Babban layin wutar lantarki ya sake faɗuwa
Published: 10th, September 2025 GMT
Babban Layin wutar lantarki na Najeriya ya sake faɗuwa.
Wannan matsala ta haifar da katsewar wuta a wasu sassan ƙasar, wanda ya jefa masu amfani da lantarki cikin damuwa.
Kotun Ghana ta ɗaure ’yan Najeriya 3 shekaru 96 saboda satar mota Mamakon ruwan sama ya hallaka mutum 3 a ZariyaBayanan da Hukumar Gudanar da Wutar Lantarki, sun nuna cewa wutar ta ragu daga megawat 2,917 zuwa megawat 1.
Kamfanin rarraba wuta na Abuja (AEDC), ya tabbatar da faruwar matsalar a saƙon da ya aike wa kwastomominsa.
Ya ce wutar ta ɗauke ne sakamakon matsalar da aka samu daga layin ƙasa da misalin ƙarfe 11:23 na safe.
“Saƙonmu zuwa gare ku shi ne, rashin wutar da ake fuskanta yanzu ya faru ne saboda matsalar da ta samu daga layin ƙasa.
“Wannan ya shafi yankunan da muke bai wa wuta. Muna aiki tare da hukumomin da suka dace domin a dawo da wuta da zarar an komai ya daidaita. Mun gode da haƙurinku,” in ji AEDC.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Babban Layi Wutar Lantarki
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi
Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da fasinjoji a cikin wasu motocin bas Toyota guda biyu a titin Itobe zuwa Ajegwu-Anyigba a Ƙaramar hukumar Ofu ta jihar Kogi.
An samu rahoton cewa, lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 5 na asubahi a tsakanin ƙauyukan Ojiwo’-Ajengo da Mamereboh da ke kan babbar hanyar.
Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da shirin amfani da ma’adanai Kotu ta dakatar da babban taron PDP na ƙasaAn ce masu garkuwa da mutanen sun yi amfani da wata tirela da aka kama wajen tare hanyar bayan shingen binciken jami’an tsaro, da ke kusa da wurin da lamarin ya faru.
Shedun gani da ido sun ce ɗaya daga cikin motocin bas ɗin mai lamba KG: KPA 622LG na kan hanyarta zuwa Abuja, tare da fasinjoji daga wata tashar mota a unguwar Ankpa da ke yankin Kogi ta Gabas.
Har yanzu ba a iya gano adadin fasinjojin da aka yi garkuwa da su ba zuwa yanzu, sai dai mun iya tabbatar da cewa ɗaya daga cikin motocin na ɗauke da fasinjoji ne daga yankin Ankpa, kamar yadda aka gano wasu takardu da wasu kayayyaki a wurin da lamarin ya faru suka bayyana.
“Motocin bas ɗin guda biyu suna kan hanyar Abuja ne a lokacin da suka ci karo da shingayen ’yan bindiga a safiyar ranar Alhamis. Dukkanin fasinjojin, ciki har da direban motocin bas ɗin biyu an yi awon gaba da su cikin daji,” in ji Unubi Ademu, wani mazaunin Achigili, a ƙauyen da ke maƙwabta.
Al’ummar yankin sun ƙara da cewa, jami’an tsaro da suka haɗa da sojoji da mafarauta da kuma ’yan banga suna ƙoƙarin magance lamarin.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Kogi (PPRO), CSP William Aya bai amsa kira da saƙo ba lokacin da aka tuntuɓe shi har zuwa lokacin tattatara wannan rahoto.