Araqchi Ya Gana Da Babban Malamin Yahudawa Mai Adawa Da ‘Yan Sahayoniyya A Gefen Taron Kungiyar BRICS
Published: 7th, July 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya gana da babban malamin yahudawa rabbi mai adawa da ‘yan sahayoniyya a gefen taron BRICS a Brazil
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya gana kuma ya zanta da wani babban malamin yahudawa mai adawa da ‘yan sahayoniyya a gefen taron kasashen BRICS a kasar Brazil.
Rabbi Yisrael Dovid Weiss, wanda ya je Brazil domin ganawa a gefen taron BRICS, ya gana da ministan harkokin wajen Iran, inda suka yi musayar ra’ayi da shi.
Wani abin lura shi ne cewa a baya malamin ya ziyarci ofishin jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ke kasar Brazil bayan bude littafin ta’aziyya ga shahidan da yahudawan sahayoniyya da suke kai wa hari a kasar hari. A cikinsa ne ya rubuta kalamai na nuna goyon bayansa ga al’umma da gwamnatin Iran tare da jajantawa iyalan shahidan da suka rasa rayukansu sakamakon zaluncin da yahudawan sahayoniyya suka dauka kan kasar Iran.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Taron Ashura Ya Zama Lamari Mafi Girma Da Cinkoson Jama’a, Inda Masu Ziyara Daga Sassan Duniya Suka Isa Karbala
Gangamin Ashura ya zama lamarin mafi girma da cunkoson jama’a inda tattakiin Tuwairij yake gudana tare da faɗaɗa da ba a taɓa ganin irinsa ba
Tattakin Tuwairij na bana zuwa birnin Karbala na fuskantar hallara da cunkoson jama’a da ba a taba ganin irinsa ba, inda dimbin masu ziyara daga sassan duniya ke tururuwa zuwa hubbaren Imam Husaini da kuma titunan da ke kewaye.
Mai ba da shawara ga babban sakataren cibiyar Hubbaren Imam Husain {a.s} Fadel Oz a cikin wata sanarwa da ya aikewa kafafen watsa labarai ya bayyana cewa: “A shirye-shiryen wannan juyayi, babban Sakatariyar Haramin Imam Husain (a.s) da haramin Abbas sun samar da dukkan sharuddan da suka dace don kula da masu ziyara da kuma tabbatar da jin dadinsu.
Ya kara da cewa, “Yankin da aka kebe domin gudanar da juyayin Ashura ya samu gagarumin ci gabata hanyar fadada shi, domin a shekarun da suka gabata ana ci gaba da gudanar da ayyukan da suka yi na mallakar wuraren da ke kewaye da fadada titunan da ke zuwa gare su da nufin daukar saukaka wa masu halartar taron.
Oz ya ci gaba da cewa “Hukumar ayyuka, ‘yan sanda, sassan jami’ai, da kuma cibiyoyin gwamnati sun kuma taka rawar gani wajen hada kai don tabbatar da gudanar da juyayin Ashura cikin kwanciyar hankali da lumana.”
Ya bayyana cewa, “wannan hadin gwiwa yana nuna irin kishin da hukumomin da abin ya shafa suke da shi wajen tabbatar da nasarar gudanar da juyayin Ashura a cikin yanayi na musamman na ruhi,” yana mai jaddada cewa “wadannan fadadawa da shirye-shirye suna tafiya tare da ci gaba da karuwar masu ziyara da kuma tabbatar da samun kwarewa da kwanciyar hankali a wannan babban taron addini.”