Gwamnatin Jihar Jigawa  ta amince da ƙarin kasafin kuɗi na Naira Biliyan 75 na shekarar 2025, ga gwamnatin jiha da kuma ƙananan hukumomi 27.

Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan zaman majalisar da aka gudanar a gidan gwamnati dake Dutse, babban birnin jihar.

Ya bayyana cewa, wannan ƙarin kasafin kuɗi ya samo asali ne daga ƙarin kuɗaɗen shiga domin biyan buƙatun kuɗaɗen da suka taso, da kuma ƙarfafa manyan fannoni da za su kawo ci gaba mai ɗorewa a faɗin jihar.

Alhaji Sagir Musa Ahmed ya ce, majalisar ta amince da Naira Biliyan 58 ga gwamnatin jiha da kuma Naira Biliyan 17 ga Kananan Hukumomi 27, wanda ya shafi kashe-kashen kudade na yau da kullum da kuma manyan ayyuka.

Ya ce, wannan ƙarin kasafin kuɗin zai inganta ayyuka da tsare-tsare da ake gudanarwa a muhimman fannoni irin su ilimi, kiwon lafiya, ababen more rayuwa, noma da sauran muhimman ayyukan ci gaba.

Sagir ya ƙara da cewa, za a mika ƙarin kasafin kuɗin ga Majalisar Dokokin Jihar domin tattaunawa da amincewa da shi, kamar yadda kundin tsarin mulki da ka’idojin kasafi suka tanada.

Kwamishinan ya ƙara jaddada cewa, wannan mataki ya nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen gudanar da mulki bisa gaskiya da adalci, da kula da kuɗaɗen jama’a yadda ya dace, da kuma tabbatar da samar da ingantattun ayyuka ga al’ummar jihar baki ɗaya.

 

Usman Muhammad Zaria

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jigawa ƙarin kasafin Naira Biliyan

এছাড়াও পড়ুন:

NSCDC Za Ta Fara Sanyan Ido Kan Muhimman Abubuwan More Rayuwa A Jihar Kano

“Bayan karbar mukaminsa na sabon kwamandan hukumar NSCDC na jihar Kano, kwamared Bala Bodinga ya umurci jami’ansa da su sadaukar da kansu ga muhimmin aiki na tabbatar da amincin muhimman kadarori da ababen more rayuwa na kasa.

 

“Kwamandan jihar ya ba da umarnin cewa, ba dare ba rana, cikin sa’o’i 24, dole jami’an hukumar su rika yin sintiri da sanya ido domin dakile ayyukan barayi da masu aikata laifuka a lunguna da sako na jihar,” inji shi.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu Ya Janye Dokar Ta-baci A Jihar Rivers
  • Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a Ribas
  • ALGON ta karrama Gwamna Buni da lambar yabo kan kawo ci gaba a Yobe
  • Najeriya Na Asarar Dala Biliyan 10 Bayan Girbi Duk Shekara- Gwamnatin Tarayya
  • NSCDC Za Ta Fara Sanyan Ido Kan Muhimman Abubuwan More Rayuwa A Jihar Kano
  • Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar 
  • NDLEA ta kama ɗan Indiya da ƙwaya ta Naira biliyan 3 a Legas
  • Gwamnatin Neja Ta Musanta Rahoton Hana Da’awa A Jihar
  • An kama mabaraci da kuɗaɗen ƙasar waje a Ilorin