 2025 Iran Tace IAEA Ta Amince Da Sabuwar yarjeniya Da Ita September 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Kungiyar Human Rights Watch; Isra’ila Ta Kashe ‘Yan Jarida Fiye Da 30 A Kasar Yemen Ne Da Gangan  

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta ce: Laifin da Isra’ila ta yi na kashe ‘yan jaridun Yemen babban ta’addanci ne

Kungiyar kare hakkin bil’ adama ta Human Rights Watch ta tabbatar da cewa: Harin da yahudawan sahayoniyya suka kai a ranar 26 ga watan Satumba kan ‘yan jaridun kasar Yemen, wanda ya yi sanadiyar mutuwar ‘yan jarida sama da 30, laifi ne da ba za a iya kubutar da girman laifin kan wanda ya aikata ba.

A cikin rahoton baya-bayan nan, kungiyar ta fitar ta bayyana cewa, ta tattara bayanan harin da makiya yahudawan sahayoniyya suka kaddamar a ranar 10 ga watan Satumba kan hedkwatar kafafen yada labarai a kasar Yemen, kuma ta yi la’akari da wannan laifi a matsayin misali na hadarin da ‘yan jarida a Yemen da Palastinu ke fuskanta daga hare-haren wuce gona da iri na ‘yan sahayoniyya.

Kungiyar ta yi nuni da cewa harin da aka kai wa cibiyar ‘yan jaridu a ranar 26 ga watan Satumba a kasar Yemen, ya zo daidai da laifuffukan da yahudawan sahyuniya suka aikata a yankin Al-Jawf, wanda ya yi sanadin jikkatar fararen hula da dama, wadanda akasarinsu ‘yan jarida ne.

Wannan bayani ya karyata ikirarin makiya na cewa sun kai hari ne kawai a ginin ma’aikatar kula da dabi’u, kungiyar kare hakkin bil’adaman tana mai cewa faifan bidiyo da shaidun ganin ido na ‘yan kasar, sun tabbatar da cewa da gangan makiya yahudawan sahayoniyya suka kai hari kan hedkwatar ‘yan jaridun fararen hula.

An lura cewa: ” Unguwar da aka kai harin, wani yanki ne mai yawan jama’a da ke kusa da tsohon birnin Sana’a, wurin tarihi na UNESCO.”

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kungiyar Kare Hakkokin Bil’Adama Ta Siriya Ta Bankado Karin Fararen Hula Da Aka Kashe A Rikicin Suweida September 16, 2025 Tawagar Yan Wasan Damben Gargajiya Ta Iran Ta Zama Zakara A Damben Ta Duniya September 16, 2025 An Fara Taron Hukumar Makamashin Nukliya Ta Duniya IAEA Karo Na 69 A Birnin Vienna September 16, 2025 Espania Ta Soke Cinikin Makamai Na EUR Miliyon 700 Da HKI Saboda Kissan Kiyashi A Gaza September 16, 2025 Makaman ‘Drons’ Na Yemen Sun Fada Kan Wurare Masu Muhimmanci A  HKI September 16, 2025 Taron Doha: Daga matakin Allawadai zuwa matakan kalubalantar laifukan Isra’ila September 16, 2025 Ministan Tsaron Venezuela Ya Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Juyin Mulki A Kasar September 16, 2025 Pezeshkian: Ya kamata kasashen musulmi su yanke alaka da gwamnatin sahyoniya September 16, 2025 Bayanin Bayan Taron Doha Ya Yi Kira Da A Kafa Rundunar Hadin Gwiwa Ta Kare Kai September 15, 2025 Fira Ministan Spain: Bai Kamata A Rika Barin “Isr’ila” Tana Shiga Gasar September 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  •  Gaza: HKI Tana Ci Gaba Da Yi Wa Falasdinawa  Kisan Kiyashi A Gaza
  • Iran Ta Bukaci Musulmi Su Goyi Bayan Yunkurin Kasa da Ka Na Kauracewa Isra’ila
  • Akalla Falasdinawa 78 ne sukayi shahada a hare-haren Isra’ila a Gaza
  • Iran Ta Bukaci IAEA Tayi Tir Da Harin Da Isra’ila Ta Kai A Tashoshin Nukiyarta.
  • Pezeshkian: Ta’addancin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Kan Kasar Qatar Zalunci Ne Ga Diflomasiyya
  • Kungiyar Human Rights Watch; Isra’ila Ta Kashe ‘Yan Jarida Fiye Da 30 A Kasar Yemen Ne Da Gangan  
  • Bayanin Bayan Taron Doha Ya Yi Kira Da A Kafa Runduwar Hadin Gwiwa Ta Kare Kai
  •  Dan Kasar Iran Mai Kirkira Ya Sami Kyautar Yabo A Kasar China
  • Gwamnatin Sudan Ta Ce: Babu Sulhu Da ‘Yan Tawayen Kasar Na Kungiyar Rapid Support Forces
  • Rabin Sojojin Isra’ila da suka ji rauni a yakin Gaza na fama da ciwon damuwa