Hukumomin Bada Agajin Gaggawa Sun Bada Horo Kan Aikin Ceto A Karamar Hukumar Auyo
Published: 18th, September 2025 GMT
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa (SEMA) tare da haɗin gwiwar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) da Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF sun shirya horar da aikin ceto yayin ambaliya, a Ƙaramar Hukumar Auyo.
Taron horaswar ya haɗa masu ruwa da tsaki daga hukumomi daban-daban, inda aka bai wa mahalarta ƙwarewa da ilimin da ya dace domin samun nasarar ceto da kuma kai dauki ga al’ummomin da ambaliya ta shafa.
A yayin horon, an gudanar da darussa kan dabarun bincike da ceto, bayar da taimakon farko, da hanyoyin kwashe jama’a daga wuraren da ambaliya ta shafa.
Wannan shiri ya nuna jajircewar SEMA, NEMA, da UNICEF wajen horar da al’umma yadda za su kai dauki yayin ambaliya, da bada agajin gaggawa.
A jawabin sa, Jami’in kungiyar ba da agajin ta Red Cross, Ali Yohanna, ya yaba wa SEMA, da NEMA, da UNICEF da kuma Sarakuna bisa halartar horon da zai taimaka wajen ceton jama’ar da ke buƙatar kulawar gaggawa.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
An kashe ’yan ta’addan IPOB da yawa a Imo — ’Yan Sanda
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Imo, ta ce jami’an tsaro da suka haɗa da ’yan sanda, sojoji da DSS sun kashe ’yan ta’addan ƙungiyar IPOB da yawa.
Kakakin rundunar, DSP Henry Okoye, ya ce tawagar ta lalata sansanonin IPOB a yankin Ezioha da ke Ƙaramar Hukumar Mbaitoli, da kuma a Umuele, Ubuakpu, da Amakor a Ƙaramar Hukumar Njaba.
’Yan bindiga sun sako ma’auratan da suka sace a Katsina bayan biyan N50m NAJERIYA A YAU: Wadanne Kalubale Gwamna Fubara Zai Fuskanta Bayan Dawowa Mulkin Ribas?Ya ce da yawa daga cikin mambobin ƙungiyar sun mutu yayin samamen, wasu kuma an kama su, yayin da wasu suka tsere da raunuka.
Okoye, ya ƙara da cewa an gano bindigogi da harsasai da dama a sansanonin, haka kuma ƙwararru sun lalata abubuwan fashewa da aka samu wuraren.
Rundunar ta jadadda ƙudirinta na wanzar da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa tare da roƙon jama’a su yi aiki tare da jami’an tsaro.