UNGA: Yau Shettima zai gabatar da jawabin Najeriya a MDD
Published: 24th, September 2025 GMT
Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima a ranar Laraba zai gabatar da jawabin Najeriya a taron Babban Zauren Majalisar Dinkin duniya (UNGA) karo na 80 da ke gudana a birnin New York na Amurka.
Zai yi jawabin ne a madadin Shugaban Kasa Bola Tinubu tsakanin karfe 3:00 na yamma zuwa 9:00 na dare agogon birnin New York.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa ana sa ran Najeriya za ta bayyana sabbin kudurorinta na kasa (NDCs) da aka sabunta a karkashin yarjejeniyar Paris yayin wannan jawabi.
A baya, Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya halarci zaman bude taron Majalisar Dinkin Duniya, inda Shugaban Amurka, Donald Trump, ya gabatar da jawabi na musamman, yana maraba da shugabannin duniya zuwa taron.
Da yake magana da NAN kan muhimmancin jawabin na Najeriya Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Yada Labarai da Sadarwa (Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa), Stanley Nkwocha, ya ce ana sa ran sakon Najeriya ya karade duniya.
“Ko a fannin diflomasiyyar ilimi, al’adu, wasanni, tsaro, ko diflomasiyyar tattalin arziki, Shugaba Tinubu ya sauya yadda Najeriya ke mu’amala da al’ummar duniya.
“Ya gyara salon manufofin kasashen waje na Najeriya.
“Idan kana son auna karfin muryar Najeriya a matakin duniya, ka tuna da jawabin da ya gabatar a UNGA na shekarar 2024.
“Jawabi ne mai karfi da ya bukaci a yi sauye-sauye, ciki har da karin kujeru ga kasashen Afrika a Kwamitin Tsaro na MDD,” in ji Nkwocha.
(NAN)
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Taraba
এছাড়াও পড়ুন:
Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya
Haka kuma, kaso 73.2 sun yi imanin cewa manyan kasashe ba sa sauke dukkan nauyin da ya rataya a wuyansu game da harkokin kasa da kasa, sannan kaso 81.9 sun yi kira ga MDD da ta kara mayar da hankali kan muradu da bukatun kasashe masu tasowa. (FMM)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA