An kama sojan bogi da ɓarayin mota 2 a Jigawa
Published: 18th, September 2025 GMT
Rundunar ‘yan Sandan Jihar Jigawa ta bada sanarwar nasarar cafke wani sojan bogi da ƙarin wasu mutum biyu da ake zargi da satar mota a ƙauyen Sabon Sara.
Kamar yadda Kakakin rundunar ’yan sanda na Jigawa, SP Shiisu Lawan Adam ya sanarwa manema labarai a garin Dutse cewa, an kama matashin sojan bogin da abokansa da ake zargin su da satar mota a ƙauyen Sabon Sara, cikin ƙaramar hukumar Kafin Hausa.
A cewar majiyar an kama sojan bogin mai suna Kabiru Musa da abokan aikinsa Umar Ali da Sabi’u Bashir, dukkansu ‘yan asalin Jihar Kano.
A cewar kakakin rundunar waɗannan mutane an kuma same su da katin cire kuɗi ATM guda 7, lasisin tuƙi guda biyu da kuma sauran kayan da su ke amfani da su wajen aikata laifin da suka ƙunshi kakin sojan da shi Kabiru Ali ke amfanin da shi.
“Da zarar an kammala bincike za a miƙa su gaban kuliya don fuskantar abin da suka aikata.”in ji SP Lawan.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jigawa Sabon Sara
এছাড়াও পড়ুন:
An Kashe Mutum 3 Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Kan Iyakokin Kano
Majiyar ta kara da cewa, bayan yunkurinsu bai yi nasara ba a Tsanyawa, maharan sun sake wani sabon shiri, inda suka kai hari a kauyen Yar Tsamiya da ke gundumar Faruruwa, karamar hukumar Shanono, da misalin karfe 1:30 na dare, inda suka kashe mutane uku suka, tare da sace wasu uku.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA