Aminiya:
2025-10-13@15:50:23 GMT

Kwankwaso ya fara tattaunawa da Nentawe kan maganar komawa APC

Published: 26th, September 2025 GMT

Kwararan bayanai na nuni da cewa tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya fara tattaunawa da Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, kan shirin komawa jam’iyyar.

Majiyoyi daga cikin APC a Kano sun bayyana cewa Kwankwaso ya rubuta wasiƙa zuwa sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa a Abuja, yana sanar da aniyarsa ta komawa jam’iyyar.

An rufe wurin haƙar zinare a Kebbi Sauya Sheƙa: Kwankwaso ya gindaya sharuɗa kafin sake komawa APC

Sai dai Aminiya ba ta iya tabbatar da hakan ba ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Wata majiya daga sakatariyar APC ta ƙasa kuma ta tabbatar da cewa ana ci gaba da tattaunawa tsakanin Kwankwaso da Farfesa Nentawe kan sauya shekar, kuma maganar ta yi nisa sosai.

Majiyar ta ce hakan ya biyo bayan wata ganawa da Kwankwaso ya yi da fadar shugaban ƙasa kan batun.

“A matsayinmu na jam’iyya, za mu bi duk shawarar da shugabanni suka yanke idan har za ta amfani jam’iyyar,” in ji majiyar.

Kwankwaso shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, kuma shi ne ginshiƙin nasarar jam’iyyar a zaɓen shugaban ƙasa da na gwamna a Kano, inda Abba Kabir Yusuf ya doke Nasiru Yusuf Gawuna na APC.

Wata majiya mai tushe daga APC Kano ta shaida wa wakilinmu cewa Kwankwaso ya gabatar da wasu sharuɗɗa kafin komawarsa jam’iyyar.

Abuja ya tura wasikar ba Kano ba

Majiyar ta ce an tura wasiƙar ne zuwa shugabannin jam’iyyar na ƙasa a Abuja, ba reshen Kano ba, saboda sabanin da ke tsakanin Kwankwaso da shugabannin APC na jihar.

“Mun san da wasiƙar da ya tura, amma ba za mu iya magana a kai ba yanzu. Idan zai shigo, babu matsala, ana maraba da shi,” in ji majiyar.

“Abin da muka sani shi ne, ya tura wasiƙar ne Abuja, ba Kano ba. Duk yadda aka yi, idan an kammala komai, za a sanar da jama’a,” in ji majiyar.

Masana harkokin siyasa na ganin rubuta wasiƙar na nuni da cewa Kwankwaso ya yanke shawarar matakin da zai dauka na gaba kafin babban zaben 2027.

‘Dole a ba Abba takara a APC a 2027’

Cikin sharuɗɗan da majiyarmu ta bayyana akwai buƙatar a bai wa Abba Kabir Yusuf, wanda shi ne gwamnan Kano kuma yaron Kwankwaso, damar yin takarar gwamna a APC, yayin da Kwankwaso zai samu matsayi babban matsayi a gwamnatin APC mai zuwa.

Duk da cewa majiyoyi na kusa da Kwankwaso sun ƙi bayyana yadda shirin ke tafiya, wasu majiyoyi masu tushe na kusa da Gwamna Abba sun ce gwamnan ya shirya tsaf.

“Gwamnanmu ba shi da wata matsala kwata-kwata,” in ji wata majiya.

“Yana jiran duk abin da maigidansa za ice ne kawai,” in ji majiyar.

Daraktan Yaɗa Labarai na APC na ƙasa, Bala Ibrahim, ya shaida wa Aminiya cewa batun wasiƙar da Kwankwaso ya tura har yanzu jita-jita ce.

“Ba ni da masaniya kan tura wasiƙar da Kwankwaso ya yi,” in ji shi.

Kan ko akwai wata tattaunawa a ƙasa da Kwankwaso, Bala Ibrahim ya ce, “Ban sani ba gaskiya. Duk wannan jita-jita ce.”

Wakilanmu sun fahimci cewa daidai tsarin jam’iyya, ya kamata tsohon gwamnan ya fara da tuntuɓar mazabarsa, ba kai tsaye zuwa sakatariyar ƙasa ba.

Makomar Kwankwasiyya a APC

A makon da ya gabata ne Kwankwaso ya bayyana cewa jam’iyyarsa ba ta da matsala da shiga APC.

Yayin da yake karɓar tsohon mai ba Ganduje shawara kan harkokin siyasa, Buhari Bakwana tare da mambobin APC daga ƙananan hukumomi 44 na Kano a gidansa da ke titin Miller Road a Kano, Kwankwaso ya ce duk wata tattaunawa kan haɗin gwiwa ko komawa APC dole ne ta bayyana abin da NNPP za ta samu.

Taron Shugabannin APC na Kano a Abuja

A matsayin martani ga rahotannin yiwuwar sauya shekar Kwankwaso, manyan jiga-jigan APC daga Kano a ranar Alhamis sun gudanar da taron tattauna batutuwan siyasa a Abuja.

Taron ya samu halartar fitattun shugabannin APC ciki har da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin; tsohon Shugaban APC na ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje; Karamin Ministan Gidaje da Raya Birane, Abdullahi Ata; da Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin Majalisar Dattawa, Basheer Lado.

A taron, an amince da goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu don yin tazarce.

Shugabannin sun kuma sha alwashin yin aiki tukuru don dawo da mulki ga APC a Kano a zaɓen gwamna na 2027.

Sauran wadanda da suka halarci taron sun haɗa da Sanata Kawu Sumaila (APC, Kano ta Kudu), Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Wakilai, Abubakar Kabir Bichi; Sanata Kabiru Ibrahim Gaya; Shugaban APC na jihar, Alhaji Abdullahi Abbas da sauran jiga-jigan jam’iyyar.

Aminiya ta rawaito cewa APC ta rasa Kano a hannun NNPP a zaɓen 2023, inda ta koma matsayin babbar jam’iyyar adawa a jihar.

Daga Andrew Agbese, Saawua Terzungwe, Abdullateef Salau, Salim Umar Ibrahim da Sani Ibrahim Paki

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Kwankwaso Nentawe in ji majiyar da Kwankwaso Kwankwaso ya

এছাড়াও পড়ুন:

Barin PDP Zuwa Wata Jam’iyyar Alamun Rashin Jarumta Ne – Gwamnan Bauchi

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sanatan Bauchi Ta Arewa Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP October 11, 2025 Siyasa Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu October 9, 2025 Labarai Kotu Ta Yi Watsi Da Ƙarar Da Aka Shigar Da Tinubu Kan Sanya Dokar Ta-Ɓaci A Ribas October 2, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Majalisar Shura ta fara ganawar sirri da Malam Triumph
  • Hukumar Hisbah Ta Kama Wasu Matasa Da Suka Yi Aure Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Kano
  • Ahmed Musa Ya Nemi Afuwar Ƙungiyar 3SC Akan Abinda Ya Faru Da ‘Yan Wasansu A Kano
  • Zaɓen Kamaru: Tchiroma Bakary na da kwarin gwiwa a yayin da ake jiran sakamako
  • Gwamna Sani Ya Gana Da Ministan Ayyuka Domin Ganin An Kammala Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna 
  • Gwamna Uba Sani Ya Gana Da Ministan Ayyuka Domin Ganin An Kammala Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna 
  • Barin PDP Zuwa Wata Jam’iyyar Alamun Rashin Jarumta Ne – Gwamnan Bauchi
  • Sanatan Bauchi Ta Arewa Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP
  • Rashin wutar lantarki ta kassara kasuwanci a Kaduna, Kano da Katsina
  • Falasdinawa Daga Kudancin Gaza Sun Fara Komawa Gidajensu Da Aka  Rusa A Arewacin Yankin