Jakadan Iran A Majalisar Dinkin Duniya Ya Ce: Kwamitin Sulhu Ya Rasa Damar Tattaunawa Da Fahimtar Juna
Published: 20th, September 2025 GMT
Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Kwamitin sulhun Majalisar ya rasa damar tattaunawa da fahimtar juna a yau
Jakadan kasar Iran kuma wakilin din-din-din a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani, ya yi tsokaci kan rashin amincewa da daftarin kudiri na ci gaba da dage takunkumin da aka kakabawa Iran a taron kolin na yau, sakamakon matsin lamba daga kasashen Amurka da Turai.                
      
				
Irawani ya bayyana a yayin taron kwamitin sulhun a jiya Juma’a cewa: Kwamitin sulhun ya yi watsi da damar tattaunawa da fahimtar juna, yayin da Rasha da China bisa gaskiya suka gabatar da wani madaidaicin kudiri na tsawaita kudurin Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 2231 da kiyaye tsarin diflomasiyya.
Ya ce: “Maimakon amincewa da wannan tafarki na hankali, Amurka da Troika na Turai sun zaɓi haɓaka matsin lamba, da rarrabuwan kai.” Ya kara da cewa: “Wannan sabanin da ke tsakanin kalamansu da ayyukansu ya sake tabbatar da cewa hakikanin manufarsu ba ta diflomasiyya ba ce illa kara ta’azzarar matsaloli, don haka dole ne a yanzu su dauki cikakken alhakin rikicin da su kansu suka haifar.”
Wakilin Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana matakin da kwamitin sulhun ya dauka a yau a matsayin mai gaggawa, wanda bai dace ba, kuma ya sabawa doka. Iran ba ta ganin wajibcin aiwatar da ita. Yana mai jaddada cewa “alhakin mummunan sakamakonsa ya rataya ne kacokan ga Amurka da kungiyar Troika ta Turai, wadanda suka kirkiro zargin karya kan Iran tare da ba da damar kai hare-hare da haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi a kan cibiyoyi masu kariya.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Jaddada ‘Yancin Kasar Na Mayar Da Martani Kan Sabawa Doka September 20, 2025 Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Mayar Da Martani Kan Zargin Shugaban Kasar Faransa September 20, 2025 Shugaban Kasar Faransa Zai Amince Da Kasar Falasdinu A Ranar Litinin Mai Zuwa A Birnin New York September 20, 2025 Tinubu Zai Dauki Nauyin Gasar Wasanni Commonwealth A 2030 September 19, 2025 Kungiyar Tarayyar Turai EU Ta Mika Bukatunta Ga Kasar Iran. September 19, 2025 Dakarun Sojin Yamen Su Kai Hare-hare A Muhimman Wurare A HKI. September 19, 2025 Isra’ila Na ci Gaba Da Kutsa Kai A Tsakiyar Gaza A Yau Juma’a September 19, 2025 Dangantaka Na Kara Tsami Tsakani Faransa Da Isra’ila Kan Falasdinu . September 19, 2025 Sojojin HKI 12 Ne Suka Halaka Ko Suka Ji Rauni A Gaza September 19, 2025 Amurka Ta Yi Amfani Da Kujeran Veto Don Hana Zaman Lafiya A Gaza September 19, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: a Majalisar Dinkin Duniya
এছাড়াও পড়ুন:
UNICEF Tayi Gargadi Game Da Mawuyacin Hali Da Yara Ke Ciki A Gaza
Kakakin hukumar kula da kanana yaran ta majalisar dinkin duniya tess ingram ta bayyana cewa yanayin da yara ke ciki a yankin gaza yayi muni sosai, inda sama da yara miliyan daya dake gaza suke bukatar taimakon gaggawa na ruwan sha da kuma abinci
Ingram ta fadi a wata hira da aka yi da ita cewa dubban yara a falasdinu suna kwana da yunwa kusan kowanne dare, kuma akalla yara 650,000 ba su koma makaranta ba duk da yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimamma a baya –bayan nan tsakanin bangarori biyu,
Har ila yau ta bayyana batun dakatar da bude wuta a matsayin labari mai kyau, da ya kawo karshen ci gaba da lugudan wuta da israila ke yi kowanne lokaci da ya ci rayukan dubban yara kanana, sai dai ta jaddada cewa yarjejeniyar dakatar da bude wuta ba za ta wadatar ba dole ne sai an kawo karshen yunwa da kuma samar da ruwan sha ga sauran iyalai yankin gaza.
A ranar 10 ga watan okotba ne yarjejeniyar dakatar da bude wuta ta fara aiki a gaza amma duk da haka yanayin da ake ciki ya kara tsananta baka iya zuwa wasu yankuna da dama a yankin saboda ci gaba da kasancewar sojojin isra’ila a wajen.
Isra’ila tana ci gaba da keta yarjejeniyar da ta cimma da kungiyar Hamas, tana ci gaba da kai hare-hare da harbe harbe kuma tana hana shigar da kayan agaji da ake bukata zuwa yankin na Gaza, kuma kashi 2 cikin 3 na adadin wadanda aka kashe mata ne da yara kanana.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hamas Ta yi Watsi Da Zargin Da Amurka Tayi Mata Kan Batun Motocin Agaji A Gaza November 3, 2025 El-Zakzaki: Yakin Sudan Yana Kare Maslahar Kasashen Yamma ne Kawai November 3, 2025 Iran Ta Karbi Sako Kan Batun Komawa Teburin Tattaunawa Ba Kai Tsaye Ba November 3, 2025 Ministar Jin Dadin Jama’a ta Sudan: Mayakan RSF Sun Kashe Mata 300 Da Yi Wa 25 Fyade A El Fasher November 3, 2025 Pezeshkian: Bunkasa Masana’antar Makamashin Nukiliyar Iran Don Inganta Rayuwar Al’ummar Iran Ne November 2, 2025 Araqchi: Da Hadin Bakin Amurka, Gwamnatin Isra’ila ta kaddamar Da Hari Kan Kasar Iran November 2, 2025 Larijani: Iran Ba Ta Tsoron Gudanar Da Tattaunawa, Amma Ta Zama Mai Amfani November 2, 2025 Gwamnatin Isra’ila Tana Ci Gaba Da Hana Masu Jinya Zuwa Kasashen Waje Neman Magani Daga Gaza November 2, 2025 Kasar Qatar Ta Ba Da Tallafin Gaggawa Ga Al’ummar Sudan Bayan Gumurzun El-Fasher November 2, 2025 IAEA : Babu wata shaida da ke nuna cewa Iran na kera makaman nukiliya November 2, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci